Aminiya:
2025-11-27@20:59:05 GMT

Wata mata ta kashe ’yar shekara 7 a Ribas

Published: 27th, November 2025 GMT

Ana fargabar cewa wata mata mai suna Success ta kashe wata yarinya mai shekaru bakwai, Alicia Olajumoke, a unguwar Rumueme da ke birnin Fatakwal na Jihar Ribas.

Mazauna yankin sun shaida wa Aminiya cewa matar da ake zargin tana da kusanci da dangin mahaifiyar yarinyar, wacce ita kaɗai ce a wurin iyayenta.

El-Rufai ya koma jami’yyar haɗaka ta ADC An janye ’yan sanda 11,566 daga gadin manyan mutane a faɗin Nijeriya

Bayanai sun ce ita ma matar ta caka wa kanta wuƙa a wuya bayan kashe yarinyar, kuma bayan an garzaya da duk su biyun asibiti, likitoci suka tabbatar da cewa sun riga mu gidan gaskiya.

Lamarin wanda ya faru a ranar Talata ya ɗimauta mazauna yankin, la’akari da zargin cewa matar ta kashe yarinyar ce a gidanta bayan ta je har makarantarsu ta ɗauko ta ba tare da izinin mahaifiyarta ba.

Jami’ar hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Jihar Ribas, SP Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis, inda ta ce an kai gawar yarinyar ɗakin ajiye gawa domin bai wa likitoci damar kammala bincikensu na kimiyya gabanin soma nasu binciken.

“Mun ziyarci wurin da abin ya faru, mun ɗauki hotuna, kuma an garzaya da su asibiti inda aka tabbatar da mutuwarsu.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Jihar Ribas yarinya

এছাড়াও পড়ুন:

Jami’an tsaro sun ƙaddamar da shirin murƙushe ’yan bindiga a Kaduna

Jami’an tsaro a Jihar Kaduna, sun fara gudanar da babban samame domin kawar da ’yan ta’adda da ’yan bindiga a wasu ƙananan hukumomin jihar.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya fitar, ya ce an gudanar da aikin tare haɗin gwiwar sojoji, DSS, NSCDC, KADVS, da kuma ƙungiyoyin sa-kai da mafarauta.

Tukur Mamu ya karbi N50m daga kuɗin fansar harin jirgin kasan Kaduna – DSS Zulum ya ba kowanne ɗalibin Borno da ke karatu a Indiya tallafin N500,000

Aikin ya shafi ƙananan hukumomin Makarfi, Hunkuyi da Ikara.

Rundunar ta ce manufar wannan samame shi ne “share dukkanin maɓoyar miyagu, rushe sansanonin da suka kafa, da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.”

Wannan mataki ya biyo bayan umarnin Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, wanda ya umarci dukkanin rundunonin ’yan sanda a faɗin ƙasar nan su ƙara ƙaimi wajen yaƙi da aikata laifuka.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Rabiu Muhammad, ya tabbatar wa jama’a cewa jami’an tsaro za su ci gaba da matsa wa miyagu lamba.

Ya ce za su ci gaba da yin gwiwa da rundunonin tsaro domin tabbatar da tsaro a jihar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnati Za Ta Biya Wasu Kudaden Ariyas Ga Masu Fensho Wannan Wata
  • An rantsar da sabon shugaban kasa a Guinea-Bissau bayan juyin mulkin sojoji
  • Majalisar Wakilai ta nemi gwamnati ta gaggauta dauko Jonathan daga Guinea Bissau
  • Jihar Jigawa Za Ta Rufe Karbar Kudaden Aikin Hajjin 2026 Ranar 24 Ga Watan Disamba
  • Ma’aikatar Harkokin Wajen Falasdinu Ta Sanar Cewa Akalla Yan Mata 33000 Ne Isra’ila Ta Kashe A Gaza
  • Jami’an tsaro sun ƙaddamar da shirin murƙushe ’yan bindiga a Kaduna
  • ’Yan bindiga sun sake kai hari a Kwara, sun sace mutum 11
  • An ceto ’yan mata 24 d aka yi garkuwa da su a makaranta a Kebbi
  • Amarya ta yi wa angonta yankan rago bayan kwana 3 da aurensu a Katsina