Aminiya:
2025-11-25@15:48:15 GMT

Chelsea za ta kece raini da Barcelona a Gasar Zakarun Turai

Published: 25th, November 2025 GMT

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea za ta karɓi baƙuncin Barcelona a wasan mako na biyar na gasar cin Kofin Zakarun Turai (Champions League) da ke ci gaba da gudana a kakar nan.

Wasan da za a buga a filin Stamford Bridge, yana zuwa ne bayan da ’yan wasan Barcelona suka ƙauracewa atisayi a bainar jama’a domin ɓoye salon horon su.

Amarya ta yi wa angonta yankan rago bayan kwana 3 da aurensu a Katsina Matsalar Tsaro: Gwamnonin Arewa sun shirya taron gaggawa

Chelsea da Barcelona sun haɗu sau 14 a gasar Zakarun Turai, inda kowacce ƙungiyar ta yi nasara huɗu, sannan aka yi kunnen doki shida.

Wannan shi ne karo na farko da ƙungiyoyin za su kara tun kakar 2017/18 a zagayen ’yan 16, lokacin da Barcelona ta yi nasarar tsallakawa zagaye na gaba, bayan cin jimilla 4–1 a waje da gida — wanda aka tashi 1–1 a Stamford Bridge da kuma nasarar 3–0 a Sifaniya.

Chelsea ta sha kashi sau ɗaya ne kawai daga wasanninta bakwai da ta yi a gida a gasar Zakarun Turai da Barcelona — inda ta yi nasara huɗu tare da tashi kunnen doki biyu a Stamford Bridge.

Haka kuma, Chelsea ta  cin wasa biyu a fafatawa 61 baya a gasar Zakarun Turai a gida, sannan ba ta yi rashin nasara ba a fafatawa 16, wadda ta ci 12 da canjaras huɗu — tun bayan doke ta 1-0 da Valencia a Satumbar 2019.

A gefe guda, Barcelona ta yi rashin nasara uku ne kacal daga wasa 20 a Champions League da ta fuskanci wata ƙungiyar Ingila, bayan cin 13 da canjaras huɗu da kuma rashin nasara ɗaya daga fafatawa 11, baya ga samun nasara a karawa takwas da canjaras biyu daga ciki.

Lamine Yamal, wanda zai cika shekara 18 da kwana 135 ranar Talata, ya riga ya zura ƙwallo bakwai a Champions League kafin cikarsa shekara 19.

Yana buƙatar ƙarin uku domin ya yi daidai da tarihin Kylian Mbappé a wannan rukuni.

Barcelona ta zura ƙwallo 96 a raga cikin wasanninta 20 na baya-bayan nan a Champions League.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Barcelona Gasar Zakarun Turai a gasar Zakarun Turai da Barcelona

এছাড়াও পড়ুন:

An Fitar Da Kudurin Bayan Taron Kungiyar G20 Ba Tare Da Halartar Kasar Amurka Ba

Shugabannin kasashen duniya da su ka halarci taron kungiyar G 20 sun amince da kudurin akan hanyoyin bunkasa tattalin arziki, sai dai ba a fitar da da cikakken bayani akan abinda ya kunsa ba.

Gwamnatin Donald Trump ta ki halartar taron na kungiyar G 20 da aka bude jiya a kasar Afirka Ta Kudu, da kuma yake zuwa karshe a yau Lahadi,sannan kuma ta yi kira da kar a kuskura a fitar da wani kuduri ba tare da wakilanta suna wajen ba.

Shugaban kasar Afirka Ta Kudu Cyril Ramaphosa ya bayyana cewa; Amincewa da kudurin wani sako ne akan cewa duniyar da bangarori mabanbanta suke tafiyar da ita, za ta iya daukar matakai.”

 A baya kadan shugaban kasar Afirka ta Kudun ya mayar wa da Amurka martani da cewa kasarsa ba za ta mika wuya ga halayyar nuna karfi da Gadara ba.”

Mai Magana da yawun shugaban kasar Afirka Ta Kudu ya ce, an amince da kudurin ne a cikin jam’i, sai dai kuma kasar Argentina ta ce, ba ta cikin wadanda su ka amince da shi.

Shugaban kasar Argentina Javier Milei bai halarci taron na Afirka Ta Kudu ba saboda goyon bayan shugaba Trump na Amurka. Ministan harkokin wajen kasar ne Pablo Quirno ya wakilci kasarsa a wurin taron na Johannesburg.

A bisa yadda aka saba, Sai a karshen taron ne ake fitar da kuduri,amma da alama a wannan karon Afirka Ta Kudu tana son ganin an cimma matsaya ne da wuri akan batutuwan da ake da sabani a kansu.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka  An Kulla Yarjejeniyar Aikin Soja A Tsakanin Kasashen UAE Da Ethiopia November 23, 2025 Pezeshkian: Iran na Allawadai da hare-haren Isra’ila a kan Lebanon November 23, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 161 November 23, 2025 Esma’il Khatib: Isra’ila Na Fuskantar Manyan Ayyukan Leken Asiri Daga Iran November 23, 2025 An Gabatar Da Jawabin Bayan Taro Na Kungiyar G20 Duk Tare Da Kauracewar Amurka November 23, 2025 Zabebben Magajin Garin Birnin NewYork Ya Nanata Cewa HKI Tana Aikata Kissan Kiyashi A Gaban Trump November 23, 2025 Venezuela Ta Gargadi Amurka Kan Shirin Tada Hankali A Kan Iyakokin Kasar November 23, 2025 CAN: Yawan Yaran Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Ranar Jumma’a Sun Fi 300 November 23, 2025 Ribadu Ya Gana da Sakataren Yakin Amurka Kan Batun Kashe Kiristoci A Nijeriya November 22, 2025 Daliban Jami’ar st Gorges Ta Birnin London Sun yi Zanga-zangar Nuna Adawa Da Daukar Tsohon Sojan Isra’ila Aiki November 22, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Amarya ta yi wa angonta yankan rago bayan kwana 3 da aurensu a Katsina
  • Wakilin MDD Ya Bukaci Goyon Bayan Iran Wajen Tabbatar Da Zaman Lafiya A Yamen
  • Slot na fuskantar matsin lamba saboda rashin kataɓus a Liverpool
  • Habasha: Bayan Shekaru 10,000 Dutsen Hayli Gubbi Ya Yi Aman Wuta
  • NAJERIYA A YAU: Halin Da Shirin Samar Da Tsaro A Makarantun Najeriya Ke Ciki
  • An Fitar Da Kudurin Bayan Taron Kungiyar G20 Ba Tare Da Halartar Kasar Amurka Ba
  • An Gabatar Da Jawabin Bayan Taro Na Kungiyar G20 Duk Tare Da Kauracewar Amurka
  • Gwamnatin Yobe ta ba da umarnin rufe makarantun kwana a jihar
  • ’Yan Sanda a Zamfara Sun Ceto Mutane 25 Bayan Dakile Harin ’Yan Bindiga a Damba