Atiku ya karɓi katin jam’iyyar ADC a hukumance
Published: 24th, November 2025 GMT
Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya karɓi katin kasancewa ɗan jamʼiyyar ADC a hukumance.
Atiku wanda ya yi wa jam’iyyar PDP takarar kujerar shugaban ƙasar Zaɓen 2023, ya karɓi katin ya yi rajistar zama tabbataccen ɗan jam’iyyar ADC a mazaɓarsa ta Jada da ke jihar Adamawa.
Jarumin fina-finan Indiya Dharmendra ya rasu Slot na fuskantar matsin lamba saboda rashin kataɓus a LiverpoolYa sanar da hakan ne a shafinsa na X, inda ya wallafa hotuna riƙe da katin sabuwar jami’yyarsa, da gajeren rubutu da ke nuna ya shiga jam’iyyar a hukumance.
A ranar 14 ga watan Yulin 2025 ne cikin wata sanarwa Atikun ya bayyana ficewa daga PDP ba tare da ɓata lokaci ba.
Tun a wancan lokacin dai Atikun ya kuma ce wajibi ne ya raba gari da jam’iyyar ta PDP bisa la’akari da yadda ta sauka daga tubalinta na asali.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Atiku Abubakar Jihar Adamawa
এছাড়াও পড়ুন:
Atiku ya nemi a ayyana dokar ta-ɓaci kan satar ɗalibai a Najeriya
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya roƙi Gwamnatin Tarayya da ta ayyana dokar ta-ɓaci saboda yawaitar sace-sacen ɗalibai da malamai a Najeriya.
Atiku, ya yi wannan kira ne bayan harin da “yan bindiga suka kai yankin Papiri da ke Ƙaramar Hukumar Agwara ta Jihar Neja.
Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai a Neja Sojoji sun bar makarantar Maga kafin ’yan bindiga su kai hari — Gwamna KebbiMaharan sun sace ɗalibai da ma’aikatan makarantar St. Mary’s Catholic.
Har yanzu hukumomi ba su tabbatar da adadin mutanen da aka sace ba.
Harin ya auku ne bayan sace ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka a Ƙaramar Hukumar Maga, a Jihar Kebbi, lamarin da ya nuna yadda rashin tsaro ya ƙara taɓarɓarewa, musamman a Arewa.
A wani saƙo da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Atiku ya nuna damuwarsa.
“Abin takaici ne sosai. Har yaushe za a ci gaba da rasa rayuka ba tare da an ɗauki matakin gaggawa ba?”
Ya ce lokaci ya yi da gwamnati za ta ɗauki tsauraran matakai.
Ya kuma buƙaci ƙarin tsaro a makarantu domin kare ɗalibai da malamai daga hare-haren ’yan bindiga.