An rufe duk makarantu a Jihar Bauchi saboda matsalar tsaro
Published: 24th, November 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Bauchi ta ba da umarnin rufe dukkan makarantun firamare, sakandare, da manyan makarantu—ciki har da Gwamnatin Tarayya da makarantu masu zaman kansu saboda matsalolin rashin tsaro da ke faruwa a faɗin ƙasar kan.
Sanarwa da Jalaludeen Usman Jami’in Hulɗa da Jama’a na Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Bauchi, ya fitar ta ce, “Wannan shawara, duk da cewa tana da wahala, Gwamnatin Jihar Bauchi ta yanke ta ne bayan tattaunawa mai zurfi da kuma la’akari da matsalolin tsaro da suka shafi tsaron ɗalibai, malamai, da al’ummomin makarantu a faɗin jihar.
“Gwamnati ta san abin da wannan matsala ka iya haifarwa. Duk da haka, kare ’ya’yanmu ya kasance babban nauyin da ke kanmu. Muna sane da cewa lowane ɗalibi a Jihar Bauchi ya cancanci ya yi karatu a cikin yanayi mai aminci, kwanciyar hankali, kuma ba tare da tsoro ba.
“Saboda haka muna kira ga iyaye, masu kula, masu mallakar makarantu, da duk masu ruwa da tsaki da abin ya shafa da kada su firgita, amma su kwantar da hankalinsu su kuma ba da haɗin kai.”
“Gwamnati tana aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumomin tsaro don magance matsalolin cikin sauri da kuma cikakkiyar fahimta, tare da tabbatar da cewa ayyukan ilimi na yau da kullum, za su ci gaba da gudana da zarar an tabbatar da hakan.
“Muna kuma kira ga jama’a da su ci gaba da taka tsantsan. Idan kun ga wani abu da ba ku gane ba ku bayar da bayani wa jami’an tsaro saboda bayar da bayanai da a kan lokaci suna da mahimmanci wajen kare al’ummominmu.
“Gwamnatin Jihar Bauchi za ta ci gaba da samar da sabbin bayanai yayin da lamarin ke ci gaba.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ɗalibai Rufe Makarantu Tsaro Jihar Bauchi
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Tarayya ta musanta jita-jitar rufe dukkanin makarantu a faɗin Najeriya
Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta ƙaryata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa za a rufe dukkanin makarantu a faɗin Najeriya daga ranar 24 ga watan Nuwamba, 2025.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar, ma’aikatar ta ce labarin ƙarya ne, ba shi da tushe daga Gwamnatin Tarayya, Ma’aikatar Ilimi ko kuma wata hukuma ta tsaro.
Obi ya yi watsi da hukuncin ɗaurin rai da rai da aka yi wa Kanu Mutane 315 ne suka ɓace bayan hari a makaranta NejaMai magana da yawun ma’aikatar, Folasade Boriowo, ta shawarci jama’a da su yi watsi da duk wata sanarwa da ba ta fito daga hukumomin gwamnati ba.
Ta ƙara da cewa jama’a su riƙa tantance gaskiyar kowane bayani kafin su yaɗa shi domin kauce wa yaɗs labarun ƙarya.
Wannan bayani ya biyo bayan umarnin Gwamnatin Tarayya na rufe manyan makarantun sakandare 41 da ke yankunan da ke fuskantar barazanar tsaro, sakamakon sace ɗalibai a jihohin Neja da Kebbi.
Haka kuma wasu jihohi kamar Kwara, Filato, Katsina da Neja sun rufe makarantunsu saboda matsalar tsaro.
Jihar Taraba ma ta bayar da umarnin rufe dukkanin makarantu da ke jihar.