Gwamnati Ta Jaddada ƙudirin Kare ‘Yancin Faɗin Albarkacin Baki Da ‘Yancin ‘Yan Jarida
Published: 21st, March 2025 GMT
Ya ce: “Ina so in sake nanata cewa Shugaban Ƙasa Tinubu, wanda yake cikakken ɗan dimokiraɗiyya, yana da niyyar kare ‘yancin ‘yan Nijeriya kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada. Haka zalika, yana ƙarfafa sukar gwamnati mai ma’ana da adawa tagari saboda suna da muhimmiyar rawa da suke takawa wajen ingantawa da zurfafa tsarin dimokiraɗiyyar mu.
“Ina kuma tabbatar da cewa wannan gwamnati za ta ci gaba da kare ‘yancin ‘yan jarida da samar da yanayi mai kyau ga aikin jarida a Nijeriya. Gwamnatin nan tana da yaƙinin cewa ‘yancin ‘yan jarida yana da muhimmanci wajen inganta nagartar shugabanci, gaskiya, da ci gaban ƙasa.”
Ministan ya yi amfani da damar taron don taya Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ) murnar cika shekaru 70, yana mai bayyana wannan lokaci a matsayin wata babbar alama ta jajircewar su wajen kare ‘yancin ‘yan jarida da inganta aikin jarida.
Ya ce: “Ina kuma so in gode wa kafafen yaɗa labarai saboda jajircewar su wajen yaɗa muhimman batutuwan gwamnati. Wannan taro yana gudana a cikin wani lokaci mai muhimmanci, yayin da Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ) take bikin cika shekaru 70. Wannan babbar alama ce da ke nuna yadda NUJ ke ci gaba da jajircewa kan ‘yancin ‘yan jarida da ingancin aikin jarida.”
Idris ya bayyana cewa Zauren Taron Bayani na Ministoci da ma’aikatar sa take jagoranta yana da manufar bai wa ‘yan Nijeriya damar samun cikakken bayani kan manufofi da shirye-shiryen gwamnati, tare da jaddada ƙudirin gwamnati na nuna gaskiya da ɗaukar alhakin ayyukan ta.
“Wannan taro wata babbar dama ce ga ministoci su sanar da ‘yan Nijeriya irin cigaban da aka samu a ma’aikatun su. Ta wannan zauren tattaunawar, wanda aka inganta ta hanyar fasahohin zamani, muna tabbatar da ƙudirin mu na bayyana gaskiya da bayar da bayanai kai-tsaye dangane da manufofi, shirye-shirye, da sauye-sauyen da ke faruwa a ma’aikatun gwamnati.”
Ministan ya yaba wa Ministan Harkokin Wajen Nijeriya, Ambasada Yusuf Tuggar, bisa ƙoƙarin sa na inganta martabar Nijeriya a idon duniya ta hanyar manufofin diflomasiyya da tsare-tsaren hulɗa da ƙasashen ƙetare.
Haka nan, ya jinjina wa Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, saboda irin sauye-sauyen da yake aiwatarwa domin daidaita ma’aikatar daidai da Ajandar Sabunta Fata ta Shugaba Tinubu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Tinubu bai shirya gudanar da sahihin zaɓe ba a 2027 – Buba Galadima
Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya yi zargin cewa gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ba ta da niyyar gudanar da sahihi kuma ingantaccen zaɓe a 2027.
Galadima ya bayyana hakan ne ranar Talata a wata hira da aka yi da shi a shirin Prime Time na gidan talabijin na Arise TV, inda ya ce gwamnatin da jam’iyyar APC ke jagoranta ta kankane cibiyoyin gwamnati don amfaninta.
Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu Kano Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo“Wannan gwamnati ba ta shirya gudanar da zaɓen adalci ba. Daga yadda suke tafiyar da al’amura, za ka gane yadda suke tarwatsa jam’iyyun siyasa. Wannan yana nuna cewa ba sa son a samu hamayya a lokacin zaɓe,” in ji shi.
Galadima ya kuma yi gargadi kan shirin nada wani da ya kira mai lam’a a matsayin sabon shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), yana mai cewa hakan na iya jefa ƙasar cikin rudani.
“Ina fatan ba gaskiya ba ne, domin idan wannan mutumin ya zama shugaban INEC, ka tabbata cewa wannan gwamnati na neman tayar da yaƙin basasa,” in ji shi.
Sai dai bai ambaci sunan mutumin ba.
Dangane da batun fara yaƙin neman zaɓe da wuri da wasu jam’iyyu ke yi, Buba Galadima ya zargi INEC da gazawa wajen aiwatar da tanade-tanaden dokokin zaɓe.
“Wannan batun fara yaƙin neman zaɓe kafin INEC ta ba da izini, gwamnatin da ke kan mulki ce ta fara shi. Wannan yana nuna cewa INEC ba za ta iya zama mai adalci a irin wannan yanayin siyasa da muke ciki ba,” in ji shi.