Mbappe ya ci ƙwallaye 4 rigis a wasan Madrid da Olympiacos
Published: 27th, November 2025 GMT
Ɗan wasan gaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid, Kyalian Mbappe ya samu nasarar zura kwallaye huɗu rigis a ragar Olympiacos a wasan mako na biyar na kofin zakarun nahiyyar turai da suka buga a yammacin jiya Laraba.
Real Madrid dai caskara Olympiacos 4-3 ne a wasan, lamarin da ya ba ta damar haɗa maki 12 cikin fafatawa biyar.
Kawo yanzu dai Mbappe ya shiga gaban Victor Osimhen na Galatasaray wajen yawan zura ƙwallaye a raga a gasar ta kakar nan, inda Mbappe ya ke da 9, yayin da Osimhen wanda ke fama da rauni ya zura shida a raga.
Kafin wannan nasarar, Real Madrid ba ta ci wasa ko ɗaya ba a cikin fafatawa bakwai a gasar Zakarun Turai da ta fuskanci ƙungiyoyin Girka ba.
Yanzu haka dai Real Madrid ta koma mataki na biyar a saman teburin yayin da ya rage wasanni uku a kammala zagayen rukuni na gasar ta wannan kaka.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Andrea Thompson ta zama mace mafi ƙarfi a duniya
An naɗa Andrea Thompson, ’yar ƙasar Birtaniya, a matsayin mace mafi ƙarfi a duniya.
Wannan na zuwa ne bayan tabbatar da cewa wanda aka bayyana a matsayin zakara — Jammy Booker — tun da farko namiji ne da aka sauya masa halitta zuwa mace, lamarin da ya sa aka soke nasararsa bisa saɓawa dokokin gasar.
Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro Real Madrid za ta yi karon-batta da Olympiacos a Gasar Zakarun TuraiThompson mai shekaru 43, ta karɓi lambar yabon ne daga masu shirya gasar nunin ƙarfi ta duniya, kwanaki biyu bayan kammala bikin a Arlington da ke birnin Texas na Amurka, wanda aka gudanar a daga 20 zuwa 23 ga watan Nuwamba.
Gasar nuna ƙarfin ta duniya tana da tsauraran ƙa’idoji, inda ake bai wa ’yan takara damar fafatawa ne kawai bisa jinsinsu na asali domin tabbatar da adalci.
A gasar bana, Thompson ta ƙare a matsayi na biyu bayan kammala fannonin wasanni guda shida da suka haɗa da ɗaga nauyi da sauran gwaje-gwaje a rukunin mata.