Gobarar tankar mai ta ƙone gidaje a Jihar Neja
Published: 25th, November 2025 GMT
Wata tankar mai ta yi gobara a wani gudan mai a yankin Tungan-Bunu da ke Ƙaramar Hukumar Rijau a Jihar Neja, lamarin da ya janyo ƙonewar gidaje da kadarori da masu yawa.
Shaidu sun ce gobarar ta tashi ne a lokacin da tankar take shirin sauke mai a ranar Litinin da yamma, inda wutar ta bazu zuwa gidajen da ke kusa.
Duk da cewa babu wanda ya rasa ransa, lamarin ya haifar da firgici inda mazauna yankin suka yi ta tserewa suka bar gidajensu yayin da tankar ke ci da wuta.
Tankar mai ta yi hatsari a hanyar Lapai-Agaie Amurka za ta tallafa wa Nijeriya daƙile matsalar tsaro Mayaƙan Boko Haram sun fille kan mata 2 a BornoA wani lamari ba daban, wata tankar mai ta kife a kan hanyar Lapai zuwa Agaie, lamarin da ya toshe hanya tare da haddasa cunkoson ababen hawa.
Shaidu sun ce tankar, wadda ke ɗauke da fetur daga Legas zuwa Gombe, ta kife ne da misalin karfe 10 na safe a ranar Litinin bayan jikinta ya rabu da kan motar, ya ƙetare hanya, abin da ya tayar da hankalin jama’a.
Wani mazaunin yankin, Malam Mahmud Abubakar, ya ce jami’an tsaro sun garzaya wajen domin tsare yankin, sannan aka tura ma’aikatan kashe gobara don kauce wa tashin wuta.
Ya ƙara da cewa lamarin ya faru ne a yankin Efu-Nda-Egbo na Ƙaramar Hukumar Lapai, inda ya haddasa cunkoson ababen hawa mai tsanani.
Kokarin tuntuɓar Darakta-Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), Abdullahi Baba Arah, bai yi nasara ba, domin bai amsa kiran wayar da wakilinmu ya yi masa ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gobara ranka tankar mai tankar mai ta
এছাড়াও পড়ুন:
Matsalar Tsaro: Gwamnatin Tarayya Ta Ba da Umarnin Rufe Makarantu 41 Nan Take
Gwamnatin Tarayya ta bada umarnin rufe makarantu arba’in da daya saboda matsalolin tsaro.
A wata takardar sanarwa da aka aikewa dukkan Shugabannin makarantu, wadda Daraktan Makarantu Manyan Sakandare na Ma’aikatar Ilimi ya sanya wa hannu, gwamnati ta bayyana cewa sakamakon ƙalubalen tsaro da ake fuskanta a wasu sassan ƙasar nan da kuma buƙatar kare duk wani yunkurin hari, Ministan Ilimi ya amince a rufe makarantun nan dltaje.
Ga jerin makarantu da abin ya shafa:
Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Minjibir, Jihar Kano Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Ganduje, Jihar Kano Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Zariya, Jihar Kaduna Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Kafanchan, Jihar Kaduna Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Bakori, da wacce ke Bwari, Abuja. Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Dayi, Jihar Katsina Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Daura, Jihar Katsina Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Tambuwal, Jihar Sakkwato Kwalejin Kimiyya ta Tarayya, Jihar Sakkwato Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Wurno, Jihar Sakkwato Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Gusau, Jihar Zamfara Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Anka, Jihar Zamfara Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Gwandu, Jihar Kebbi Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Birnin Yari, Jihar Kebbi Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Zuru, Jihar Kebbi Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Kazaure, Jihar Jigawa Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Kiyawa, Jihar Jigawa Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Hadejia, Jihar Jigawa Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Bida, Jihar Neja Kwalejin Gwamnatin Tarayya, New Bussa, Jihar Neja Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Kuta-Shiroro, Jihar Neja Akademiyar Gwamnatin Tarayya, Suleja, Jihar Neja Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Ilorin, Jihar Kwara Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Omu-Aran, Jihar Kwara Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Gwanara, Jihar Kwara Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Ugwolawo, Jihar Kogi Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Kabba, Jihar Kogi Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Ogugu, Jihar Kogi Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Bwari, Abuja Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Rubochi, Abuja Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Abaji, Abuja Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Potiskum, Jihar Yobe Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Buni-Yadi, Jihar Yobe Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Gashua, Jihar Yobe Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Michika, Jihar Adamawa Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Ganye, Jihar Adamawa Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Azare, Jihar Bauchi Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Misau, Jihar Bauchi Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Bajoga, Jihar Gombe Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Billiri, Jihar Gombe Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Zambuk Jihar Gombe.Takardar ta umarci Shugabannin makarantu da abin ya shafa su tabbatar da cikakken bin wannan umarni.
RN