HausaTv:
2025-07-24@03:41:12 GMT

MDD : Gaza na cikin bala’i mafi muni tun soma yaki a Zirin a Oktoban 2023

Published: 1st, June 2025 GMT

Wani rahoto da ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar, ya nuna cewa Gaza na fuskantar bala’i mafi muni tun soma yaki a Zirin a watan Oktoban 2023.

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan hakkin bil adama a yankunan Falasdinawa da aka mamaye ya zargi gwamnatin Isra’ila da yin amfani da batun agajin jin kai da gangan domin ci gaba da aiwatar da munanan laifukan da take aikatawa a Gaza.

Francesca Albanese a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce: “Dukkan wadannan matakan an boye su ne a karkashin sunan agaji don karkatar da hankulan kasashen duniya.”

A wani labarin kuma Kakakin Majalisar Dinkin Duniya Stéphane Dujarric ya shaida wa manema labarai a ranar Juma’a da ta gabata cewa: Bukatun jin kai a Gaza ya karu sosai bayan kusan kwanaki 80 na hana shigar da tallafi a zirin.

‘’tallafin da ake samu a yanzu haka bai wadatar ba wajen biyan bukatun mutane sama da miliyan 2.1 da ke bukatar agajin gaggawa. » inji shi.

Adadin wadanda sukayi shahada a wannan yanki na Falasdinu tun daga ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023 ya kai mutane 54,381, a cewar ma’aikatar lafiya ta Gaza.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

 Netanyahu: Ba Za Mu Daina Yakin Gaza Ba

Fira ministan HKI wanda kotun duniya ta manyan laifuka take nem ruwa a jallo ya bayyana cewa; Babu yadda za su tsayar da yakin Gaza, matukar kungiyar Hamas ba ta mika wuya baki day aba.

Benjemine Netanyahu ya kuma ce; A lokacin da Hamas za ta mika makamanta ne, shi ne za mu yi tunanin ko za mu bude mata hanyar ficewa daga Gaza, da kuma dakatar da yaki.

A gefe daya tashar talabijin din CNN ta ambato wata majiya ta gwamnatin Amurka tana cewa; Amurka ta gargadi kungiyar Hamas akan cewa, hakurinta ya kusa karewa akan batun tsagaita wuta, tare da neman kungiyar ta gwagwarmaya ta bayar da jawabi a cikin gaggawa kafin makwanni biyu masu zuwa.

Tashar talabijin din CNN din ta kuma bayyana cewa;  Amurkan ta bai wa Hamas lamunin cewa Isra’ila ba za ta shiga cikin tattaunawar kawo karshen yaki ba a tsawon lokacin dakatar da yaki da zai dauki kwanaki 60.

Sai dai kuma majiyar ta fada wa tashar talabijin din CNN cewa, Amurkan za ya janye wannan lamunin idan har kungiyar ta Hamas ba bayar da jawabi a cikin sauri ba.

 Sai dai kuma masu bin diddigin abubuwan da suke faruwa sun bayyana cewa; HKI ce ummul-haba’isin tsaikon da ake samu a tsagaita wutar yakin ba kungiyar gwgawarmaya ta Hamas ba.

A nata gefen kungiyar Hamas ta ce, a mataki na baidaya kungiyar tana son ganin an tsagaita wuta, duk da cewa jagorancin kungiyar na Gaza ne zai yanke hukunci na karshe.Khalilul Hayya wanda ya bayyana hakan ya kara da cewa; Jagororin Hamas na cikin gida ne ke da alhakin aiwatar da duk wani mataki na tsagaita wuta, don haka su ne za su bayyana mataki na karshe.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dalilin da muka gaza biyan ma’aikata mafi ƙarancin albashi — Gwamnatin Borno
  •  Fiye Da  Kungiyoyin 100 A Duniya Sun Yi Gargadi Akan Halin Yunwa Da HKi Ta Jefa Mutanen Gaza A Ciki
  • A Kalla Falasdinawa 10 Yunwa Ta Kashe A Gaza A Cikin Sa’o’i 24
  • Yahudawan Sahayoniyya Sun Bullo Da Dabarar Kisa Kan Falasdinawa Musamman ‘Yan Gudun Hijira
  • Sheikh Qasem: Nuna Halin Ko In-Kula Na Duniya Ne Ya Jawo Kisan Kiyashi A Gaza
  •  Netanyahu: Ba Za Mu Daina Yakin Gaza Ba
  • Jami’an tsaro sun dakile yunkurin Sanata Natasha na shiga harabar Majalisa
  • Tsoffin Jami’an ‘Yan Sanda Sun Bukaci A fitar Da Su Daga Cikin Shirin Fansho
  • Mataimakiyar Shugaban Majalisar Dinkin Duniya Ta Jinjinawa Gwamnan Kano Bisa Ayyukan Cigaban Jihar
  • Jami’in Shari’ar Kasa Da Kasa Ya Bayyana Cewa: Harin Da Aka kai Kan Iran Babban Laifi Ne