Aminiya:
2025-11-27@14:46:02 GMT

An rantsar da sabon shugaban kasa a Guinea-Bissau bayan juyin mulkin sojoji

Published: 27th, November 2025 GMT

Sojojin Guinea-Bissau sun naɗa Janar Horta Nta Na Man a matsayin sabon shugaban ƙasar na rikon kwarya, kwana ɗaya bayan sun yi juyin mulki tare da kama shugaban ƙasar, Umaro Sissico Embalo.

Sojojin dai sun kwace mulkin ne yayin da ake shirin bayyana sakamakon zaɓen kasar mai cike da takaddama.

Majalisar Wakilai ta nemi gwamnati ta gaggauta dauko Jonathan daga Guinea Bissau Abubuwa 20 da ya kamata ku sani game da Sheikh Dahiru Bauchi

“Na rantsar da kaina a matsayin shugaban Babban Kwamandan Soja,” in ji Janar Horta bayan ya karbi rantsuwar aiki a wani biki da aka gudanar a hedkwatar sojoji a ranar Alhamis, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito.

Daruruwan sojoji dauke da makamai sun kasance a wurin rantsuwar.

A ranar Laraba, kwana guda bayan manyan ’yan takara biyu a zaɓen shugaban ƙasa mai cike da takaddama kowannensu ya ayyana nasara, wata ƙungiyar hafsoshin soja ta bayyana cewa ta karɓi “cikakken iko” a ƙasar.

Sojojin sun karanta sanarwa a talabijin, suna bayyana cewa sun dakatar da tsarin zaɓe “har sai an ba da sanarwa ta gaba.”

Sun kifar da Shugaba Umaro Sissoco Embalo a sabon lamari na rikice-rikicen siyasa da ke yawan faruwa a ƙasar.

Wata ƙungiyar hafsoshin sojoji ta bayyana cewa ta karɓi cikakken iko da mulkin ƙasar, kwana guda bayan manyan ’yan takara biyu, Shugaba Umaro Sissoco Embalo da Fernando Dias, kowannensu ya yi ikirarin samun nasara.

Sojojin sun bayar da umarnin dakatar da tattara sakamakon zaɓen har sai an ba da sanarwa ta gaba.

Haka kuma sun bayar da umarnin rufe dukkan iyakokin ƙasa da na sama da ruwa, tare da sanya dokar hana fita da dare.

“An yin min juyinmulki,” in ji Embalo a zantarwarsa da gidan talabijin na Faransa France24 ta wayar tarho, yana mai cewa “yanzu haka ina hedkwatar babban hafsan sojoji.”

Shugaban babbar jam’iyyar adawa ta PAIGC, Domingos Simoes Pereira, ma an kama shi, in ji Haque. “Haka kuma mun ji cewa sojoji na ƙoƙarin katse intanet. An kuma sanya dokar hana fita.”

Shugaban rundunar tsaron fadar shugaban ƙasar, Denis N’Canha, shi ne dai sojan da ke jagorantar juyin mulkin.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Amurka za ta tallafa wa Nijeriya daƙile matsalar tsaro

Gwamnatin Najeriya ta ce Amurka ta amince za ta ƙara faɗaɗa haɗin gwiwar tsaro tsakaninsu, wanda ya haɗa da samar da karin bayanan sirri, makamai da sauran kayan yaƙi, domin ƙarfafa yaƙi da ’yan ta’adda da ƙungiyoyin masu tayar da kayar baya a ƙasar.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Mashawarci na Musamman ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu kan Bayar da Bayanai da Tsara Dabaru, Bayo Onanuga ya fitar a ranar Litinin.

Atiku ya karɓi katin jam’iyyar ADC a hukumance Jarumin fina-finan Indiya Dharmendra ya rasu

Wannan dai ya biyo bayan jerin tattaunawa da aka gudanar a Washington tsakanin manyan jami’an Najeriya da na Amurka, domin zurfafa dangantakar tsaro da ƙulla sabbin hanyoyin haɗin gwiwa.

Tawagar Najeriya ƙarƙashin jagorancin mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, ta gana da jami’an majalisar dokokin Amurka, Fadar White House, ma’aikatar harkokin waje, da hukumomin tsaro na ƙasar.

A cikin tawagar akwai Antoni Janar na Tarayya, Lateef Fagbemi; Shugaban Ma’aikatan Tsaro, Janar Olufemi Oluyede; Shugaban Leƙen Asirin Tsaro, Laftanar Janar Emmanuel Undiandeye; da Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, tare da wasu wakilai daga ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro.

A yayin ganawar, tawagar Najeriya ta ƙaryata zargin da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi na cewa ana kashe Kiristoci a ƙasar, tana mai cewa matsalolin tsaron ƙasar babu wanda suka ƙyale domin kuwa suna shafar al’ummomi daban-daban ba tare da la’akari da addini ko ƙabila ba.

Zargin na Trump ya haifar da ƙalubale da dama a cikin ƙasar, inda hannayen jari suka zube, baya ga ta’azzarar matsalolin da ake gani a ’yan kwanakin nan.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Majalisar Wakilai ta nemi gwamnati ta gaggauta dauko Jonathan daga Guinea Bissau
  • Gwamna Kefas Ya Bayyana Alhininsa Bisa Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi
  • An Rutsa Da Tsohon shugaban Kasar Najeriya A Guine Bissau Bayan Juyin Mulki
  • Juyin mulki ya rutsa da Jonathan a Guinea-Bissau
  • Ɗan bindiga ya harbe sojoji 2 a fadar shugaban Amurka
  • Sojojin Sun Sanar Da Kwace Mulki A Kasar  Guinea Bissau
  • Sojoji sun yi juyin mulki a Guinea-Bissau
  • Tabarbarewar Tsaro na Barazana ga Siyasar Ƙasar Nan Gabanin Zaɓen 2027-Ado Doguwa
  • Amurka za ta tallafa wa Nijeriya daƙile matsalar tsaro