Harin Ƴan Bindiga Ya Yi Sanadin Kashe Ɗansanda Da Wasu Mutane 4 A Kwara
Published: 10th, August 2025 GMT
Ƴan bindiga sun kashe mutane biyar, ciki har da wani Ɗansanda, a sabon harin da suka kai garin Babanla a ƙaramar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara. Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, kwanaki ƙalilan bayan kisan wasu matafiya uku da garkuwa da wasu biyu a yankin.
Mai magana da yawun rundunar ƴansandan jihar, Toun Ejire-Adeyemi, ta ce maharan sun kai ɗaruruwa akan babura ne suka farmaki garin, kuma suka kai hari ofishin Ƴansanda na yankin, sannan suka yi ɓarna a kasuwar garin.
Ta bayyana cewa haɗin gwuiwar Ƴansanda, da Sojoji, da Jami’an sa-kai da mafarauta ya fatattaki maharan tare da dawo da zaman lafiya, inda yanzu aka fara sumame don kamo su. A ranar Lahadi, kwamishinan Ƴansanda Adekimi Ojo da Daraktan DSS na jihar sun ziyarci Babanla don tantance halin tsaro, tare da ganawa da Sarkin garin, Oba Yusuf Aliyu Alabi Arojojoye II.
Kwamishinan ya bayar da umarnin ci gaba da sintiri da tattara bayanan sirri tare da tura ƙwararrun jami’an bin sawu, yayin da DSS ta yi alƙawarin bayar da goyon baya da bayanan sirri domin kama duk masu hannu a harin. An kuma roƙi jama’a su kwantar da hankula, su kasance masu lura, tare da bayar da sahihan bayanai ga jami’an tsaro.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Kwara
এছাড়াও পড়ুন:
A gaggauta sakin Sowore — Atiku
Madugun adawa a Nijeriya, Atiku Abubakar ya bukaci a gaggauta sakin fitaccen ɗan gwagwarmayar, Omoyele Sowore da ke tsare a hannun ’yan sandan kasar.
Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriyar wanda ya yi Allah-wadai da lamarin ya ce abin kunya ne cin zarafi da tawagar sa ido ta sufeto janar na ’yan sandan ƙasar suka yi wa Sowore.
Mahaifin Ɗan Bello ya rasu Abba ya yi alhinin hadiminsa da ’yan daba suka kashe a Kano“Bai dace a tsare Sowore ba, kuma hakan ya saba wa ka’ida. Dole ne a yi tur da lamarin,” in ji Atiku.
Ya ce laifin ɗan gwagwarmayar kawai shi ne don ya fito ya yi magana kan rashin shugabanci nagari da ake yi a Nijeriya.
Wasu rahotanni ma na bayyana cewa ana zargin ’yan sandan sun lakaɗa wa Sowore duka har ma an ƙarya masa hannu.
Wazirin na Adamawa ya ce wannan abin da ƴa nsanda suka aikata ba ga Sowore kaɗai ba ne, inda ya ce hakan ya nuna cewa za a far wa kowane ɗan Nijeriya da ya yi ƙoƙarin fitowa ya faɗi gaskiya.
“Don haka muna buƙatar a saki Sowore cikin gaggawa ba tare da gindaya wasu sharuɗa ba,” in ji Atiku.
A ranar Laraba ne dai aka bayar da rahoton tsare Sowore bayan da ya amsa gayyatar jami’an ’yan sanda domin amsa wasu tambayoyi.
A jiya Laraba ne dai aka bayar da rahoton tsare Sowore bayan amsa gayyatar da ofishin Babban Sufeton ’Yan sanda ya yi masa don ya amsa wasu tambayoyi da suke da alaka da zanga-zangar da tsofaffin ’yan sanda suka yi a makon jiya.
Haka kuma, an son Soworen ya bayar da bahasi kan zargin da ya yi na cewa, Babban Sufeton ya kara wa jami’an ’yan sandan da ke aiki a gidansa girma ba bisa ka’ida ba.
Sai dai ya yi watsi da zarge-zargen, inda ya bayyana su a matsayin borin kunya da hukumar ‘yan sandan take don “dauke hankalin jama’a daga abin kunyar da Babban Sufeton Kayode Egbetokun da kuma hukumar ‘yan sandan ke aikatawa.”
Tuni dai Kungiyar Kare Hakkin Bil’Adama ta Amnesty International ta fitar da sanarwar Allah wadai da kamun da aka yi wa Sowore wanda ta ce ya saba wa ‘yancinsa na fadin albakacin baki.
Haka kuma, Amnesty International ta bukaci a saki Omoleye Sowore nan take ba tare da gindaya masa wasu sharuda ba.