Tsaron makarantu: ’Yan Sanda da Shugabannin Makarantu sun tsara sabbin matakai a Gombe
Published: 25th, November 2025 GMT
Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Gombe ta ƙaddamar da sabbin matakan ƙarfafa tsaro a makarantu bayan wani taron tattaunawa da aka gudanar tsakanin Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, Bello Yahaya, da shugabannin Ƙungiyar Malaman Sakandare reshen jihar.
An gudanar da taron ne a Hedikwatar Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Gombe, bisa umarnin Sufeton ’Yan Sanda na Ƙasa, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, na ƙara tsaurara tsaro a makarantu a faɗin ƙasar nan.
Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi ya bayyana cewa tattaunawar ta mayar da hankali kan duba tsarin tsaro na yanzu a makarantu, musamman waɗanda ke yankunan da ke da ƙalubale, tare da gano wuraren da ake buƙatar gaggawar gyara.
CP Bello Yahaya ya tabbatar da kudirin Rundunar ’Yan Sanda ta Najeriya na ci gaba da kare cibiyoyin ilimi, yana mai cewa makarantu dole ne su kasance wurare masu aminci domin koyo da koyarwa.
Ya jaddada muhimmancin yin nazarin tsaro a kai a kai, tsara matakan rigakafi, da kuma tabbatar da ci-gaba da haɗin gwiwa tsakanin shugabannin makarantu, Ma’aikatar Ilimi da hukumomin tsaro.
Kwamishinan ya bayyana cewa rundunar ta ƙara karfafa sintiri, sa ido, da kuma gaggawar amsa kira a yankunan makarantu da aka fi ganin haɗarin tsaro.
Ya kuma bukaci shugabannin makarantu su riƙa kasancewa a shirin tuntuɓar ofisoshin ’yan sanda mafi kusa, tare da hanzarta ba da rahoton duk wani abin da ya haifar da zargi.
Ya yaba wa shugabannin ANCOPSS bisa jajircewarsu wajen aiki tare da hukumar ’yan sanda domin ƙarfafa tsaro a makarantu.
A nasu ɓangaren, shugabannin ANCOPSS sun gode wa rundunar ’yan sanda bisa ƙoƙarin da take yi na tabbatar da lafiyar dalibai da malamai, tare da alƙawarin yin aiki kafada da kafaɗa da rundunar da Ma’aikatar Ilimi domin ƙarfafa duk tsare-tsaren tsaro a makarantun sakandare.
Rundunar ta kuma yi kira ga iyaye, malamai, shugabannin al’umma, da mazauna unguwanni da su kasance masu lura da faɗakarwa, tare da tallafa wa duk wani yunƙurin inganta tsaro a makarantu, domin kiyaye rayuwar ɗalibai nauyi ne da ya rataya a kan kowa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: tsaro a makarantu
এছাড়াও পড়ুন:
Rundunar Sojan Iran Tana Cikin Shirin Mayar Da Martani Akan Kowace Barazana
Kwamandan sojan kasa na Rudnunar sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran Birgerdiya Janar Ali Jahanshahi ya ce; Sojojin kasar a shirye suke su mayar da martani akan duk wata barazana daga abokan gaba saboda suna da zaratan mayaka da kuma sabbin makamai.”
Har ila yau Ali Jahanshahi ya ce; Sojojin za kuma su yi amfani da kwarewar da tsofaffin sojoji suke da ita, haka nan kuwa darussan da su ka koya daga kallafaffen yakin kwanaki 12 da HKI.
Janar Jahanshahi ya kuma ce; A wannan lokacin kwarewar da sojojin kasa na Iran suke da su, ta kai koli saboda wararrun masana da kuma amfani da fannoni mabanbanta na ilimomi, musamman kirkirarriyar Fasaha.”
A dalilin hakan, sojojin suna cikin Shirin mayar wa da abokan gaba martani idan su ka kawo wani hari.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Madagascar: An Bayyana Jadawalin Farko Na Gwamnatin Rikon-Kwarya Da Kuma Manyan Zabuka November 22, 2025 Unifil: Girmama Hurumin Kasar Lebanon Ne Ginshikin Kuduri Mai Lamba 1701 November 22, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 160 November 22, 2025 Duniyarmu A Yau: Sabon Kuduri Mai Yin Allawadai Da Iran A Hukumat IAEA November 22, 2025 Ghalibaf: Makiya Sun Sawya Dabarbarun Yaki Da Iran November 22, 2025 Tsohon Ma’aikacin CIA Ya Ce HKI Ta Yi Barazanar Amfani Da Makaman Nukliya Kan Iran November 22, 2025 Yan Majalisar Dokokin Amurka Sun Sami Rarrabuwar Kai Dangane Da ‘Keshe Kiristoci A Najeriya’ November 22, 2025 Kasar Ukraine Ta Ki Amincewa Da Sabon Shirin Amurka Na Kawo Karshen Yaki A Kasar November 22, 2025 Yan Wasan Kasar Iran Sun tashi Da Lambobin Yabo 81 A Wasannin Zumunci Tsakanin Kasashen Musulmi November 22, 2025 Shugaban Rasha yace Ba zai Janye Ayyukan Soji Da Yake Yi A Kasar Ukrain Ba November 21, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci