Daga Sani Sulaiman

 

Gwamnan Jihar Taraba, Dr. Agbu Kefas, ya yi jimami kan rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ya rasu a ranar Alhamis 27 ga watan Nuwamban 2025, yana da shekaru 102.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai bai wa gwamnan shawara na musamman kan Yada Labarai da Hulda da Jama’a, Mista Emmanuel Bello, ya sanyawa hannu.

Gwamnan ya ce rasuwar wannan babban malami babban rashi ne ga kasa, yana mai nuna cewa a wannan lokaci ne ake matuƙar bukatar irin gudummawar da yake bayarwa, duba da kalubalen da kasar ke fusfuskanta.

Ya kara da cewa marigayi Sheikh ya koyar da ilimi da zai ci gaba da jagorantar kasa kan batun zaman lafiya tsakanin addinai.

Haka kuma, Dr. Kefas ya yabawa halayen Sheikh Bauchi, wanda ya bayyana shi a matsayin mutum mai tawali’u, jin kai, da haƙuri.

Saboda haka, Gwamna Agbu Kefas ya yi kira ga jama’a da su yi koyi da jagorancin wannan fitaccen malami.

Ya ce al’ummar  kasa za su ci gaba da bin tsarin ladabi da tarbiyyar da marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya koyar.

A wani bangaren, Dr. Kefas ya ja hankalin  ‘yan Najeriya da  su ci gaba da kasancewa cikin zaman lafiya da juna ba tare da la’akari da addininsu ba.

Ya jaddada muhimmancin jurewa da girmama ra’ayin juna maimakon nacewa a kan namu ra’ayin, tare da tabbatar da aniyarsa ta ci gaba da hidima ga dukkan ‘yan Jihar Taraba bisa adalci ba tare da la’akari da addini ko kabilarsu ba.

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Gwamna Kefas Ta aziyya Taraba

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamna Namadi Ya Kaddamar da Titi Mai Tsawon Kilomita 13 a ‘Yankwashi

Daga Usman Muhammad Zaria

Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, ya kaddamar da titi mai tsawon kilomita 13 da rabi, da ya tashi daga Sada zuwa Danakari zuwa Unguwar Malam Kuda, zuwa Magina, a Karamar Hukumar Yankwashi ta jihar.

A  jawabinsa wajen bikin kaddamarwar, Namadi ya bayyana kudirin gwamnatinsa na ci gaba da samar da muhimman abubuwan more rayuwa a karkara domin inganta harkokin tattalin arzikinsu.

Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa Gwamna Umar Namadi ya ce titin, wanda aka gina akan kudi Naira biliyan 1 da miliyan 690, na daga cikin manyan ayyukan gine-ginen hanyoyi 48 da gwamnatinsa ta bayar a shekarar 2024.

A cewarsa, titin zai hada al’ummomin karkara na Sada, Danakari, Unguwar Malam Kuda da Magina.

 

Ya jaddada cewa mutanen wadannan yankuna sun daɗe suna bukatar wannan aiki na hanyar.

Malam Umar Namadi ya ce titin zai ba su damar kai amfanin gonakinsu kasuwanni mafi kusa cikin sauki.

Ya kuma ce yawancin wadannan hanyoyi sun kai matakin kammaluwa, kuma nan ba da dadewa ba za a gudanar da jerin bukukuwan kaddamar da su gaba daya.

Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da samar da hanyoyin sufuri a karkara domin saukaka samun hanyoyin shiga kasuwanni da birane.

Namadi ya bayyana cewa shirin tuntubar jama’a ya bai wa al’umma damar tattaunawa kai tsaye da gwamnati.

Tun da farko, Kwamishinan Ayyuka da Sufuri na jihar, Injiniya Gambo Malam, ya ce titin na daga cikin hanyoyi 48 masu dauke da jimillar tsawon kilomita 977 da aka bayar a 2024 a kan kudi Naira biliyan 304.

Wasu daga cikin mazauna yankin, Malam Abdullahi Musa da Malam Muhammad Gata, sun yaba wa gwamnatin jihar bisa wannan aiki.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An rantsar da sabon shugaban kasa a Guinea-Bissau bayan juyin mulkin sojoji
  • Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi ta bar babban gibi a Najeriya – Tinubu
  • Mutuwar Sheikh Dahiru Bauchi Babban Rashi Ne Ga Kasa Baki Daya- Shugaba Tinubu
  • Mutuwar Sheikh Dahiru Bauchi Babban Rashi Ne Ga Kasa Baki Daya
  • Abubuwa 20 da ya kamata ku sani game da Sheikh Dahiru Bauchi
  • Sheikh Dahiru Bauchi: Malamin da zuri’arsa ta fi kowacce yawan mahaddata Alkur’ani
  • Gwamnan Bauchi ya yi ta’aziyyar rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi
  • Allah Ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa
  • Gwamna Namadi Ya Kaddamar da Titi Mai Tsawon Kilomita 13 a ‘Yankwashi