Aminiya:
2025-09-18@05:40:53 GMT

Babu ’yan adawan da za su iya hana Tinubu lashe zaɓen 2027 — Ganduje

Published: 21st, March 2025 GMT

Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa babu wata gamayyar ’yan adawa da za ta iya hana Shugaba Bola Ahmed Tinubu lashe wa’adi na biyu a zaɓen 2027.

Ya yi wannan jawabi ne domin mayar da martani ga sabuwar haɗakar ’yan adawa da Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, da wasu shugabanni suka kafa.

NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Wasu Teloli Cika Alƙawari Majalisar wakilai ta amince da dokar ta-ɓaci a Ribas

A yayin taron manema labarai da Atiku ya gudanar a Abuja a ranar Alhamis, ya soki yadda Tinubu ke tafiyar da mulki, musamman batun ayyana dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas.

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da Tsohon Gwamnan Jihar Imo, Emeka Ihedioha, da wasu ’yan siyasa sun hallara, inda suka bayyana shirin haɗa kai domin karɓe mulki daga hannun Tinubu a 2027.

Sai dai Ganduje ya yi watsi da wannan yunƙuri, inda ya bayyana cewa tafiyar ba za ta yi tasiri ba.

“Babu wata yarjejeniya ko haɗa kai da za ta hana ’yan Najeriya sake zaɓen Tinubu a 2027,” in ji shi a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan wayar da kan jama’a, Cif Oliver Okpala, ya fitar.

Ya ce irin nasarorin da Tinubu ya samu tun bayan hawansa mulki ne zai tabbatar da nasararsa.

“Tabbas Tinubu zai sake lashe zaɓe saboda irin ci gaban da ya kawo tun bayan da ya zama shugaban ƙasa,” in ji Ganduje.

Haka kuma, ya ce wannan sabuwar haɗakar ’yan adawa ba za ta yi tasiri ba, domin ’yan siyasar da ke ciki na da manufofi daban-daban.

“Ku manta da waɗannan tarukan na ‘yan siyasa da maganganunsu marasa tushe, domin yawancinsu ba su da wata makoma ta siyasa,” in ji shi.

“Haɗin gwiwarsu – kama daga kan jam’iyyar LP zuwa PDP da SDP – na ƙunshe da mutanen da ke da ra’ayoyi daban-daban da kuma son zuciya. Ba za su taɓa iya cimma muradi na siyasa ba.”

Wannan martani na Ganduje na nuni da cewa zaɓen 2027 zai kasance mai ɗaukar hankali tare da fafatawa mai zafi tsakanin ɓangarorin siyasa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Adawa adawa Dokar Ta Ɓaci Zaɓen 2027

এছাড়াও পড়ুন:

Wata Ta Kashe ’Yar Uwarta Kan Bashin Naira 800 A Ondo

An garzaya da ita asibiti, amma daga baya likitoci suka tabbatar da mutuwarta.

’Yansanda sun kama Bosede kuma suna bincike a kan lamarin.

Kakakin rundunar, DSP Olusola Ayanlade, ya ce za su tabbatar da adalci.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Kano Ta Inganta Cibiyoyin Horas Da Sana’o’i Domin Dakile Aikata Laifuka Tsakanin Matasa
  • Tinubu bai shirya gudanar da sahihin zaɓe ba a 2027 – Buba Galadima
  • Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo
  • Tinubu Ya Taya Amusan Da Gumel Murnar Samun Nasarori A Ɓangarori Daban-daban
  • Wata Ta Kashe ’Yar Uwarta Kan Bashin Naira 800 A Ondo
  • Gwamnatin Neja Ta Musanta Rahoton Hana Da’awa A Jihar
  • Peter Obi ya kai wa Obasanjo ziyara
  • An kama tsohon minista kan zargin kisan kai domin tsafi a Nijar
  • Arewa Ba Zata Ƙarɓi Mulki A 2027 Ba, Gwamna  Bago
  • Gwamnatin Sudan Ta Ce: Babu Sulhu Da ‘Yan Tawayen Kasar Na Kungiyar Rapid Support Forces