Aminiya:
2025-11-24@15:09:12 GMT

Sace ɗalibai: Idan Tinubu ba zai iya ba ya sauka kawai — PDP

Published: 24th, November 2025 GMT

Jam’iyyar PDP ta yi soki matakin rufe makarantu da Gwamnatin Tarayya da wasu jihohi suka ɗauka sakamakon yawaitar sace-sacen dalibai, tana mai gargaɗin cewa hakan na iya taimaka wa ’yan ta’adda cimma burinsu.

A taron manema labarai da aka gudanar a Abuja a ranar Lahadi, kakakin jam’iyyar, Ini Ememobong, ya ce, ya buƙaci Shugaba Tinubu da ya ajiye muƙaminsa idan ba zai iya kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya.

“Muna sake tunatar da Shugaba Tinubu da gwamnatin APC cewa tsaron rayuka da dukiyoyi shi ne aikin farko na kowace gwamnati. Duk lokacin da gwamnati ta kasa yin wannan aiki, dole ta nemi taimako—na cikin gida ko na waje—ko kuma ta yi murabus idan tana da gaskiya da shugabanci,” in ji Ememobong

Ya ci gaba da cewa, “Idan aka rufe makarantu, to ’yan ta’adda sun cimma nasara.”

Umarnin janye ’yan sanda daga faɗin manyan mutane na iya zama magana kawai —Shehu Sani Yau Atiku zai karɓi katin zama ɗan a Jama’iyyar ADC

Ya buƙaci gwamnati ta samar da tsari na musamman don magance matsalar tsaro, maimakon sauƙaƙa ta, ta hanyar rufe makarantu don kauce wa sace-sace da kuma neman yabo saboda siyasa.

Ememobong ya jaddada muhimmancin aiwatar da shirin samar da tsaro a makarantu, wanda ya ce ya ta’allaƙa ne kan bayanan sirri daga al’umma da kuma tsarin ɗaukar matakan gaggawa na dakile hare-hare.

Ya bayyana cewa rashin tsaro ya zama babban cikas ga ilimi a Najeriya, musamman a Arewacin ƙasar. Ya yi nuni da alƙaluman Asusun Kula da Ƙananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) da ke nuna cewa Arewacin Najeriya na da mafi yawan yara da ba sa zuwa makaranta—miliyan 10.2 a matakin firamare da miliyan 8.1 a sakandare.

Ememobong ya ce, “Wannan bayanin ba wai kawai yana nuna mummunan hoto ba, har ma yana bayyana ainihin halin da ake ciki a Najeriya. Jerin hare-hare da sace-sace a jihohi daban-daban cikin mako guda na nuna yadda rashin tsaro ya zama sabon yanayin rayuwa a ƙarƙashin gwamnatin APC ta Bola Tinubu.”

Ya kuma soki yadda gwamnati ke mayar da martani ga sace-sacen ɗalibai, yana mai cewa, “Abin damuwa shi ne, duk lokacin da irin wannan mummunan lamari ya faru, martanin gwamnati ba ya da ƙarfi kuma ba ya nuna tausayi.

“Misali, maimakon Shugaban Ƙasa ya ziyarci jihohin Kebbi da Neja don jajanta wa iyayen da ’ya’yansu ke hannun ’yan bindiga da kuma karfafa jami’an tsaro, sai kawai ya umarci Ƙaramin Ministan Tsaro ya koma Kebbi.”

Ya ƙara da cewa kwatanta yadda aka tura tawagPDP ta buƙaci Shugaba Tinubu da ya ajiye muƙaminsa idan ba zai iya kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya.a zuwa Majalisar Dokokin Amurka da taron G-20 da kuma yadda aka tura wakili guda zuwa Kebbi, ya nuna yadda Fadar Shugaban Ƙasa ke ɗaukar wannan matsala da sakaci.”

PDP ta sake jaddada cewa kare rayuka da dukiyoyin ’yan ƙasa shi ne babban aikin kowace gwamnati.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: yan ta adda makarantu Tsaro da gwamnati

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai a Neja

Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) sun nuna damuwarsu kan sace malamai da ɗaliban makarantar St. Mary’s da ke Ƙaramar Hukumar Agwara, a Jihar Neja.

Sun ce wannan lamari babban hatsari ne ga rayuwar yara da makomar ilimi a yankin Arewa baki ɗaya.

DSS ta mayar da Nnamdi Kanu gidan yarin Sakkwato Sojoji sun bar makarantar Maga kafin ’yan bindiga su kai hari — Gwamna Kebbi 

Shugaban ƙungiyar kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ce wannan hari abin takaici ne wanda ba za a lamunta da shi ba.

Ya jaddada cewa makarantu wajibi ne su kasance wuraren karatu da tsaro, ba wuraren tashin hankali ba.

Gwamna Yahaya ya ce Arewa ba za ta lamunci koma baya ba wajen rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.

Ya ce: “Arewa na fama da ƙalubalen ilimi kuma ba za mu bari miyagu su lalata ci gaban da ake samu ba.”

Ya bayyana damuwa kan yadda hare-hare ke ƙaruwa a makarantu yayin da gwamnatocin Arewa ke ƙoƙarin samar da ingantattun tsare-tsaren tsaro ga ɗalibai.

Ya ce ƙungiyar za ta ci gaba da aiki tare da hukumomin tsaro da al’umma don ƙarfafa tsaro a unguwanni da makarantu, da kuma tattara bayanai masu muhimmanci.

A madadin gwamnonin, Gwamna Yahaya ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda aka sace da Gwamnatin Jihar Neja.

Ƙungiyar ta buƙaci a ɗauki matakin gaggawa don ceto waɗanda aka sace cikin ƙoshin lafiya da kuma hana faruwar irin wannan lamari a nan gaba.

Haka kuma, ta yaba wa jami’an tsaro da ke aikin ceto ɗaliban da malamai, inda ya roƙe su da su ƙara himma, tare da roƙon jama’a su ba da haɗin kai don samun nasarar ceto waɗanda lamarin ya shafa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sace ɗalibai: Ba rufe makarantu ba ne mafita — PDP
  • Umarnin janye ’yan sanda daga faɗin manyan mutane na iya zama magana kawai —Shehu Sani
  • An ceto mutum 38 da aka sace a cocin Kwara — Tinubu
  • An gano wurin da ’yan bindiga ke tsare da ɗalibai 25 da aka sace a Kebbi
  • Sace ɗalibai: An rufe makarantu a Katsina da Taraba
  • Gwamnati ta ba da umarnin rufe makarantun kwana 47 a faɗin Najeriya
  • Atiku ya nemi a ayyana dokar ta-ɓaci kan satar ɗalibai a Najeriya
  • Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai a Neja
  • Sace ɗalibai: Tinubu ya bai wa Ministan Tsaro umarnin tarewa a Kebbi