Amma saboda yanzu yanayin rayuwa ya canza, ba ni da mota ko ɗaya; ya sa idan na yi waccan maganar sai wasu su riƙa nuna rashin amincewarsu, wannan kuma rashin sani ne kawai, domin kuwa da a ce sun san wane ne Mai Dawayya a shekarun da suka gabata, da ba su yi wannan magana ba, koda kuwa da wasa, in ji shi.

Mai Dawayya ya buƙaci matasan mawaƙa masu tasowa a masana’antar ta Kannywood, da su tabbatar sun yi amfani da wannan lokaci da suke kan ganiyarsu, duniya kuma take yi da su; wajen gina gobensu, ba wai su dinga hawan motoci da sauran sharholiyar rayuwa ba.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Kannywood

এছাড়াও পড়ুন:

Jarumar Kannywood Rahama Sadau ta yi aure

Fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau, ta yi aure da masoyinta, Ibrahim Garba.

An ɗaura auren a ranar Asabar a Masallacin da ke Unguwan Rimi, a Jihar Kaduna, bayan Ibrahim ya biya sadaki Naira 300,000.

Za a biya ma’aikata 445 garatutin sama da biliyan ɗaya a Kebbi Kotu ta ɗaure wata mata shekara 3 a kan damfara 

Rahama, ta sanar da ɗaurin auren a shafinta na Facebook, inda ta gode wa Allah tare da neman addu’a daga masoyanta.

Ta bayyana farin ciki da godiyarta, tare da fatan wannan sabon babi na rayuwarta zai kasance mai albarka.

Auren mata na zuwa ne watanni biyu bayan rasuwar mahaifinta, Ibrahim Sadau.

’Yan uwanta sun yaɗa hotuna da bidiyon bikin a kafafen sada zumunta, inda mutane da dama suka yi mamakin yadda aka yi bikin ba tare da sanin jama’a ba.

Rahama, wacce furodusa ce a Kannywood, an naɗa ta memba a Kwamitin Fasaha na shirin Investment in Digital and Creative Enterprise (iDICE).

An ba ta muƙamin ne a 2024 ƙarƙashin ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Fa’ida Da Muhimmancin Tattalin Lokaci Ga Ɗan’adam
  • Jarumar Kannywood Rahama Sadau ta yi aure
  • Za A Inganta Fannin Lafiya Da Sauran Ababen More Rayuwa A Sule Tankarkar
  • Shin Amurka Ta Manta Da Azabar “Babban Koma-Baya” Tare Da Haraji Mafi Yawa a Lokacin Na Tsawon Kusan Karni?
  • An Bude Taron Mutum-Mutumin Inji Na Duniya Na 2025 A Yau Juma’a
  • Sai Ƴan Siyasa Sun Haɗa Kansu Sannan Za Su Iya Tunkarar APC A 2027 – Lukman
  • Tinubu zai kashe tiriliyan 1.5 wajen gina layin dogo na zamani a birnin Kano
  • Ziyarar Manzon Allah (SAW) A Madinah (1)
  • Kauyuka 30 Sun Yi Zanga-zanga Kan Ta’addancin ‘Yan Bindiga A Zamfara