Gwamna Namadi Ya Gabatar da Kasafin Naira Biliyan 900 ga Majalisa
Published: 26th, November 2025 GMT
Daga Usman Muhammad Zaria
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya gabatar da kasafin kuɗi na shekarar 2026 na sama da naira biliyan 900 ga Majalisar Dokokin jihar.
Yayin gabatar da kasafin da aka lakaba wa suna “Kasafin Kirkire-kirkire da Sauyi Don Cigaban Jigawa II,” Gwamna Namadi ya ce za a ware sama da naira biliyan 693.
Gwamnan ya kuma ce sama da naira biliyan 208 za su tafi ne ga ayyukan yau da kullum.
A cewarsa, an ware sama da naira biliyan 310 ga bangaren ilimi da lafiya, yayin da kimanin naira biliyan 186 za su tafi ga hanyoyi da sufuri.
Malam Umar Namadi ya ƙara da bayyana cewa an ware sama da naira biliyan 74 ga bangaren noma da kiwo, sai naira biliyan 50.74 don wutar lantarki da makamashi, yayin da naira biliyan 12.68 za su tafi ga shirin ƙarfafa matasa.
Ya nuna cewa an tanadi naira biliyan 25.4 don ruwa da tsafta, sannan naira biliyan 35.4 don muhalli da sauyin yanayi.
Gwamna Namadi ya kuma gabatar da sama da naira biliyan 288 don ayyukan kananan hukumomi 27 na jihar.
Radio Nigeria ya ruwaito cewa kasafin shekarar 2026 ya fi na shekarar 2025 da kaso 19 cikin 100.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa sama da naira biliyan
এছাড়াও পড়ুন:
An rufe makarantun Filato saboda matsalar tsaro
Hukumar Ilimi ta Matakin Farko ta Jihar Filato (PSUBEB) ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun firamare da sakandire na gwamnati a faɗin jihar sakamakon fargabar tsaro da ta taso a kwanakin nan.
A sanarwar da hukumar ta fitar, ta ce za a rufe ƙananan makarantun sakandare tun daga Asabar, 22 ga Nuwamba, 2025, yayin da makarantun firamare za a rufe su daga Litinin, 24 ga Nuwamba, 2025.
H-JRBDA ta yi alƙawarin magance ambaliyar ruwa a Jigawa Gwamnatin Yobe ta ba da umarnin rufe makarantun kwana a jiharWannan mataki na zuwa ne bayan sace ɗalibai a wasu makarantu da ke jihohin Kebbi da Neja a ‘yan kwanakin da suka gabata, abin da ya tayar da hankalin iyaye da hukumomi.
PSUBEB ta sanar da cewa rufe makarantun mataki ne na wucin-gadi domin daƙile duk wata barazana da ka iya tasowa, tare da tabbatar wa jama’a cewa gwamnati na ɗaukar lafiya da tsaron ɗalibai da muhimmanci.
Hukumar ta buƙaci Hukumomin Ilimi na Kananan Hukumomi, shugabannin makarantu da shugabannin al’umma da su ba da cikakken haɗin kai wajen aiwatar da umarnin, tare da zama masu kula da duk wata alama ta rashin tsaro a yankunansu.