Babban Kwamandan Sojojin Iran Ya Sanar Da Tsarin Sabunta Matakan Mayar Da Martani Kan Makiya
Published: 18th, February 2025 GMT
Babban kwamandan sojojin kasar Iran ya bayyana cewa: Sun sabunta hanyoyin da sojojin Iran zasu mayar da martani kan duk wani harin wuce gona da iri kamar yadda Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bada umarni
Babban kwamandan sojojin kasar Iran Manjo Janar Abdur-Rahim Mousawi ya bayyana cewa: Tun tsawon kwanaki da suka gabata jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana cewa: Idan Amurka ta farma tsaron al’ummar Iran, to lallai Iran za ta kai farmaki kan tsaronta ba tare da wata shakka ba, wannan ya kasance umarni ne bayyananne ga dakarun Iran, kuma kwamandojin sun sabunta shirinsu na aiwatar da wannan umarni, kuma a halin yanzu Iran a shirye take tsaf don gudanar da umarni a aikace.
Manjo Janar Mousawi ya kara da cewa: Sun sha wahalhalu da dama, kuma makiyansu sun yi kokari da dukkan karfinsu a cikin shekaru 46 da suka gabata don dakile juyin juya halin Musulunci da ruguza shi da karkatar da alkiblarsa, amma wannan al’umma karkashin jagorancin Jagoran juyin juya halin Musulunci da jinin shahidan ta, ta ci nasara kan dukkanin wadannan makirce-makircen da alfahari da nasara.
Mousawi ya jaddada cewa: Su al’umma ce da ke cewa sun nisanta daga karbar wulakanci, kuma sun yi alkawari ga Allah Madaukakin Sarki, da jagoransu da kasarsu mai albarka da kuma al’ummarsu masu zurfin hankali da basira gami da hakuri da jinin shahidan Iran 200,000, wadanda suka yi shahada, da Falasdinawa sama da 50,000, da suka yi shahada a Gaza da jinin Sayyed Hassan Nasrullahi da Sayyed Hashim Safiyyullah da Imad Mughniya da Isma’il Haniyya da Yahaya Al-Sinwar, cewa za su ci gaba da gwagwarmaya da kalubalantar mamayar mulkin mallakar Amurka har sai ta mika wuya kuma ta mutunta hakkokin al’ummomi.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: juyin juya halin
এছাড়াও পড়ুন:
Za mu ci gaba da shirye-shiryen babban taronmu — PDP
Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa za ta ci gaba da shirin gudanar da babban taronta wanda za a yi a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba a Ibadan da ke Jihar Oyo.
Tun da farko, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta hana jam’iyyar gudanar da taron, inda ta ce PDP ta karya dokokinta na cikin gida.
’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi Kotu ta dakatar da gudanar da babban taron PDPMai shari’a James Omotosho, wanda ya jagoranci shari’ar, ya umarci Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), da kada ta karɓi ko ta wallafa sakamakon taron har sai PDP ta cika dukkanin sharuɗan da doka ta tanada.
Sai dai a cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar da yammacin ranar Juma’a, kakakinta na ƙasa, Debo Ologunagba, ya ce jam’iyyar ba za ta dakatar da shirin gudanar da taron ba.
Ya bayyana hukuncin kotun a matsayin tauye haƙƙin dimokuraɗiyya a Najeriya.
Ologunagba, ya ce hukuncin ba zai hana PDP ci gaba da shirye-shiryenta na zaɓen sabbin shugabanni da za su jagoranci jam’iyyar na tsawon shekaru huɗu masu zuwa ba.
Ya yi nuni da cewa Kotun Ƙoli ta tabbatar da cewa jam’iyyu na da ’yancin tafiyar da harkokinsu na cikin gida.
“PDP na kira ga mambobinta da shugabanni a faɗin ƙasar nan da su kuma ci gaba da shirye-shiryen babban taron jam’iyyar,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa jam’iyyar mai bin doka ce, kuma ta umarci lauyoyinta da su ɗaukaka ƙara game da hukuncin kotun.