Aminiya:
2025-11-23@20:18:08 GMT

’Yan sanda sun ƙaryata jita-jitar kai wa coci hari a Gombe

Published: 23rd, November 2025 GMT

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta ce labarin da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta na kai wa cocin ECWA da ke Kashere hari, ba gaskiya ba ne.

Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi ne, ya bayyana haka, inda ya ce sun bincika tare da gano cewar jita-jita ce.

Ya ce DPO na Pindiga da shugaban ofishin ’yan sanda na Kashere, sun tuntuɓi wani dattijo da ya halarci cocin domin yin addu’a a ranar Lahadi.

Dattijon ya shaida musu cewa babu wani abu da ya faru, kuma ’yan sanda suna harabar cocin tun safe a domin kula da sha’anin tsaro kamar yadda suka saba.

Rundunar ta ce yaɗa irin wannan jita-jitar na iya tayae da hankalin jama’a.

Ta kuma ce ta fara bincike domin gano wanda ya ƙirƙiri wannan labari domin ɗaukar matakin doka a kansa.

DSP Abdullahi, ya roƙi jama’a da su kwantar da hankalinsu, tare da ci gaba da harkokinsu, inda ya tabbatar da cewa ’yan sanda za su ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’ar jihar.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Sanda Cocin ECWA hari

এছাড়াও পড়ুন:

Sojoji sun bar makarantar Maga kafin ’yan bindiga su kai hari — Gwamna Kebbi 

Gwamna Nasir Idris na Jihar Kebbi, ya nemi ƙarin bayani kan dalilin ɗauke sojojin da ke gadin makarantar GGCSS Maga, gabanin harin da ’yan bindiga suka kai tare da sace ɗalibai 25.

Gwamnan, ya ce gwamnati ta riga ta sanar da hukumomin tsaro game da yiwuwar kai hari, amma sojojin suka bar makarantar da misalin ƙarfe 3 na dare.

Zargi: Majalisar Kano ta dawo da shugaban ƙaramar hukumar Rano kan kujerarsa Gwamnatin Neja ta zargi makarantar da aka sace wa dalibai da kin bin umarninta

“An tura sojoji, amma sun bar makarantar da misalin ƙarfe 3 na dare, sannan ƙarfe 3:45 harin ya faru. Wa ya bayar da izinin su bar makarantar a wannan lokaci mai muhimmanci?” in ji Idris.

Ya ce bayan barin makarantar da sojoji suka yi ƙasa da awa guda ’yan bindiga suka kai hari.

Ya ce barin makarantar da sojojin suka yi, ya saɓa wa alƙawuran da aka yi na ƙarfafa tsaro a makarantu da ke kan iyakar jihar.

Idris, ya ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya da ta jihar na aiki tuƙuru don ceto ɗaliban da aka sace.

Gwamnan, ya bayyana cewa an umarci malaman addini da su yi addu’a domin samun zaman lafiya da kuɓutar da waɗanda aka sace.

Idris, ya ce abin da ya faru na nuna cewa akwai maƙiya da ke ƙoƙarin kawo cikas ga ci gaban jihar.

A yayin ziyarar nuna goyon baya, Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya ce abin da ya faru abin damuwa ne, musamman ma a lokacin da Kebbi ke samun ci gaba mai kyau.

Ya ƙara da cewa duk wani yunƙuri na daƙile ci gaban jihar ba zai yi nasara ba, kuma ya shawarci gwamnan da ya dage.

Ajaero ya ce, “Wannan kawo cikas ne, amma duk wani yunƙuri na daƙile ci gaban jihar ba zai yi nasara ba. Muna tare da ku.”

A halin yanzu, rundunar sojin ƙasa ta fara bincike kan dalilin da ya sa sojojin da aka tura makarantar suka bar wajen aiki kafin aukuwar harin.

Majiyoyin tsaro sun ce a yanzu haka an fara binciken wasu manyan jami’ai kan lamarin.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An ceto mutum 38 da aka sace a cocin Kwara — Tinubu
  • Barin jama’a su kare kansu ne ke rura rashin tsaro — Sojoji
  • Ma’aikatan lantarki na shirin shiga yajin aiki a faɗin Najeriya 
  • ’Yan Sanda a Zamfara Sun Ceto Mutane 25 Bayan Dakile Harin ’Yan Bindiga a Damba
  • Gwamnatin Tarayya ta musanta jita-jitar rufe dukkanin makarantu a faɗin Najeriya
  • Gwamnatin Katsina Ta Umurci a Gaggauta Rufe Dukkan Makarantun Jihar
  • Mutane 315 ne suka ɓace bayan hari a makaranta Neja
  • Sojoji sun bar makarantar Maga kafin ’yan bindiga su kai hari — Gwamna Kebbi 
  • Hukumar Hisbah Ta Rufe Wani Wuri da Ake Zargin Ana Aikata Badala A Kano