Gwamna Bago Ya Kaddamar da Katafaren Kamfanin sarrafa Man Kade A Afirka.
Published: 11th, August 2025 GMT
Gwamna Mohammed Umar Bago na jihar Neja, ya kaddamar da aikin sarrafa man kade tan dubu talatin a karamar hukumar Mokwa ta jihar tare da alkawarin samar da muhallin kasuwanci don bunkasa.
Wani wuri mai daraja na duniya, wanda Salid Agriculture Nigeria Ltd ya gina kuma bankin NEXIM PLC zai samar da shi zai kawo sauyi ga tattalin arzikin matan karkara, kananan manoma, da kuma tattalin arzikin jihar Neja.
Gwamna Mohammed Umar Bago ya samu rakiyar Dr. Aliyu Sabi Abdullahi, Ministan Noma, Abba Bello, MD/Shugaban Bankin NEXIM, Alhaji Ali Sa’idu, MD/Shugaba na Salid Agriculture Nigeria Ltd da tsohon Gwamnan Bayelsa da kuma fitattun iyayen gidan sarauta da suka hada da mai martaba Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar da dai sauransu.
A nasa jawabin, gwamnan ya nuna matukar godiya ga bankin NEXIM, Salid Agriculture Nigeria Ltd, da ma’aikatar kasuwanci da zuba jari ta jihar Neja bisa hadin kan da suka yi wajen ganin an samar da aikin, sannan ya bukaci al’ummar Kusopa da su ci gaba da bin doka da oda, tare da daukar kamfanin a matsayin abokin tarayya mai kima wajen ci gaban al’umma.
Da yake jawabi a madadin kungiyar noma ta Salid, MD/Shugaba Alhaji Ali Sa’idu ya godewa Gwamna Bago bisa samar da filaye, da samar da yanayin kasuwanci da kuma soke haraji na tsawon shekaru uku.
ALIYU LAWAL.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Zulum ya ba kowanne ɗalibin Borno da ke karatu a Indiya tallafin N500,000
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a ranar Litinin ya ziyarci ɗaliban jihar da ke karatu a ƙasar Indiya, inda ya ba kowannen su tallafin Naira 500,000.
Gwamnan, wanda ke ziyarar aiki a Indiya, ya fara ganawa da waɗanda suka ci gajiyar shirin tallafin karatu na jihar a Jami’ar Sharda da ke Noida.
Ko sisi ba a biya ’yan bindiga ba kafin su saki ɗaliban da suka sace – Gwamnan Kebbi Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Oyo saboda aikata kisan kaiYa tabbatar musu da jajircewar gwamnatinsa wajen kula da walwalarsu domin samun nasarar karatunsu, sannan ya gargade su da su mai da hankali kan karatun nasu.
Ya ce, “Na zo nan yau saboda dalili ɗaya, don tunatar da ku cewa gwamnatin Jihar Borno na alfahari da ku, wadda kan haka take saka hannun jari a kan makomarku.
“Kuna da muhimmanci ga ci gaba da sake gina jiharmu. Ilimin da ƙwarewar da kuke samu a nan zai amfani, ga jama’arku da kuma kannenku masu zuwa,” in ji Zulum.
Gwamna Zulum ya bayar da tallafin kuɗi na Naira 500,000 ga kowane ɗalibi, abin da ya jawo farin ciki matuƙa ga ɗaliban.
Daga nan, gwamnan ya tafi zuwa yankin Lucknow a ƙasar Indiya, inda ya yi irin wannan taimako ga ɗaliban Jihar Borno a Jami’ar Integral.
Ya kuma ba da umarni a bai wa waɗanda suka ci gajiyar tallafin karatu na Jihar Borno da ke karatu a ƙasar Malesiya irin wannan tallafin kuɗi, yana mai jaddada alkawarin yin adalci ga dukkan ɗaliban da ke amfana da shirin tallafin karatu.
Ɗaliban sun yaba wa gwamnan saboda ziyarar, inda bayyana shi a matsayin shugaba mai tausayi da kulawa.
A cikin tawagar gwamnan akwai Babban Sakataren Fadar Gwamnatin Borno, Barista Mustapha Busuguma da Babban Sakataren Hukumar BOGIS, Injiniya Adam Bukar Bababe.