Aminiya:
2025-11-26@05:36:09 GMT

’Yan bindiga sun sake kai hari a Kwara, sun sace mutum 11

Published: 26th, November 2025 GMT

’Yan bindiga sun yi garkuwa da aƙalla mutum 11 mazauna garin Isapa da ke kusa da Eruku a Ƙaramar Hukumar Ekiti ta Jihar Kwara.

Harin ya faru ne sa’o’i kadan bayan sakin wasu masu ibada da aka yi garkuwa da su suna tsaka da ibada a coci.

An haramta cin naman Kare da Kyanwa a Indonesia An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a Kebbi

A cocin CAC da ke Ekuru, ana gudanar da bikin godiya domin murnar ’yantar da mambobi 18 da aka yi garkuwa da su kusan wata guda da ya gabata, sai ’yan bindiga suka kutsa suka yi garkuwa da mutum 38 bayan sun harbe uku har lahira.

Sabon harin, wanda ya faru da misalin ƙarfe 6:00 na yammacin Litinin, an ce ’yan bindiga kimanin 20 zuwa 30 ne suka kai shi.

Bayanai sun una cewa maharan su rika yin harbi ta ko’ina yayin da suke kutsa cikin garin, lamarin da ya sa mutane suka ranta a na kare.

Wata tsohuwa ta ji rauni sakamakon harbin kan mai uwa da wabi.

Wani jagoran al’umma da bai amince a bayyana sunansa ba, ya tabbatar da lamarin, inda ya ce: “Mutane 11 aka yi garkuwa da su, bakwai daga cikin su ’yan gida ɗaya. Waɗanda aka sace sun haɗa da mace mai juna biyu, masu shayarwa biyu da kuma kananan yara.”

Shaidar y ace sunaye mutanen sun hada da Talatu Kabiru, 20, Magaji, 6, Kande, 5, Hadiza, 10, Mariam, 6, Saima, 5, Habibat (mahaifiya), Fatima Yusufu (mahaifiya), Sarah Sunday, 22 (mai juna biyu), Lami Fidelis, 23 (uwa mai shayarwa) da kuma Haja Na Allah, ita ma uwa mai shayarwa.

Shaidun gani da ido sun ce ’yan bindigar sun bi wasu sassa na garin, inda suka bar alamun ramukan harsashin harbe-harbe a bangon gidaje da ƙofofi.

An gano harsashin bindiga AK-47 da aka harba daga wurare da dama bayan ’yan bindigar sun ja da baya tare da mutanen da suka yi garkuwa da su.

Lamarin ya haifar da tsananin tashin hankali a yankin da makotan garuruwa, yayin da jami’an tsaro da ’yan sa-kai ke ƙara ƙoƙari wajen gano maharan da ceto waɗanda aka sace.

Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kwara, Adekimi Ojo, ya tabbatar da lamarin ga yana mai cewa: “Eh, lamarin ya faru, amma ba zan iya cewa komai da yawa ba yanzu ba. Ina gab da shiga Isapa daga Ilorin. Zan ba da rahoto idan na isa.”

A yanzu haka dai Najeriya na fuskantar ɗaya daga cikin mafi munin matsalolin tsaro a tarihin ta. Hakan dai ya haifar da rufe makarantu da dama, musamman a Arewacin ƙasar.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Kwara Masu Garkuwa da mutane yi garkuwa da su yan bindiga

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan bindiga sun kashe ɗan kasuwa, sun sace matarsa a Bauchi

Ana zargin wasu ’yan bindiga da kashe wani fitaccen ɗan kasuwa, Alhaji Muhammad Bakoshi, lokacin da suka kai hari garin Zalau da ke Ƙaramar Hukumar Toro a Jihar Bauchi.

Bayan kai hari, sun sace ɗaya daga cikin matansa, Hannatu Muhammad.

Tinubu ya dakatar da ’yan sanda daga tsaron manyan mutane a Najeriya An ceto mutum 38 da aka sace a cocin Kwara — Tinubu

Wani mazaunin yankin, Shamsuddeen Hashimu Zalawa, ya shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar sun je gidan mutumin da tsakar dare.

Ya ce sun dinga harbe-harbe ba ƙaƙƙautawa, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin firgici.

Ya ƙara da cewa sun nufi gidan Bakoshi kai-tsaye, wanda hakan ya sa wasu ke zargin ko turo su aka yi.

Ɗan kasuwar mutum ne da ke taimakon jama’a musamman a sha’anin tsaro da kuma sabgogin maharba.

Haka kuma, ya kasance jami’in ladabtarwa a ƙungiyar First Aid ta JIBWIS a Zalau.

Zalawa, ya ce Bakoshi yana da mata biyu.

’Yan bindigar sun tafi da babbar matarsa, yayin da suka bar ƙaramar matarsa wacce ba ta jima da haihuwa ba.

Ƙoƙarin jin karin bakin kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi, bai yi nasara ba zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • DAGA LARABA: Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane?
  • An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a Kebbi
  • ’Yan bindiga sun sace mutum 8 a Kano
  • ’Yan bindiga sun yi yi garkuwa da mutane 11 a Kwara
  • Amarya ta yi wa angonta yankan rago bayan kwana 3 da aurensu a Katsina
  • ’Yan bindiga sun kashe ɗan kasuwa, sun sace matarsa a Bauchi
  • Najeriya : An sako mutum 38 da ‘yan bindiga suka sace a jihar Kwara_Tinubu
  • An ceto mutum 38 da aka sace a cocin Kwara — Tinubu
  • An gano wurin da ’yan bindiga ke tsare da ɗalibai 25 da aka sace a Kebbi