Aminiya:
2025-11-23@06:15:42 GMT

H-JRBDA ta yi alƙawarin magance ambaliyar ruwa a Jigawa

Published: 23rd, November 2025 GMT

Hukumar Raya Kogunan Hadejia da Jama’are (H-JRBDA) ta yi alƙawarin ɗaukar matakan gaggawa don magance matsalar ambaliyar ruwan da ke addabar al’ummar Ƙaramar Hukumar Jahun a Jihar Jigawa.

Manajan Daraktan Hukumar, Injiniya Rabi’u Sulaiman Bichi, ya bayyana hakan bayan karɓar roƙon da jama’ar yankin suka miƙa ta hannun Shugaban Ƙaramar Hukumar, Jamilu Ɗan Malam Mai Rice, kan yawaitar ambaliya a yankin.

Gwamnatin Yobe ta ba da umarnin rufe makarantun kwana a jihar Gwamnatin Tarayya ta musanta jita-jitar rufe dukkanin makarantu a faɗin Najeriya

A cewar Injiniya Bichi, “Mun karɓi kokenku hannu biyu. Matakin da shugabancin Jahun ya ɗauka ya yi dai-dai. Za mu tura ƙwararrun injiniyoyi su yi aikin da ya kamata domin daƙile ambaliyar, tare da inganta noman yankin ta hanyar gina madatsar ruwa domin ruwan sha da na aikin gona.”

A nasa bangaren, Shugaban Ƙaramar Hukumar Jahun, Hon. Jamilu Ɗan Malam Mai Rice, ya ce sun gabatar da koken ne saboda matsalar ambaliyar ta daɗe tana addabar su ba tare da samun mafita ba.

Ya ce, “Muna godiya bisa yadda kuka amsa kiranmu. Kun zo kun duba matattarar ruwan Akama da ta Fande tare da ƙwararrun injiniyoyinku. Wannan ya nuna ku na da niyyar magance matsalar da ta dade tana damunmu.”

Tawagar hukumar da ta kai ziyarar ta haɗa da Daraktan Kuɗi da Mulki, Musa Iliyasu Kwankwaso; Daraktan Tsare-tsare, Alhaji Tijjani Musa Isah; Daraktan Na’urori, Injiniya Dan Baffa Abdulƙadir; da Injiniya Sabi’u Ɗan Malan, tare da sauran manyan jami’an hukumar.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Ambaliya Jihar Jigawa

এছাড়াও পড়ুন:

Hukumar Hisbah Ta Rufe Wani Wuri da Ake Zargin Ana Aikata Badala A Kano

Daga  Khadijah Aliyu 

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama wasu samari bakwai da ke shiga irin ta mata da aikata badala a wani shahararren gurin nishadi da ke kan titin Zoo Road a karamar hukumar Kano Municipal.

Yayin tabbatar da faruwar lamarin ga Rediyon Nijeriya, Mataimakin Kwamanda Janar na hukumar Hisbah, Sheikh Mujahid Aminudeen Abubakar, ya ce an kama samarin da ke kasa da shekaru 23 bayan samun bayanan sirri daga wani mai kishin ƙasa.

Mai bayar da bayanan ya sanar da cewa mmatasn da aka fi sani da ‘Yan Daudu, suna yawan zuwa wurin, inda ake zargin cewa motocin mutane daban-daban ke zuwa su ɗauke su.

Sheikh Mujahid ya bayyana cewa binciken farko ya nuna cewa matasan sun fito ne daga jihohin Kogi, Bauchi da Kano.

Ya ƙara da cewa yayin gudanar da aikin, jami’an Hisbah sun kuma kama wani saurayi da wata budurwa da aka same su tare a cikin babur mai ƙafafu uku, sannan kuma an gano wata yarinya da aka ce ta bace a Sakkwato, aka kuma maida ta ga iyayenta.

Mataimakin Kwamanda Janar din ya ƙara da cewa hukumar za ta rufe wurin nishadin saboda zargin  ɓoye ƙananan yara da ke aikata munanan ayyuka.

Ya ce za a mika matasan da aka kama tare da masu kula da wurin ga hukumomin da suka dace domin ci gaba da daukar mataki.

Sheikh Mujahid ya tabbatar da jajircewar Hisbah na kawar da dukkan nau’o’in munanan dabi’u a jihar, tare da kira ga jama’a da su rika kai rahoton duk wata matsala ko abin da suke shakku ga hukumar Hisbah ko wasu hukumomi da suka dace.

 

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An rufe makarantun Filato saboda matsalar tsaro
  • Hukumar Alhazai Ta Jihar Jigawa Za Ta Mayar Da Rarar Kudi Ga Maniyyatan 2026
  • Duniyarmu A Yau: Sabon Kuduri Mai Yin Allawadai Da Iran A Hukumat IAEA
  • Majalisar Kano ta dawo da shugaban ƙaramar hukumar Rano kan kujerarsa
  • Zargi: Majalisar Kano ta dawo da shugaban ƙaramar hukumar Rano kan kujerarsa
  • Dalibai a Jihohin Arewa Maso Yamma Sun Koka Game da Ƙalubalen Tsaro a Yankin
  • Hukumar Hisbah Ta Rufe Wani Wuri da Ake Zargin Ana Aikata Badala A Kano
  • Jihar Jigawa Ta Amince da Naira Biliyan 3.5 a Matsayin Kudaden Tallafin UBEC 2025
  • Gwamnatin Kwara ta rufe makarantu a kananan hukumomi 4 saboda matsalar tsaro