An Fitar Da Kudurin Bayan Taron Kungiyar G20 Ba Tare Da Halartar Kasar Amurka Ba
Published: 23rd, November 2025 GMT
Shugabannin kasashen duniya da su ka halarci taron kungiyar G 20 sun amince da kudurin akan hanyoyin bunkasa tattalin arziki, sai dai ba a fitar da da cikakken bayani akan abinda ya kunsa ba.
Gwamnatin Donald Trump ta ki halartar taron na kungiyar G 20 da aka bude jiya a kasar Afirka Ta Kudu, da kuma yake zuwa karshe a yau Lahadi,sannan kuma ta yi kira da kar a kuskura a fitar da wani kuduri ba tare da wakilanta suna wajen ba.
Shugaban kasar Afirka Ta Kudu Cyril Ramaphosa ya bayyana cewa; Amincewa da kudurin wani sako ne akan cewa duniyar da bangarori mabanbanta suke tafiyar da ita, za ta iya daukar matakai.”
A baya kadan shugaban kasar Afirka ta Kudun ya mayar wa da Amurka martani da cewa kasarsa ba za ta mika wuya ga halayyar nuna karfi da Gadara ba.”
Mai Magana da yawun shugaban kasar Afirka Ta Kudu ya ce, an amince da kudurin ne a cikin jam’i, sai dai kuma kasar Argentina ta ce, ba ta cikin wadanda su ka amince da shi.
Shugaban kasar Argentina Javier Milei bai halarci taron na Afirka Ta Kudu ba saboda goyon bayan shugaba Trump na Amurka. Ministan harkokin wajen kasar ne Pablo Quirno ya wakilci kasarsa a wurin taron na Johannesburg.
A bisa yadda aka saba, Sai a karshen taron ne ake fitar da kuduri,amma da alama a wannan karon Afirka Ta Kudu tana son ganin an cimma matsaya ne da wuri akan batutuwan da ake da sabani a kansu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka An Kulla Yarjejeniyar Aikin Soja A Tsakanin Kasashen UAE Da Ethiopia November 23, 2025 Pezeshkian: Iran na Allawadai da hare-haren Isra’ila a kan Lebanon November 23, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 161 November 23, 2025 Esma’il Khatib: Isra’ila Na Fuskantar Manyan Ayyukan Leken Asiri Daga Iran November 23, 2025 An Gabatar Da Jawabin Bayan Taro Na Kungiyar G20 Duk Tare Da Kauracewar Amurka November 23, 2025 Zabebben Magajin Garin Birnin NewYork Ya Nanata Cewa HKI Tana Aikata Kissan Kiyashi A Gaban Trump November 23, 2025 Venezuela Ta Gargadi Amurka Kan Shirin Tada Hankali A Kan Iyakokin Kasar November 23, 2025 CAN: Yawan Yaran Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Ranar Jumma’a Sun Fi 300 November 23, 2025 Ribadu Ya Gana da Sakataren Yakin Amurka Kan Batun Kashe Kiristoci A Nijeriya November 22, 2025 Daliban Jami’ar st Gorges Ta Birnin London Sun yi Zanga-zangar Nuna Adawa Da Daukar Tsohon Sojan Isra’ila Aiki November 22, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Afirka Ta Kudu kasar Afirka ta
এছাড়াও পড়ুন:
Nijar: Dubban Mutane Sun Tarbi Janar Thiani Bayan Komarwa Birnin Yamai
A ranar Alhamis da dare ne janar Thiani wanda ya karare kasar ta Nijar a cikin motoci a wani ran gadi da shi ne irinsa na farko da wani shugaban kasar ya yi, ya sami kyakkyawar tarba a wurin mazauna babban birnin.
Kafar wasta labaru ta “Afircanews” ta nakalto wani dan fafutuka mai suna Zakari Bizo yana nuna jin dadinsa da komawar shugaban kasar sannan ya kara da cewa, batun gina kasa da hadin kan al’umma shi ne abinda suke son ganin ya tabbata.”
A tsawon lokacin da yake rangadin, shugaban kasar ta Nijar ya yi kira ga al’umma da su zama masu tsayin daka,su kuma sojoji su kasance masu zama cikin fadaka da sa ido.
Ana daukar wannan ziyarar ta shugaban kasar a fadin kasar a matsayin kokarin sake tabbatar da hadin kai a tsakanin al’ummar kasar.
Fiye da shekaru 10 kenan Jamhuriyar Nijar take fuskantar matsalolin ta’addanci.
Wani mai fafutukar, Dr.Iro Tanimou ya fada wa manema labaru cewa, ziyarar da shugaban kasar ya kai a fadin kasar, yana nuni ne da sadaukar da kansa,kuma abin alfahari ne yadda ya ziyarci wurare da suke akan iyakokin Burkina Faso da Aljeriya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Afirka Ta Kudu: Rashin Halartar Amurka Taron G-20 Ba Zai Yi Wani Tasiri Ba November 22, 2025 Rundunar Sojan Iran Tana Cikin Shirin Mayar Da Martani Akan Kowace Barazana November 22, 2025 Madagascar: An Bayyana Jadawalin Farko Na Gwamnatin Rikon-Kwarya Da Kuma Manyan Zabuka November 22, 2025 Unifil: Girmama Hurumin Kasar Lebanon Ne Ginshikin Kuduri Mai Lamba 1701 November 22, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 160 November 22, 2025 Duniyarmu A Yau: Sabon Kuduri Mai Yin Allawadai Da Iran A Hukumat IAEA November 22, 2025 Ghalibaf: Makiya Sun Sawya Dabarbarun Yaki Da Iran November 22, 2025 Tsohon Ma’aikacin CIA Ya Ce HKI Ta Yi Barazanar Amfani Da Makaman Nukliya Kan Iran November 22, 2025 Yan Majalisar Dokokin Amurka Sun Sami Rarrabuwar Kai Dangane Da ‘Keshe Kiristoci A Najeriya’ November 22, 2025 Kasar Ukraine Ta Ki Amincewa Da Sabon Shirin Amurka Na Kawo Karshen Yaki A Kasar November 22, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci