2025-09-17@21:53:39 GMT
إجمالي نتائج البحث: 6135
«yankin Sahel»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Ministan harkokin wajen kasar Malasiya Muhammad Hassan ya sake nanata bukatar a kori HKI daga MDD saboda kissan kare dangin da take yi a zirin gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar ya nakalto Muhammad Hassan yana fadar haka a yau Jumma’a ya kuma kara da cewa, kasashen masu rauni a duniya sun damu da yadda manya-,manyan kasashen duniya suka kyale HKI take yin abinda taga dama a kasar Falasdinu da ta mamaye. Kuma hakan zai sa kasashe da dama su kauravewa HKI. Labarin ya kara da cewa HKI a cikin shekaru kimani biyu da suka gabata, sun kashe falasdinawa fiye da dubu 62, amma MDD da kuma sauran kasashen yamma sun hana hatta shigar abinci a cikin zirin gaza....
Francesca Albanese, Jami’a mai tattara bayanai kan al-amuran Falasdinawa a MDD ta yi tir da gwamnatin kasar Jamus dangane da yadda jami’an tsaron kasar suke dirar mikiya kan masu goyon bayan Falasdinawa a birnin Berline. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Albanese tana fadar haka a yau Jumm’a ta kumamkara da cewa: Ina kiran mutanen Jamus kan cewa ku ne kuka samar da ikidar Nazi, a yayinda mu a kasar Italia da Spaine muka samar da akidar Fasim a nahiyar turai a baya, wana ya kai kasashen turai ga lalacewa.. Jami’ar ta bayyana haka ne bayan dirar mikiyan da jami’an tsaro na Jamus suka yi kan masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa wadanda kuma suke bukatar HKI ta...
Rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi ta kafa kwamitin bincike mai ƙarfi na ƙwararrun jami’an tsaro tare da haɗin gwiwar rundunar ‘sojan Najeriya, domin gano abin da ya jawo aka kashe wani jami’in soja da wani sifeton ’yan sanda ya yi a jihar kwanan nan. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sanda (PPRO), CSP Ahmed Mohammed Wakil ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a madadin Kwamishinan ’yan sandan, Sani-Omolori Aliyu a hedikwatar rundunar da ke Bauchi a ranar Juma’a. Na bar APC saboda Tinubu bai cika alƙawarin da ya yi ba — Marafa An kama wani mutum da laifin kashe mahaifiyarsa kan zargin maita Wakil ya ce, an ɗora wa kwamitin alhakin tattarawa da...
Haka kuma, Ma Zhaoxu ya bayyana cewa, kasar Sin tana son mutunta juna, da zaman tare cikin lumana, da kulla hadin gwiwar samun nasara ga kowane bangare tare da Amurka, bisa tabbatar da kare muradun ikon mallakar yankunan kasarta, da tsaro da kuma ci gaban kasar. Ya kara da cewa, a shirye muke mu yi aiki tare da Amurka a kan turba guda, da aiwatar da muhimman yarjejeniyoyi da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da ci gaba da sadarwa a tsakaninmu, da warware batutuwan da muka sha bamban a kai, da fadada hadin gwiwa, da kuma ci gaba da lalubo hanyar da ta dace manyan kasashen biyu su tafi tare da juna a sabon zamani. Jami’in ya...
“Ban ga dalilin da ya sa ba a raba fifikon fasaha na Brazil da Afirka ba. Mun tabbatar wa junanmu cewa mune kawai za mu iya bunkasa tattalin arzikinmu don taimakawa kasarmu,” Tinubu ya shaida. Tinubu ya kuma bai wa masu zuba hannun jari tabbacin cewa manufofin farfado da tattalin arzikin Nijeriya na haifar da sakamakon masu kyau a halin yanzu. “Sauye-sauyen da na dukufa samarwa tun lokacin da na hau kan mulkin Nijeriya suna matukar tasiri. Da farko sun yi tsanani, amma a halin yanzu ana ganin gayar sakamakon masu kyau,” ya tabbatar. Shi kuma a bangarensa, shugaba Lula na Brazil ya nuna farin cikinsa ne da sake sabunta kyakkyawar alaka tsakanin Nijeriya da Brazil. Ya ce, a halin...
Kasar Sin ta gabatar da ‘yancin samun ci gaba a matsayin hakkin dan Adam mafi muhimmanci. Ta hanyar dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka (FOCAC), ta zuba jari mai yawa a fannin samar da ababen more rayuwa, da cinikayya, da fasahohi a fadin nahiyar Afirka. Ayyuka irin su hanyar dogo na Addis Ababa zuwa Djibouti, manyan tituna, tashoshin ruwa da wutar lantarki, gadojin kan hanyar ruwa da masana’antu, duk wadannan an tanade su ne don su zama hanyar rage talauci da tallafawa al’umma. Ta hanyar inganta yanayin rayuwa da samar da damarmakin tattalin arziki, kasar Sin ta yi nuni da cewa, tana kara karfafa martabar jama’ar Afirka ta hanyar samar musu da ci gaba. ’Yancin Cin Gashin...
Sanata Kabiru Garba Marafa tsohon ɗan Majalisar Dattawa da ya wakilci yankin Zamfara ta tsakiya jigo a Jam’iyar APC a jihar ya fice daga jam’iyar. Sanata Marafa ya bayyana ficewarsa a wani faifan bidiyo da aka wallafa a shafin Facebook a ranar Jumu’a ya ce bayan tattaunawa da magoya bayansa sun cimma matsayar barin Jam’iyyar APC kan ta zalunce su. An kama wani mutum da laifin kashe mahaifiyarsa kan zargin maita Ƙara Kuɗin Fasfo: Gwamnati na jefa ’yan Najeriya cikin matsi — Obi “Bayan mun yi waiwaye a shekara biyu da rabi da suka gabata mun gano cewa, APC a matakin ƙasa da jiha ta zalunce mu, a matakin jiha lalacewar jam’iyar ya kai matuƙa tun bayan kafa kwamitin riƙon...
Osuman ya koka kan yadda a kowace rana ake kashe rayukan mutane a yankin, ya kara da cewa, yara, mata, maza, tsofaffi duk sun fada cikin matsalolin ambaliyar ruwa, ta’addancin ‘yan bindiga dadi, ayyukan ‘yan ta’adda da sauran annobobi. Ya bukaci shugabannin arewa da mazauna yankin da su farka, su hada kawunansu kana su dukufa da yin addu’o’in neman zaman lafiya a yankin. Da yake magana da kafar BBC bayan taron, mai ba da shawara ga ACF, Bashir Hayatu Gentile, ya ce, kungiyar ta yi nazari da bitar matsalolin da suke addabar arewa tare da cimma matsayar cewa akwai bukatar daukan matakan gaggawa. “Matsalolin nan ga su nan a zahirance, kuma dole ne a tursasa gwamnati ta...
Shehu, a cikin littafin nasa wanda ya bai wa wakilinmu na LEADERSHIP, ya yi zargin cewa; Obasanjo ya bijiro wa Buhari da wasu bukatu a lokacin da yana shugaban kasa (Obasanjo). Ya kara da cewa, “Akwai da dama a kusa da Buhari da ke ganin cewa; abin ban mamakin da ya faru a tsakanin Buhari da wanda ke gabansa a aikin sojan da yake mutuntawa, Shugaba Olusegun Obasanjo, shi ne sakamakon bukatar da aka ce Obasajon ya nemi a bai wa wani dan kwangila da yake so a aikin wuta ta Mambila. “A kan haka, Buhari cikin ladabi ya fada wa tsohon shugaban kasar cewa, ya bar shi ya gudanar da abin da ya kamata, ta hanyar bin...
Rundunar ’yan sandan Jihar Jigawa ta kama wani matashi ɗan shekara 25 mai suna Jibrin Ado bisa laifin kashe mahaifiyarsa kan zargin maita a unguwar Gerawa da ke jihar. Majiyar PUNCH ta ruwaito hakan ne a ranar Alhamis daga wata sanarwa ta manhajar X ta wani masani kan harkokin tsaro, Zagazola Makama. Ambaliya ta raba ƙauyukan Sakkwato 6 da sauran sassan jihar An fara gyaran layin dogon Abuja-Kaduna bayan hatsarin jirgin ƙasa A cewarsa, Ado ya aikata wannan aika-aika ne tare da wasu masu laifin a ranar Talata. Waɗanda suka haɗa da: Musa Kwalle da Dan Abba da Sule Musa da wani Arrow dukkansu daga ƙauyen Gerawa. Majiyar ta bayyana cewa, a ranar 26 ga watan Agusta da misalin ƙarfe...
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya soki Gwamnatin Tarayya kan ƙara kuɗin fasfo. Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (NIS), ta ƙara kuɗin fasfo mai shafi 32 zuwa Naira 100,000, yayin da mai shafi 64 ya koma Naira 200,000. Ambaliya ta raba ƙauyukan Sakkwato 6 da sauran sassan jihar An fara gyaran layin dogon Abuja-Kaduna bayan hatsarin jirgin ƙasa Obi, ya wallafa wani rubutu a shafinsa na X, inda ya ce wannan ƙarin ba adalci ba ne duba da halin matsin tattalin arziƙi da ake fuskanta. “Wannan gwamnati kullum na ƙara jefa mutane cikin wahala a maimakon ta sauƙaƙa musu rayuwa,” in ji shi. “An ƙara kuɗin fasfo sau uku cikin shekaru biyu...
Ambaliyar ruwar da ta biyo bayan mamakon ruwan saman da aka tafka ta raba kauyuka shida da ke karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sakkwato da saurann yankunan jihar. Kauyukkan da ambaliyar ta shafa su ne Makuwana da Dangawo da Faru da Gumbula da ’Yan Faruna da kuma Magajin Dawaki, sannan ta lalata hanyar da ta hada kananan hukumomin Goronyo da Sabon Birni. An fara gyaran layin dogon Abuja-Kaduna bayan hatsarin jirgin ƙasa Hadimin Gwamnan Kano ya maka mawallafin Daily Nigerian a kotu saboda kiransa da ‘ɓarawo’ Tuni dai Majalisar Dokokin Jihar ta yi kira ga gwamnatin jiha da ta tarayya da ke kula da harkokin ruwa da su dauki matakin da ya dace kan wadanda lamarin ya shafa. Hakan...
Duk da yawan wadanda aka gano suna dauke da cutar, jami’an kiwon lafiya sun bayyana irin ci gaban da ake samu. Daraktan kula da lafiyar al’umma a ma’aikatar lafiya ta tarayya, Dakta Godwin Ntadom, ya bayyana cewa; Nijeriya ta samu sanarwar bullar cutar tarin fuka mafi yawa a 2024, inda ta gano sama da mutum 400,000 da ke dauke da cutar, kwatankwacin kashi 79 cikin 100 na masu jinyar. Haka nan, akwai yara da dama wadanda ke dauke da cutar ta TB, amma ba a gano ba. Kazalika, yaran da aka gano suna dauke da cutar, yawansu ya karu daga 8,293 a 2018 zuwa 43,000 a 2024, in ji shi. Duk da haka, Ntadom ya bayyana cewa; tarin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Yana mai cewa: “Da yawa yanzu an manta zaurance ko ba a yi, saboda yanayin yadda zamani yake. Amma a da, musamman ma idan ka je wajen da ka ga sun iya Hausa kuma su ba Hausawa ba ne, za ka iya juya harshe ta amfani da zaurance wajen canza yaren ba tare da wanda ka ke tare da shi ya fahimci me kake faa ba.” Shi ma a nasa jawabin, Shugaban Kwalejin Share Fagen Shiga Jami’a (CAS), Dakta Sunusi Yakubu Ahmed, ya bayyana jin dadinsa matuka bisa zabar kwalejin don gudanar da wannan taron. Dakta Sunusi ya ce: “Tun lokacin da na ga an yi irin wannan taron a Jami’ar Northwest, na bukaci nima ina da burin...
Masu shirya taron sun dauki lokacin ana shirye-shiryen garin taron ta yi armashi da kuma nasara musamman saboda gayyato baki da aka yi daga makwabciyar kasar wato jamhuriyar Nijar. Kasancewar masarautar Daura na da alaka da aka al’adun gargajiya an shirya kasaitaiccen bikin wanda ya burge mahalarta taron musamman baki. Masu shirya taron sun kara da cewa dalilin da ya sa suka zabi masarautar Daura domin shirya wannan taron shine saboda kasancewar Daura tushen Hausa da al’adu hausawa. Haka kuma an shirya wani tattaki daga Katsina domin zuwa Daura karkashin hukumar raya al’adu ta jihar Katsina inda aka shafe kwana biyu ana tafiya akan dawakai zuwa garin na Daura duk a cikin shirye-shiryen bikin ranar Hausa ta...
Ba wai muna yin jayya da sanarar da ofishin Nuhu ya samu a tsakanin wadannan watanni ba ne kuma muna sane da kokarin da yake yi, na ganin cewa, ‘yan Nijeriya na samu su kwanta su yi barcin dare, idanuwansu biyu a rufe ba tare da wata fargabar ko za a kai masu hari ba. Tabbas, muna jinjina masa kan yunkurin da yake ci gaba da yi na rage kalubalen rashin tsaro da Gwamnatin mai ci ta gada. Amma mummunan harin da wasu mahara suka kai a watannin baya a yankin Yelwata, inda suka yi wa wasu al’umomin yankin kisan kiyashi da kuma harin da ‘yan bindiga suka kai kan Masallaci a garin Malumfashi ta Jihar Katsina, ba...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A ’yan watanni da suka gabata, matasa da yawa a Najeriya sun dukufa don ganin hakar su ta cimma ruwa wajen samun kudaden kirifto. Amma alamu na cewa a baya-bayan nan wasu daga cikinsu sun sare sun kuma saduda sun dawo daga rakiyar harkar. NAJERIYA A YAU: Matakan da ciwon suga ke bi kafin illata mai fama da shi DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan dalilan wasu matasan na yin watsi da harkar kirifto. Domin sauke shirin, latsa nan
Har ila yau, hukumar jiragen kasa ta Najeriya (NRC) ta bayyana cewa; an fara bincike kan hatsarin da jirgin kasan daga Abuja zuwa Kaduna ya yi a garin Asham da ke Jihar Kaduna. Hukumar ta ce, binciken zai gudana ne karkashin kulawar hukumomin da abin ya shafa tare da sa ido daga ma’aikatar sufuri ta tarayya, domin kokarin gano musabbabin faruwar al’amarin. A cikin sanarwar da NRC ta fitar a yammacin ranar Talata, ta bayyana cewa; jimillar mutum 618 ne suke cikin jirgin a lokacin da ya sauka daga kan hanyarsa. Kazalika, hukumar ta bayyana cewa; daga cikin fasinjojin, mutum akalla 14 ne suka samu raunuka daban-daban, sannan kuma an garzaya da su asibiti. Sauran fasinjojin kuma,...
Daraktan Tsara Tafiye-tafiye na Gwamnan Kano, Abdullahi Ibrahim Rogo, ya maka jaridar Daily Nigerian da mawallafinta, Jaafar Jaafar a gaban kotu, bisa zargin ɓata masa suna ta hanyar kiransa da ɓarawo. A kwanakin baya ne dai jaridar ta zargi Daraktan da karkatar da kudade har sama da Naira biliyan shida da rabi zuwa asusunshi, kodayake daga bisani Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya wanke shi daga zargi, inda ya ce ba satar kudaden aka yi ba, na aiki ne. Magauta sun sa NNPCL a gaba – Ojulari Babu ƙawancen da NNPP ta ƙulla da wata jam’iyyar — Kwankwaso To sai dai jaridar ta sake yin labari mai taken “Gwamnan Kano ya kare hadiminsa barawo, ya ce gwamnatin Ganduje ma ta...
Harshen Hausa shine kan gaba a yawan masu magana a Afrika ta Yamma ta yadda yake da karbuwa a Nijeriya, Nijar, Ghana, Kamaru, Benin, Gabon, Togo, Afrika ta Tsakiya, Sudan da Saudiyya da sauran su. Hasalima kowace nahiya ta duniya akwai jami’ar da ake koyar da harshen Hausa da Hausanci. Bunkasar Harshen Hausa ya sa harshen ke barazanar batar da kananam harsuna wadanda tuni wasu da dama a yau suka bace ba amo ba labarin su a bisa ga yadda yake mamaye harsuna a mabambantan kasashe. Sai dai duk da kima da martabar da Harshen Hausa yake da shi da yadda daruruwan miliyoyin al’umma ke magana da Harshen har yau Jamhuriyar Nijar kadai ce kasar da ke amfani da Hausa...
Shugaban Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL), Bashir Bayo Ojulari ya ce mutanen da ba sa nufin Najeriya da alheri sun sa kamfanin a gaba saboda sabbin tsare-tsaren da yake kawowa na inganta fannin man fetur a kasar. Ya bayyana hakan hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin Manyan Ma’aikatan Bangare Man Fetur da Iskar Gas na Kasa (PENGASSAN) a hedkwatar kwamfanin da ke Abuja. Babu ƙawancen da NNPP ta ƙulla da wata jam’iyyar — Kwankwaso Dangote ya ƙulla yarjejeniyar gina kamfanin takin zamani na dala biliyan 2.5 a Habasha Ojulari ya ce duk da yake sun san za su iya fuskantar kalubalen, amma ba za su taba bayar da kai bori ya hau ba a yunkurinsu na inganta rayuwar...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Matakin da gungun kasashen Turai ke son dauka kan Iran yana dagula tsarin diflomasiyya Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya yi la’akari da yadda kasashen Turai uku suka yi amfani da tsarin warware takaddamar da ba bisa ka’ida ba a karkashin tsarin hadin gwiwa na (JCPOA) da kuduri mai lamba 2231 a matsayin doka, yana mai cewa wannan matakin yana dagula tsarin diflomasiyya. A daidai lokacin da kasashen Turai uku ke son amfani da tsarin warware takaddamar da ba bisa ka’ida ba a kan ka’ida ta JCPOA da kuduri mai lamba 2231, a yammacin ranar Alhamis, Kaya Kalas, babban wakilin kungiyar EU mai kula da harkokin waje da kuma mai kula...
Yanzu haka a nan kasar Sin ana ta shirye-shiryen gudanar da babban bikin cika shekaru 80 da cimma nasarar yaki da mamayar sojojin Japan, da nasarar yakin kin tafarkin murdiya, wanda shi ma wani lokaci ne da zai dada tabbatarwa duniya zahirin abubuwan da suka wakana, tare da karyata sassan dake kokarin lullube gaskiya, da kaucewa daukar alhakin ta’asar da aka aikawa al’ummar Sin a yayin mamayar birnin Nanjing. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp ShareTweetSendShare Previous Post Manyan Jami’ai A Ma’aikatar Tsaro Ta...
An kafa ta a cikin 1955 kuma tana da hedikwata a Tokyo, IAPH kungiya ce ta duniya mai dauke da tashoshin jiragen ruwa fiye da 190, kuma tana gudanar da kasuwanci a cikin ƙasashe 89. Mambobin kungiyar IAPH suna kula da sama da kashi 60 cikin 100 na cinikin teku da kwantena na duniya. Kungiyar tana taka muhimmiyar rawa wajen tsara manufofin tekun duniya, tare da yin aiki kafada da kafada da Hukumar Kula da Teku ta Duniya, Hukumar Kwastam ta Duniya, da tsarin Majalisar Dinkin Duniya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake...
Ƙasar Habasha ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da wani reshe na Rukunin Kamfanonin Dangote na Nijeriya domin gina wata sabuwar masana’antar samar da takin zamani ta kimanin dala biliyan 2.5. Hakan na ƙunshe cikin wani saƙo da Firayim Ministan Habasha, Abiy Ahmed ya wallafa a shafin X ranar Alhamis. Sanusi Mikail Sami ya zama sabon Sarkin Zuru Babu ƙawancen da NNPP ta ƙulla da wata jam’iyyar — Kwankwaso Abiy ya ce wannan yarjejeniya da Dangote Group na attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote, za ta sanya ƙasarsa cikin jerin manyan ƙasashen da ke samar da takin zamani a duniya. Ya bayyana cewa wannan aikin gina masana’antar wanda za a fara nan ba da jimawa ba, za ta riƙa samar...
A yau Alhamis aka bude bikin nune-nune na masana’antar manyan bayanai ta Big Data, a birnin Guiyang na lardin Guizhou dake kudu maso yammacin kasar Sin. Taken bikin na bana shi ne “Karfafa masana’antu ta hanyar bayanai, ingiza ci gaba ta hanyar basira” wanda ya kunshi rumfuna 6 da suka hada da na amfani da kirkirarriyar basira wajen yanke shawara da kayayyakin more rayuwa da hidimomi da manhajoji da bude ido da kirkire-kirkire, dukkansu masu amfani da fasahohi na zamani, wanda ya hada kamfanoni 375 na cikin gida da ketare. Yayin da Sin ke tsaka da zurfafa aiwatar da shirin “AI Plus” mai ingiza amfani da fasahar AI a bangarori daban-daban, taron ya nuna sabbin nasarorin da aka samu wajen...
Ƙasar Habasha ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da wani reshe na Rukunin Kamfanonin Dangote na Nijeriya domin gina wata sabuwar masana’antar samar da takin zamani na kimanin dala biliyan 2.5. Hakan na ƙunshe cikin wani saƙo da Firayim Ministan Habasha, Abiy Ahmed ya wallafa a shafin X ranar Alhamis. Sanusi Mikail Sami ya zama sabon Sarkin Zuru Babu ƙawancen da NNPP ta ƙulla da wata jam’iyyar — Kwankwaso Abiy ya ce wannan yarjejeniya da Dangote Group na attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote, za ta sanya ƙasarsa cikin jerin manyan ƙasashen da ke samar da takin zamani a duniya. Ya bayyana cewa wannan aikin gina masana’antar wanda za a fara nan ba da jimawa ba, za ta riƙa samar...
Siyar da Nkunku kuma yana nufin cewa Chelsea za ta iya samun riba a kasuwar musayar yan wasa, inda ka samu kusan fam miliyan 309 wajen siyar da yan wasa yayinda ta kashe fam miliyan 277 wajen sayen yan wasa, Nkunku ya zura kwallaye 18 sannan ya taimaka aka ci biyar a wasanni 62 da ya buga wa Chelsea, bayan ya koma Landan daga RB Leipzig kan fam miliyan 52 a shekarar 2023. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Nafisa wacce ta wakilci Nijeriya a karkashin Kwalejin Tulip International ta Nijeriya, ta buge abokan karawarta fiye da 20,000 daga kasashe 69, ciki har da kasashen Turanci. Gasar ‘TeenEagle’ babbar gasa ce ta duniya wacce ke bibiyar ƙwarewar ɗalibai cikin harshen Turanci, kaifin basira, da ƙwarewa a salon magana. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Alhaji Sanusi Mikail Sami Gomo na III ya zama sabon Sarkin Zuru. Kwamishinan Ƙananan hukumomi da masarautu, Alhaji Abubakar Garba Dutsin-Mari ne ya sanar da hakan yau Alhamis, a fadar Sarkin Zuru wanda kuma ya miƙa masa takardar naɗin da Gwamnan Kebbi, Nasir Idris ya sanya wa hannu. Ambaliya: Manoma sun yi asarar miliyoyin Naira a Taraba ACF ta yi Allah-wadai da rushe kasuwar Alaba Rago Ya ce, naɗin sabon Sarkin ya biyo bayan miƙa sunayen sarakuna uku da masarautar Zuru ta miƙa wa Gwamnan jihar, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada. Ya ƙara da cewa, Gwamnan wajen yin amfani da ikon da aka ba shi, ya amince da Alhaji Sanusi Mikail Sami a matsayin sabon Sarkin Zuru, wanda...
Sanadiyyar ambaliyar ruwa a gonaki amfanin gona na miliyoyin Naira ne suka salwanta inda ɗaruruwan filayen noma suka shefe da ruwa a Jihar Taraba. Kodayake, ba a bayyana ko an sako ruwa daga Logdo Dam ba ne daga jamhuriyar Kamaru ba, amma kogin Benuwe da ke Taraba ya yi ta malala daga gaɓarsa wanda ya yi sanadin ambaliya da lalata ɗaruruwan filayen noma. ACF ta yi Allah-wadai da rushe kasuwar Alaba Rago Gwamnatin Gombe da Rotary sun yi shirin rage mutuwar mata da yara Daily Trust ta gano cewa ruwan ya fara ƙaruwa a kogi a ’yan kwanakin da suka gabata, kuma a yanzu kogin ya yi ta malala a gefan koguna inda ya haddasa ambaliya a faɗin jihar. Ambaliyar...
Dakta Abdullahi Idris, ya bukaci sabbin shugabannin da zage damtse wajen ganin an samu nasarar abinda suka sanya a gaba wajen samar da zaman lafiya da hadin kan ‘yan Arewa. Akan hakan, ya bukace su da su zama jakadu na gari a jihohinsu wajen kare martabar kungiyar da kuma lalubo hanyar da za’a kara samun ci gaba a yankin Arewa baki daya. A nasa jawabin, shugaban taron Alhaji Bature Umaru Masari, ya bayyana gamsuwarsa dangane da irin gudummawar kungiyar na hada kan alummar Arewa domin samun zaman lafiya. Ya kuma bukaci sabbin shugabannin kungiyar dasu tabbatar da cewa sunyi aiki ba tare da nuna kabilanci kabila ko bambamcin addini ba Wanda hakan zai taimakawa kungiyar wajen ganin ta cimma...
Kazalika, bukatu masu alaka da kayayyakin masarufi na ci gaba da farfadowa, yayin da manufar “maye tsoffin kaya da sabbi” ta haifar da matukar karuwar bukatun kayan lantarki da na’urorin bidiyo da sauti, da kuma kayan sadarwa. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
“A yau (Ranar Laraba) majalisar zartaswa ta yi la’akari da batun ƙarin kuɗin fansho ga tsofaffin ma’aikatan jiharmu da suka yi ritaya, hakan ya biyo bayan ƙarin mafi ƙarancin albashin ma’aikata da kuma mafi ƙarancin kuɗin fanshi na ƙasa da gwamnatin tarayya ta amince da su,” in ji shugaban ma’aikatan. Barista Sani ya ƙara da cewa, tun ma kafin wannan ƙarin, hatta adadin mafi ƙarancin fansho da jihar Bauchi ke biya a baya na Naira dubu 12, wasu jihohi da dama ba su ma biyan irin wannan, ga kuma sabon ƙari da suka amince dukkan domin kyautata rayuwar tsofaffin ma’aikata a faɗin jihar. Ya misalta amincewar a matsayin kyakkyawar yunƙurin gwamna Bala Muhammad na kyautata rayuwa da jin...
Gwamnatin Jihar Gombe tare da haɗin gwiwar ƙungiyar Rotary International sun ƙaddamar da shirin aikin jinya domin rage mace-macen mata da yara a faɗin jihar. Shirin da aka gudanar a Ƙananan hukumomi uku da suka haɗa: Gombe da Kaltungo da Yamaltu-Deba, inda aka yi wa jama’a gwaje-gwaje, jinya da wayar da kai a unguwannin Yelenguruza da Kagarawal. An kama Ɗan sanda kan harbe soja a Bauchi Gwamnati ta kara kudin yin fasfo zuwa N100,000 da kuma N200,000 Shugaban Rotary Reproductive, Maternal and Child Health a Nijeriya, Farfesa Emmanuel Adedolapo Lufadeju, ya bayyana cewa fiye da mutum 120 aka duba a unguwar Kagarawal kaɗai, inda aka samu kashi 70 cikin 100 sun kamu da zazzaɓin cizon sauro. Ya ce, tun daga...
Hukumar Ƴansanda a birnin Tripoli, Libya, ta kama wasu ƴan Nijeriya biyu bisa zargin hannu a wasu jerin fashin shagunan kasuwanci da ake gudanarwa a sassan birnin. Rahotanni sun bayyana cewa an cafke mutanen ne a ranar 25 ga Agusta 2025, bayan wani bidiyon na’urar tsaro ya nuna su suna satar kaya daga wani shago. An ce dukkansu ba su da takardun izinin zama a ƙasar. Zargin Shan Guba: ’Yan Nijeriya Biyu Sun Mutu A Libya Yadda Aka Cafke Masu Saka Ƙwayoyi A Jakunkunan Matafiya A Filin Jirgin Sama A Kano Ƙungiyar Migrant Rescue Watch, wadda ke sa ido kan al’amuran baƙi da ƴan gudun hijira a Libya, ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ta fitar...
Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya (NIS) ta sanar da ƙarin kuɗin yin Fasfo, wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga Satumba, 2025. A wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, ACI AS Akinlabi, ya fitar a ranar Alhamis, an bayyana cewa wannan sabon tsari zai shafi aikace-aikacen da ake yi ne kawai a cikin Nijeriya. Nijeriya Za Ta Ɗaukaka Da Fasahar Ƙere-ƙere Da Tattalin Abinci – Tinubu Gwamnan Katsina Ya Dawo Gida Domin Ziyara Ga Al’ummar Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Wa Hari A Malumfashi Sabon tsarin ya ƙayyade kuɗin fasfo na shafuka 32 mai ingancin shekaru biyar a kan N100,000, yayin da na shafuka 64 mai ingancin shekaru goma zai kasance N200,000. Sai dai an...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya ta kara farashin yin fasfo daga ranar day aga watan Satumbar 2025. A cewar wata sanarwa da Kakakin hukumar, ACI AS Akinlabi ya fitar ranar Alhamis, hukumar ta ce karin ya shafi iya wadanda suka nemi fasfo din a iya cikin Najeriya ne. Ana zargin miji da kashe matarsa da duka saboda zuwa gona a makare Kotu ta daure dan Shugaban Equatorial Guinea kan sayar da jirgin saman kasar “A yanzu duk fasfo mai shafi 32 ya koma N100,000 wanda zai yi shekara biyar kafin ya daina aiki, yayin da mai shafi 64 da zai shekara 10 ya koma N200,000,” in ji sanarwar. Sai dai sanarwar ta ce har yanzu kudaden da...
An kai shi asibiti, inda aka kula da shi sannan aka sallame shi domin halartar jana’izar iyalan nasa. Jami’in hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar Kaduna (SEMA), Bello Garba, ya ce ba su samu rahoton faruwar lamarin a hukumance ba, amma sun shirya gudanar da bincike kan lamarin. An binne mamatan bisa tanadin addinin Musulunci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Aƙalla mutum uku ne sun rasu, yayin da wani ɗan sanda ya ji rauni a wani rikicin ƙungiyoyin asiri da ya auku a kasuwar Owode Onirin da ke Jihar Legas. Rundunar ’yan sandan jihar, ta bayyana cewa tana neman Abiodun Ariori, Shugaban Kamfanin Golden Venture Limited, bisa zarginsa da hannu a rikicin. HOTUNA: Tinubu ya dawo Abuja bayan ziyarar aiki a Japan da Brazil Kotu ta daure dan Shugaban Equatorial Guinea kan sayar da jirgin saman kasar Shaidu sun ce ƙungiyoyin asirin biyu sun yi artabu da bindigogi, adduna da kwalabe. Ɗan sandan da ya ji rauni an garzaya da shi asibiti, inda yake cikin mawuyacin hali. Kakakin rundunar, CSP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin. Amma ta ce...
Dukkan mambobin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, in ban da Amurka, sun goyi bayan ayyana bullar yunwa mafi muni a yankin zirin Gaza ta hanyar rahoton kungiyar Integrated Food Security Phase Classification (IPC), wata kungiya mai samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya. Kasashe 14 da daga cikin 15 da suka amince da hakan, sun ba da tabbaci a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka yi bayan taron da suka yi a wanann Laraba, kasa da mako guda bayan da hukumar ta IPC ta fitar da wani rahoto mai tayar da hankali game da halin da ake ciki na yunwa a zirin Gaza da kewaye. Sanarwar da Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar daga baya ta zo ne a daidai...
Ya ƙara da cewa jam’iyyarsu ta ADC za ta iya fito da ‘yan takara daga kowace shiyya, duk da cewa APC da PDP sun nuna cewa daga Kudu za su fito da ɗan takara a 2027. Duk da cewa wasu na ganin tasirinsa ya ragu a Jihar Ribas saboda rikicin siyasa tsakaninsa da Nyesom Wike, Amaechi ya ce har yanzu yana da goyon baya sosai. Ya bayar da misalin yadda aka tarbe shi a Jihar a baya-bayan nan ba tare da ya biya kowa kuɗi ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
Tawagar Sudan karkashin jagorancin babban daraktan hukumar leken asiri ta kasa (NISS) Manjo Janar Ahmed Mufadal ta isa Mogadishu babban birnin kasar Somalia a wata ziyarar aiki da ta kai kasar, inda ta gana da shugaban kasar Hassan Sheikh Mohamud a fadar shugaban kasa dake Mogadishu. Jagoran tawagar ta Sudan Mufadal Sheikh Mohamud ya aike da sako daga shugaban kwamitin rikon kwarya na kasar Sudan, Laftanar Janar Abdel Fattah Al-Burhan. Sakon ya hada da jaddada aniyar Khartoum na karfafa hadin gwiwa da Somaliya, musamman a fannin tsaro da leken asiri. Taron ya samu halartar babban daraktan hukumar leken asiri ta kasar Somalia (NISS), Mahad Mohamed Salad, wanda ya tattauna da Mufadal hanyoyin inganta hadin gwiwa domin tunkarar kalubalen da yankin...
Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame ya musanta rahotannin da ake na cewa sojojin kasarsa suna da hannu wajen ‘kashe-kashe’ a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo. Kagame, yayin da yake magana da jami’an soji da ‘yan sanda a wata cibiyar horaswa da ke gabashin Rwanda, ya ce, ‘yan tawayen FDLR, da mayakan gwamnatin Congo, da Azalendo, da kuma sojojin Congo ne suke aikata ta’asa a gabashin Kasar. Kagame ya ba da misali da Mozambique, da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, da Sudan ta Kudu, inda dakarun Rwanda ke jibge, ya kuma jaddada cewa “Rwanda ba ta yaki da wasu kasashe, sai dai tana goyon bayan wadannan kasashe bisa bukatarsu, wadanda ke fuskantar kalubalen tsaro.” Ya kara da cewa, “Ba za mu fara yaki...
Shugaban Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU), Farfesa Chris Piwuna, ya ce Gwamnatin Tarayya ba ta aiwatar da ɗaya daga cikin yarjejeniyar da ta ƙulla da ƙungiyar ba. Farfesa Piwuna, ya ce ASUU a koyaushe na zaɓar tattaunawa da jami’an gwamnati a matsayin mafita. Amma duk da cewa sun cimma matsaya kan batutuwa masu muhimmanci kamar kuɗaɗen gudanarwa, albashi, ’yancin malamai, ‘yancin jami’o’i, da sake duba wasu dokoki, ba a ɗauki mataki kan kowanne ba. “Babu saɓani a tsakaninmu da tawagar gwamnati,” in ji shi. “Mun amince kan abubuwa da dama, sai dai shugabanninsu, Ma’aikatar Ilimi da Gwamnatin Tarayya ba su ɗauki mataki kan kowanne ba.” Ya danganta yawan ficewa daga Najeriya da malamai da likitoci ke yi saboda ƙarancin...
Shugaba Bola Tinubu ya dawo Abuja, bayan ya kammala ziyarar aiki a ƙasashen Japan da Brazil. Mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya ce jirgin shugaban ƙasa ya tashi daga filin jirgin sama na Brasília a ƙasar Brazil da ƙarfe 12:57 na rana a ranar Laraba. A cewarsa ya iso Abuja da safiyar ranar Alhamis. Ga hotunan yadda wasu manyan jami’an gwamnati suka tarbi shugaban:
A lokacin ziyarar, ya gana da Shugaban Brazil, Luiz Inácio Lula da Silva, da sauran manyan jami’an ƙasar. Ƙasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniya guda biyar da suka shafi sufurin jiragen sama, harkokin waje, kimiyya da fasaha, da kuma noma, da wasu muhimman fannoni a ci gaban Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
’Yan bindigar da suka sace wani mutum, matarsa da ’yarsu a Jihar Katsina, na neman Naira miliyan 600 a matsayin kuɗin fansa. Wanda aka sace sun haɗa da Anas Ahmadu mai shekara 33, matarsa Halimat, da kuma ’yarsu Jidda. Ba zan tsaya takarar kowanne irin mukami ba a 2027 – El-Rufai NAJERIYA A YAU: Matakan da ciwon suga ke bi kafin illata mai fama da shi An sace su ne a gidajensu da ke Filin Canada Quarters a Sabuwar Unguwa, cikin garin Katsina da safiyar ranar Talata. A yayin kai harin, wani ɗan sa-kai mai shekara 25 mai suna Abdullahi Muhammad, ya rasu lokacin da yake ƙoƙarin ceto su. Wani ɗan uwan ma’auratan ya shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar...
Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya ce ba zai tsaya takarar kowanne irin mukami ba a zaben 2027, inda ya ce burinsa kawai ya samar wa jiharsa da Najeriya nagartattun shugabanni. Ya bayyana hakan ne ranar Laraba a Kaduna, lokacin da ya karbi wasu matasa karkashin jagorancin Aliyu Bello da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar hadakar ’yan adawa ta ADC. NAJERIYA A YAU: Matakan da ciwon suga ke bi kafin illata mai fama da shi Ruftawar katanga ta yi ajalin uwa da ’ya’yanta 2 a Zariya El-Rufa’i ya kuma soki lamirin gwamnati mai ci, inda ya ce ’yan Najeriya na ganin gazawarta karara ba tare da wani ya musu karin bayani ba. “Ba abin da wannan gwamnatin ke...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Mutane da dama ba sa sanin suna dauke da ciwon suga ballantana su san hanyoyin magance shi kafin ya yi tsanani. Sau da yawa ciwon sai ya kai wani matakin da zai yi wa mutum illa sannan yake sanin yana dauke da shi. NAJERIYA A YAU: Ci Gaban Da Harshe Da Al’adun Hausa Suka Samu A Shekaru 10 DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan matakan da ciwon suga ke bi kafin ya yi tsanani da kuma hanyoyin magance shi. Domin sauke shirin, latsa nan
Lardin Hubei shi ma ya bi sawu, inda ya bullo da nasa shirye-shiryen na raba takardun tallafin tare da mai da hankali musamman a kan bangaren da ya shafi cin abinci. Babban makasudin hakan shi ne a karfafa mutane su rika fita zuwa gidajen cin abinci. Wannan ya kara farfado da salon cin abinci tare a tsakanin Sinawa da kuma kwarya-kwaryan harkokin da ake yi a gefen wasu tituna bisa tsari. Baya ga bunkasa tattalin arziki, wannan dabara tana samar da yanayi mai dadi da faranta ran jama’a. Shi ma birnin Shanghai ba a bar shi a baya ba a kan wannan sabga, inda shi kuma ya mayar da hankali a kan nishadantarwa ta fuskar al’adu. Birnin ya...
Musiba da auka wa wani gida a Zariya da ke Jihar Kaduna, bayan da katangar wani kango da ke maƙwabtaka da su ta faɗa wa mazauna gidan suna tsaka da barci. Wakilinmu ya ruwaito cewa, ruftawar ginin wadda ta auku a safiyar wannan Larabar ta yi ajalin matar gidan, Habiba Nuhu da ’ya’yanta biyu, Hauwa’u da Aina’u Nuhu. Wani ɗan sanda ya harbe soja a Bauchi A ɗora min laifin hatsarin jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja — Shugaban NRC Sai dai mijinta, wanda shi ma ya samu rauni a sakamakon faruwar lamarin, tuni an sallamo shi bayan duba lafiyarsa a asibiti. Wani maƙwabcinsu, Malam Ahmed, ya shaida wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4 na asubahi,...
Wannan na zuwa ne bayan samun labarin kama wata mai suna Maryam Hussain Abdullahi a Saudiyya da zargin fataucin miyagun ƙwayoyi a daidai lokacin da take aikin Umara. Da yake bayyana yadda aka bankaɗo harƙallar ta hanyar, wadda ke jefa mutanen da ba su ji, ba su gani ba cikin masifa, ya ce ‘yan uwan wadanda aka kama ne a Saudiyya ne suka kawo ƙorafi ga hukumar NDLEA cewa an kama ’yan uwan su a Saudiyya, inda cikin gaggawa hukumar ta ƙaddamar da bincike. “’Yan Nijeriya da aka kama a Saudiyya su ne: Maryam Hussain Abdullahi da Abdullahi Bahijja Aminu da Abulhamid Sadiq waɗanda suka hau jirgin Ethiopian Airline mai lamba ET940, wanda ya bar Kano a ranar...
Wani jami’in ’yan sandan kwantar da tarzoma (MOPOL) mai muƙamin Insfekta ya harbe wani soja har lahira a garin Futuk, da ke Ƙaramar Hukumar Alkaleri ta Jihar Bauchi. Aminiya ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne bayan wata taƙaddama da ta taso kan wata mota mai ɗauke da ma’adinai da ake zargin ta wani kamfanin haƙar ma’adinai na ƙasar Sin ce. ASUU: Malaman Jami’ar FUK sun yi zanga-Zanga kan rashin cika musu alƙawura A ɗora min laifin hatsarin jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja — Shugaban NRC Mai riƙon muƙamin Daraktan Hulɗa da Jama’a na rundunar soji, Laftanar Solomon Atang Hallet, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an kama ɗan sandan da ake zargi, kuma ana ci gaba da...
A wata ziyarar da wata tawagar yan jarida daga Iran suka kai birnin Mosco, kasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjeniyoyin habaka dangantaka na sardarwa tsakanin kasashen biyu. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa hukumar tashoshin talabijin da Radiyo na kasar Iran da kuma na bangaren Rasha sun karan zurfafa dangantaka tsakaninsu a fagen yada labarai a yankin da kuma duniya gaba daya. Labarin ya kara da cewa wannan dangantakar zai sa fuskance labaran karya wadanda kafafen yada labarai na yamma suke yadawa. Har’ila yau yarjeniyoyin aiki tare tsakanin hukumomin watsa labaran kasashen biyu zai samar da labarai iri guda da kuma fadada hanyoyin samun labaran gaskiya a tsakaninsu. Daga cikin yarjeniyoyin dai akwai na tsakanin...

Jimilar Darajar Hada-Hadar Shige Da Fice A Fannin Bayar Da Hidimomi Ta Kasar Sin Ta Kai Yuan Tiriliyan 3.9 A Rabin Farko Na Shekarar Bana
Bikin CIFTIS na bana, zai kunshi nune-nune daga kasashe, da hukumomin kasa da kasa sama da 70. Kuma kusan kamfanoni 2,000 ne suka shirya shiga bikin a zahiri. (Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD (OHCHR) ta bayyana cewa sojojin HKI sun kashe Falasdinawa 982 a yankin yamma da kogin Jordan tun cikin watan Octb. Shekara ta 2023. Wannan banda wasu 42,000 da suka tilastawa barin gidajensu daga yankin. Banda haka sun rusa gidajen shaguna da sauran abinda Falasdinawa suka mallaka. Banda haka yahudawan da suke yankin suna kai farmaki kan Falasdinawa a yankin, inda suke kashe wasu Har’ila yau kungiyar red cross ta bayyana cewa ta sha jinyar wasu Falasdinawa a yankin Yamma da kogin Jordan wadanda suka sha hayaki mai guba wanda sojojin HKI suke jefa masu a yankin, Labaran sun kara da cewa a yau laraba sojojin yahudawan sun kai hare haren kan Falasdinawa a Nablus...
Ya yi alkawarin cewa, gwamnatinsa za ta kara hada kai da hukumomin tsaro domin dawo da zaman lafiya, tare da samar da kayayyakin agaji da tallafi ga wadanda abin ya shafa. Majiyoyin yankin sun ce al’ummar yankin sun sha fama da hare-hare akai-akai a ‘yan makonnin da suka gabata, lamarin da ya tilastawa mazauna yankin kauracewa gidajensu. Ku tuna cewa, Gwamna Radda a ranar 18 ga Agusta, 2025 ya bar kasar don hutun makonni uku domin duba lafiyarsa a kasar waje. Gwamnan ya samu rakiyar manyan jami’an gwamnati da shugabannin hukumomin tsaro na jihar da kuma kungiyoyin bayar da agajin gaggawa ga al’umma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun...
Ƙungiyar Malaman Jami’a (ASUU) reshen Jami’ar Tarayya Kashere (FUK), ta yi zanga-zangar lumana, inda ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta aiwatar da yarjejeniyar da suka yi da sauran buƙatunsu da ba a cika ba. Zanga-zangar ta fara ne daga ofishin ƙungiyar, ta bi ta ginin shugaban jami’ar, sannan ta ƙare a bakin ƙofar shiga makarantar. Dilan ƙwaya ya shiga hannu a Borno Ambaliya: Gwamnatin Yobe ta samar wa magidanta 250 matsugunin wucin gadi Shugaban ASUU na jami’ar, Dakta Shehu El-Rasheed, ya ce gwamnati ta kasa cika alƙawuran da suka jawo yajin aikin watanni takwas a shekarar 2022. Ya ce har yanzu ba a biya malamai albashin baya ba, haka kuma babu ƙarin albashi na tsawon shekaru. Ya ja hankalin gwamnati cewa...
Ƙungiyar Malaman Jami’a (ASUU) reshen Jami’ar Tarayya Kashere (FUK), ta yi zanga-zangar lumana, inda ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta aiwatar da yarjejeniyar da suka yi da sauran buƙatunsu da ba a cika ba. Zanga-zangar ta fara ne daga ofishin ƙungiyar, ta bi ta ginin shugaban jami’ar, sannan ta ƙare a bakin ƙofar shiga makarantar. Dilan ƙwaya ya shiga hannu a Borno Ambaliya: Gwamnatin Yobe ta samar wa magidanta 250 matsugunin wucin gadi Shugaban ASUU na jami’ar, Dakta Shehu El-Rasheed, ya ce gwamnati ta kasa cika alƙawuran da suka jawo yajin aikin watanni takwas a shekarar 2022. Ya ce har yanzu ba a biya malamai albashin baya ba, haka kuma babu ƙarin albashi na tsawon shekaru. Ya ja hankalin gwamnati cewa...
Shugaba Bola Tinubu ya yi alƙawarin hanzarta aiwatar da ci gaban Nijeriya ta hanyar amfani da fasahar kere-kere da tattalin abinci don samun nasarori irin na sauran ƙasashe masu tasowa kamar Brazil. A yayin da yake jawabi a ranar Talata a lokacin da ya gana da wasu ‘yan Nijeriya mazauna kasar Brazil, shugaba Tinubu ya jaddada kudirin gwamnatinsa na kawo sauyi ta hanyar kere-kere, gyare-gyare, da kuma samar da ci gaba mai dorewa. Sin Da Kasashen Afirka Za Su Rubuta Sabon Babin Hakkin Dan Adam Bisa Ci Gabansu NRC Ta Dakatar Da Sufurin Jirgin Ƙasan Abuja-Kaduna Bayan Hatsarin Da Ya Yi “Dole ne mu sanya Nijeriya a gaba wajen ci gaban Afirka, ta hanyar amfani da fasahar kere-kere, tattalin abinci,...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ta kama wani mutum da ake zargi da dillancin miyagun ƙwayoyi a Ƙaramar Hukumar Bayo. An cafke shi ne ranar 23 ga watan Agusta, 2025, yayin wani samame da ’yan sanda suka kai tare da haɗin gwiwar sashen leƙen asiri. DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Amurka ta ɗaure basaraken Osun kan zamba a tallafin COVID-19 Kakakin rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya ce an kama wanda ake zargin mai suna Nasiru Ibrahim da fakiti 25 na tabar wiwi. Ragowar ƙwayoyin da aka samu a wajensa sun haɗa da fakiti 34 na ƙwayar Exzol, da kuma ƙwayar D5 guda 600. An miƙa shi tare da kayan da aka ƙwato...
Gwamnatin Jihar Yobe ta kwashe magidanta sama da 250 daga Garin Kolo da ke Ƙaramar Hukumar Nangere, zuwa sabon matsuguni bayan ambaliyar ruwa ta lalata musu gidaje. An ƙaddamar da sabon matsugunin ne ƙarƙashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni domin kare rayukan waɗanda abin ya shafa. Amurka ta ɗaure basaraken Osun kan zamba a tallafin COVID-19 Amurka ta ɗaure basaraken Osun kan zamba a tallafin COVID-19 Babban sakataren Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar (YOSEMA), Alhaji Idi Jidawa, ya bayyana cewa an gina gidajen wucin gadi guda 22 domin amfanin mutanen. Haka kuma, an samar da rijiya, banɗakunan wucin gadi guda biyar, da motar ɗaukar marasa lafiya. Jami’an tsaro da suka haɗa da ’yan sanda da jami’an Sibil Difens...
’Yan bindiga sun kai hari garin Hunƙuyi da ke Ƙaramar Hukumar Kudan, a jihar Kaduna, inda suka kashe mutum ɗaya tare da sace wani ɗan kasuwa. Mutanen yankin sun ce maharan sun kai hari ne da misalin ƙarfe 12:30 na dare. ACReSAL ya tallafa wa manoma da buhunan iri 6,220 a Gombe Babu ɗaya daga cikin buƙatunmu da gwamnati ta aiwatar — Shugaban ASUU Maharan sun shiga yankin ne ta ɓangaren Katsina ɗauke da bindigogi, inda suka dinga harbi a sama. Sun harbe wani mutum mai suna Aminu Shehu har lahira, sannan suka yi awon gaba da wani ɗan kasuwa mai suna Alhaji Shehu Dakin. Majiyoyi, sun bayyana cewa maharan sun yi amfani da wayar Alhaji Shehu wajen kiran iyalansa,...
’Yan bindiga sun kai hari garin Hunƙuyi da ke Ƙaramar Hukumar Kudan, a jihar Kaduna, inda suka kashe mutum ɗaya tare da sace wani ɗan kasuwa. Mutanen yankin sun ce maharan sun kai hari ne da misalin ƙarfe 12:30 na dare. ACReSAL ya tallafa wa manoma da buhunan iri 6,220 a Gombe Babu ɗaya daga cikin buƙatunmu da gwamnati ta aiwatar — Shugaban ASUU Maharan sun shiga yankin ne ta ɓangaren Katsina ɗauke da bindigogi, inda suka dinga harbi a sama. Sun harbe wani mutum mai suna Aminu Shehu har lahira, sannan suka yi awon gaba da wani ɗan kasuwa mai suna Alhaji Shehu Dakin. Majiyoyi, sun bayyana cewa maharan sun yi amfani da wayar Alhaji Shehu wajen kiran iyalansa,...
Shirin Agro-Climatic Resilience in Semi-Arid Landscapes (ACReSAL) ya raba wa ƙungiyoyin manoma 47 a Jihar Gombe, buhunan iri na zamani 6,220 don bunƙasa harkar noma. An gudanar da rabon ne yayin taron kwanaki biyar na masu ruwa da tsaki kan kula da manyan koguna na Gongola, Gali-Lamurde da Hawal-Kilunga, wanda yake ɗaya daga cikin muhimman ayyukan ACReSAL a Najeriya. Babu ɗaya daga cikin buƙatunmu da gwamnati ta aiwatar — Shugaban ASUU ’Yan bindiga sun sace ma’aurata da ’yarsu mai shekara ɗaya a Katsina Shugaban shirin a Jihar Gombe, Dokta Sani Adamu Jauro, ya ce Gwamna Inuwa Yahaya ya nuna jajircewa wajen tallafa wa manoma ta hanyar shirin. Ya ƙara da cewa an samu nasarori kamar shuka bishiyoyi a dukkanin ƙananan...
Ministan harkokin wajen Iran ya ce: A shirye Iran take ta gudanar da shawarwari da Amurka, amma kan sharudda Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya ce; kasarsa a shirye take ta dawo da tattaunawar makamashin nukiliya da Amurka, amma tare da ba da tabbacin babu batun kai hari kan Iran. Ya bayyana cewa ba za a cimma abin da Amurka ke so ba ta hanyar kai harin soji kan cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran, kuma a duk wata tattaunawa dole ne Amurka ta kare sharuddan da Iran ta gindaya mata domin samun ci gaba mai daure wa. Araqchi wanda ya gana da Asharq Al-Awsat bayan halartar wani zama na musamman na ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan kasashen musulmi don...
Ministan harkokin wajen kasar Venezuela ya bayyana jin dadinsa ga hadin kai da goyon bayan Iran ga kasarsa A wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na kasar Iran, ministan harkokin wajen kasar Venezuela ya yabawa irin hadin kai da goyon bayan Iran ga ‘yancin kai, yana mai jaddada aniyar Iran na kare ta daga barazanar Amurka. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya tattauna da takwaransa na kasar Venezuela Ivan Gil Pinto ta wayar tarho game da alakar da ke tsakanin kasashen biyu da kuma ci gaban da ake samu a yankin Caribbean. A cikin wannan kiran, Ministan Harkokin Wajen Venezuela ya ba da rahoto kan abubuwan da ke faruwa a yankin Caribbean bayan karuwar barazanar Amurka da...
Shugaban Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU), Farfesa Chris Piwuna, ya ce Gwamnatin Tarayya ba ta aiwatar da ɗaya daga cikin yarjejeniyar da ta ƙulla da ƙungiyar ba. Ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin hira da gidan talabijin na Trust TV. ’Yan bindiga sun sace ma’aurata da ’yarsu mai shekara ɗaya a Katsina DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Farfesa Piwuna, ya ce ASUU a koyaushe na zaɓar tattaunawa da jami’an gwamnati a matsayin mafita. Amma duk da cewa sun cimma matsaya kan batutuwa masu muhimmanci kamar kuɗaɗen gudanarwa, albashi, ’yancin malamai, ‘yancin jami’o’i, da sake duba wasu dokoki, ba a ɗauki mataki kan kowanne ba. “Babu saɓani a tsakaninmu da tawagar...
Uzodimma ya ce ƙarin albashi zai inganta rayuwar ma’aikata, sannan ya bunƙasa tattalin arziƙin jihar. Ya kuma bayyana cewa kuɗaɗen shiga na cikin gida sun ƙaru daga Naira miliyan zuwa sama da Naira biliyan uku a kowane wata, yayin da bashin jihar ya ragu daga sama da Naira biliyan 280 a shekarar 2020 zuwa Naira biliyan 100. Ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu bisa cire tallafin mai, yana cewa duk da ya jawo tsadar rayuwa, amma ya ƙara yawan kuɗin da ake raba wa jihohi kuma ya bai wa gwamnati damar yin sauye-sauye. Gwamnan ya ƙara da cewa daga ranar 27 ga watan Agusta, gwamnati za ta fara biyan kashin ƙarshe na kuɗaɗen fansho da ake bai wa tsoffin ma’aikata,...
Maharan da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne a ranar Talata sun sace mata da miji tare da ’yarsu mai shekara ɗaya a cikin birnin Katsina. An dai kai harin ne a gidan ma’uratan, Anas Ahmadu, da matarsa Halimatu, da kuma ’yarsu Jiddah a Unguwar Kanada a yankin Ƙofar Ƙaura a Katsina. DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa NRC ta dakatar da jigilar jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja Rahotanni sun ce an kai harin ne wajen misalin ƙarfe 3:00 na daren Litinin inda maharan suka sace magidancin mai suna Malam Anas tare da matarsa mai suna Halimatu da ’yarsa. Bayanai sun kuma nuna wani dan bangar da yayi ƙoƙarin kai musu ɗauki ya rasa...
Haka kuma, a wani samame daban da rundunar ta kai a ranar 15 ga watan Agusta, 2025, ‘yansanda a ƙaramar hukumar Danko/Wasagu sun yi artabu da ‘yan bindiga a kusa da garin Dankade. Sun ceto mutum biyu da aka sace; Tukur Bello da Isyaka Abubakar, waɗanda aka sace a dajin Gairi na Jihar Zamfara a ranar 9 ga watan Agusta yayin da suke kiwon shanu. ‘Yansanda sun ce sun ƙwato makamai da harsasai daga hannun ‘yan bindigar, tare da alƙawarin ci gaba da yaƙi da masu garkuwa da mutane a faɗin ƙasar nan. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp...
Masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin cewa dawowar Jonathan ko Obi na iya sauya tsarin PDP wajen fafatawa da jam’iyyar mai mulki ta APC. Jonathan na da magoya baya masu tsayi da suka daɗe a PDP, yayin da Obi kuma ya fi jan hankalin matasa. Sai dai har yanzu akwai tambayoyi kan ko za su amince da wannan kira, da kuma yadda PDP za ta shawo kan matsalolin cikin gida kafin zaɓen fidda gwani. Zuwa yanzu, babu wanda ya fito fili daga cikinsu ya tabbatar da komawarsa PDP. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da...
Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS ta ce tana shirin kafa wata runduna ta dakaru 260,000 domin yaki da ta’addanci. Shugaban hukumar ta ECOWAS, Omar Alieu Touray ne ya bayyana haka a taron hafsoshin tsaron kasashen Afrika na shekarar 2025 a Abuja. Taken taron shi ne “Maganin barazana ga zaman lafiya da tsaro a Afirka a wannan zamani: muhimmancin hadaddiyar dabarun tsaro.” Touray wanda ya samu wakilcin kwamishinan harkokin siyasa, zaman lafiya da tsaro na kungiyar ECOWAS, Ambasada Abdel-Fatau Musah, ya ce hakan wani bangare ne na rage tushen ta’addanci da sauran nau’ikan rashin tsaro a yankin. Ya ce baya ga matakan yaki da ta’addanci, kungiyar tana kuma kokarin aiwatar da dabarun tsaron teku, yana mai cewa babu...
Shugaba Donald Trump, ya yi barazanar sauke Lisa Cook, Gwamnar Babban Bankin Amurka (Federal Reserve), yana mai sukar yadda ake tafiyar da harkokin bankin, musamman batun bayar da bashi da tsare-tsaren lamuni. A wata sanarwa da fadar White House ta fitar, Trump ya zargi Cook da gabatar da “bayanan ƙarya” kan sharuɗan bayar da lamunin gidaje (mortgage), yana mai cewa hakan ya jefa dubban Amurkawa cikin wahala sakamakon hauhawar kuɗin ruwa da kuma tsadar bashi. Sai dai Lisa Cook ta mayar da martani da cewa shugaban ba shi da ikon sauke ta daga muƙamin da take riƙe da shi, saboda dokar da ta kafa Babban Bankin Amurka ta tanadar da cikakken ’yanci ga ’yan kwamitin gudanarwarsa. Ta sha alwashin cewa...
Adadin wadanda suka mutu sakamakon hare-hare biyu da Isra’ila ta kai a yankin Damascus ya karu zuwa 5, yayin da wasu ma’aikatan ma’aikatar tsaron kasar Syria suka samu raunuka, a cewar kungiyar kare hakkin bil’adama ta Syria. Cibiyar sa ido ta kasar Syria ta sanar a yammacin jiya Talata cewa, hare-haren biyu an kai su ne a yankin al-Kiswah da ke yankin Damascus, kusa da hanyar Suwayda, tare da raunata wasu sojojin sabuwar gwamnatin kasar ta Syria, wanda suka kasance mambobin kungiyar Hay’at Tahrir al-Sham mai alaka da kungiyar da Aqaida. Majiyoyin cikin gida sun kuma tabbatar da cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kai hari a wani shingen binciken sojojin sabuwar gwamnatin...
Cutar kwalara ta ɓarke a ƙananan hukumomin Gumi da Bukkuyum a Jihar Zamfara, inda ta kashe aƙalla mutum bakwai tare da kwantar da kusan mutum 200 a asibiti. Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar yankin, Hon. Sulaiman Abubakar Gumi, ya ce cutar ta fara tun 10 ga watan Agusta, kuma tana ƙara yaɗuwa. Gwamnati Ta Fara Aikin Gyara Na’urar Watsa Shirye-shirye Mai Gajeren Zango Ta Gidan Rediyon Muryar Nijeriya Hukumar NRC Ta Dakatar Da Zirga-zirgar Jiragen Kasa Na Abuja zuwa Kaduna Ya bayyana cewa rashin tsaftar muhalli da ruwan sama sun taimaka wajen yaɗuwar cutar, musamman a inda ‘yan gudun hijira suke zaune. Ya yi gargaɗin cewa idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba, cutar na iya zama annoba. Daga...

Gwamnati Ta Fara Aikin Gyara Na’urar Watsa Shirye-shirye Mai Gajeren Zango Ta Gidan Rediyon Muryar Nijeriya
Idris ya gode wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa hangen nesan sa da jajircewar sa wajen zamanantar da kayan aikin yaɗa labarai a Nijeriya. A cewar sa: “Yayin da muke ɗaukar wannan babban mataki na ƙaddamar kwangilar gyara tiransimitar ‘shortwave’ ta Muryar Nijeriya mai ƙarfin kilowat 250, ya dace mu nuna ɗimbin godiyar mu ga Mai Girma Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, bisa hangen nesa da jajircewar sa wajen farfaɗo da kuma zamanantar da kayan aikin yaɗa labarai na Muryar Nijeriya.” Ya kuma tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa wannan aikin zai sauya yanayin yadda ake yaɗa labarai a ƙasar nan. Ya ce: “Da zarar an kammala wannan aiki, na’urorin tiransimita na VON da aka...
Yakin duniya na II abu ne da ya keta kasashe da iyakoki da launin fata, wanda a karshe ya kawo hadin kai tsakanin kasa da kasa domin wanzar da zaman lafiya da ci gaban duniya. Shekaru 80 bayan samun nasarar yaki da masu danniya, ya kamata a yi waiwaye, a nazarci nasarar da aka samu da kyar, da tsamo hikimomi da dabaru da ma hanyoyin karfafa gina duniya cikin kawanciyar hankali da lumana. Yayin da al’ummomin kasashen duniya ke ganin wasu kasashe na kokarin lalata wannan nasara, ya zama wajibi a tsaya tsayin daka wajen bijire musu, don ganin ba a bar su sun mayar da hannun agogo baya ba. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
Fasinjoji na jirgin kasa wanda ya taso daga Abuja zuwa Kaduna ya sauka kan layin dogo da misalign karfe 11:00 nan safe kusa da garin jere. Da dama daga cikin fasinjojin suna cikin tashin hankali saboda matsalolin tsaro da ake fama da shi a kan hanyar. Amma Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa an kawo jami’an tsaro a yankin don tsaron fasinjojin. Kamfanin jiragen kasa na kasa wato ‘The Nigerian Railway Corporation (NRC) bai bada wani bayani kan al-amarin ba har zuwa lokacin bada wannan labarin. Saukan jirgin daga layin dogon dai bai jiwa wani rauni ba, kuma babu wanda ya rasa ransa. A cikin watan mayun shekara ta 2024 da ya gabata ma, an sami...
Fasinjoji na jirgin kasa wanda ya taso daga Abuja zuwa Kaduna ya sauka kan layin dogo da misalign karfe 11:00 nan safe kusa da garin jere. Da dama daga cikin fasinjojin suna cikin tashin hankali saboda matsalolin tsaro da ake fama da shi a kan hanyar. Amma Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa an kawo jami’an tsaro a yankin don tsaron fasinjojin. Kamfanin jiragen kasa na kasa wato ‘The Nigerian Railway Corporation (NRC) bai bada wani bayani kan al-amarin ba har zuwa lokacin bada wannan labarin. Saukan jirgin daga layin dogon dai bai jiwa wani rauni ba, kuma babu wanda ya rasa ransa. A cikin watan mayun shekara ta 2024 da ya gabata ma, an sami...
Akalla mutum daya ne ya rasa ransa a yankin Qunaitra na kasar Siriya a lokacinda HKI suka kai hare-hare a yankin da jirgin yaki wanda ake sarrafashi daga nesa wato Drons. Kamfanin dillancin labaran SANA na gwamnatin kasar Siriya ya bayyana cewa majiyar yankin wanda yake kudu maso yammacin duddan Golan wadanda HKI ta mamaye, ya bayyana cewa tun bayan kifar da shugaba Asad a shekarar da ta gabata, sojojin HKI sun kai hare-hare kan dukkan rumbun ajiyar makamai na sojojin Bashhar Al-asad, kuma su kan kai hare-hare da dare a kan yankun dukkan Golan na kasar siriya wanda yaejeniyar 1974 ya bayyana a matsayin yankin babu makamai. Sannan sukan kai hare hare kan yankin Suwaida su kashe wanda suka...
Ribadu ya yaba da jajircewar sojoji da ‘yansanda da sauran jami’an tsaro da suka gudanar da aikin, yana mai cewa, wannan wata nasara ce da za a yi alfahari da ita a tarihin yaki da ta’addanci. A Guji Siyasantar da Tsaro Sai dai Ribadu ya gargadi shugabannin siyasa da masu rike da madafun iko da su guji siyasantar da al’amuran tsaro, yana mai cewa: “Wannan ƙalubale na gama gari ne, ba wai na shugabanni kaɗai ba. Domin haka nake kira ga al’umma da shugabanni su daina siyasantar da tsaro.” Ribadu ya ƙara da cewa, gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu, za ta ci gaba da yin duk abin da ya kamata domin magance barazanar tsaro tare da kawo...
A yau Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping da uwargidansa Peng Liyuan suka gana da Sarkin Cambodia Norodom Sihamoni, da mahaifiyarsa Sarauniya Norodom Monineath Sihanouk a birnin Beijing. Xi ya yi kyakkyawar maraba da zuwan Sarki Norodom Sihamoni da mahaifiyarsa Sarauniya Norodom Monineath Sihanouk kasar Sin, kana ya yi lale maraba da halartar Sarki Sihamoni bikin da za a yi na cika shekaru 80 da samun nasarar yakin turjiyar jama’ar kasar Sin kan zaluncin kasar Japan, da kuma yaki da mulkin danniya a duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da...
Hukumar Hisbah ta haramta karuwanci da duk wasu munanan ɗabi’u da ake gudanarwa a otal-otal, wuraren casu da duk wasu cibiyoyin nishaɗi a Jihar Bauchi. Babban Kwamishinan Hisbah, Barista Aminu Balarabe Isah, ya bayyana haka ne a yayin wani taron tattaunawa da masu otal-otal da wuraren shaƙatawa a Bauchi. Trump ya yi barazanar korar Gwamnar Babban Bankin Amurka Jirgin kasa dauke da fasinjoji ya yi hastari a hanyar Kaduna-Abuja Ya ce an haramta gudanar da al’adun gargajiya irin su Shadi, Sharo, Garaya da kuma shagulgulan wannan zamani kamar Kauyawa Day, Gala, DJ, Aloba da sauransu a bukukuwan aure. Isah ya ce an ɗauki waɗannan matakan ne bayan samun korafe-korafe daga jama’a kan yadda abubuwa na rashin tarbiyya da tayar da...
Har yanzu babu tabbaci ko zai iya buga wasan. Arsenal na fatan cewa Saka da Odegaard ba za su daɗe suna jinya ba. A kakar da ta wuce, Saka ya sha fama da rauni har ya yi watanni uku ba ya wasa. Sai dai a bana Arsenal ta ƙara wasu sababbin ‘yan wassan gaba kamar Viktor Gyokeres da Eberechi Eze, baya ga waɗanda ta ke da su kamar Gabriel Martinelli, Leandro Trossard, Ethan Nwaneri da Max Dowman don rage giɓin Saka da Odegaard. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe...
Jirgin kasa dauke da fasinjoji a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja ya sauka daga kan titi. Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin tarogon jirgin kasan sun mirgina a yayin da fasinjoji suka shiga tashin hankali.
Kalli hotuna da bidiyo da sauran bayanai kai tsaye daga shafin Aminiya kamar kana wurin da ake gudanar da gagarumin bikin Ranar Hausa ta Duniya ta 2025.
A halin yanzu Sarkin Daura, ya hallara a filin gagarumin bikin Ranar Hausa ta Duniya da a bana ake gudanarwa a fadarsa, inda za a gudanar da hawan daba na musamman. Sarkin Daura ya karbi bakuncin Gwamnan Jihar Damagaram daga Jamhuriyar Nijar, Kanar Yosouf Labo da kuma Sarkin Damagaram, Aboubacar Sanda Oumarou a fadarsa, albarkacin bikin Ranar Hausa ta Duniya. Ga kadan daga cikin hotunan yadda kasaitaccen bikin ke gudana.
shafin Jagoran juyin juya halin Musulunci a cikin harshen Yahudanci ya bayyana cewa: ‘Yan sahayoniyya sune wadanda aka fi kyamata a duniya Shafin Jagoran juyin juya halin Musulunci na yaren yahudanci a shafin sada zumunta na X ya rubuta cewa: Makiyar al’ummar Iran na kan gaba a yau ita ce, gwamnatin ‘yan sahayoniyya wacce ita ce mafi kyamata a tsakanin al’ummar duniya. Shafin yanar gizo na KHAMENEI.IR na yaren yahudanci ya wallafa wani kaso na jawabin Jagoran a jiya litinin a wajen taron juyayin shahadar Imam Ali dan Musa al-Rida Jagoran shiriya na Iyalan gidan Manzon Allah {s.aw}. Sanarwar ta kara da cewa: “Makiyar al’ummar Iran a yau, ita ce gwamnatin ‘yan sahayoniyya, wacce duniya ta fi kyama a duniya....
Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka ta ECOWAS ta bayyana shirinta na kafa rundunar yaki da ta’addanci mai dauke da sojoji 260,000 domin tunkarar barazanar tsaro da ke kara ta’azzara a yankin. Shugaban ECOWAS, Omar Alieu Touray, wanda wakilinsa Abdel-Fatau Musah ya gabatar da jawabi a taron shugabannin rundunonin tsaro na Afirka da aka gudanar a Abuja, ya ce wannan mataki na daga cikin kokarin dakile ayyukan ta’addanci da sauran matsalolin tsaro da suka addabi yankin. “Babu wani yanki a Afirka da ya tsira daga ta’addanci, rikice-rikicen cikin gida da kuma koma-baya ta fannin ci-gaba,” in ji Musah. ECOWAS ta ce za ta bukaci dala biliyan 2.5 a kowace shekara domin tallafa wa rundunar da kayan aiki da kudaden gudanarwa....
Yau 26 ga watan Agusta take ranar murnar zagayowar bikin Ranar Hausa ta Duniya. A halin yanzu shirye-shirye sun yi nisa domin fara gagarumin bikin Ranar Hausa ta Duniya a birnin Daura, Jihar Katsina. An shirya gudanar da gagarumin bikin na bana a birnin Daura ne, kasancewarsa inda ake gani a matsayin asalin Hausawa, shekaru arau-aru. Mahaya dawaki da sauran mahalarta bikin daga sassa daban-daban na Najeriya da kasashen waje da mazauna garin Daura sun fara tururuwa zuwa filin bikin, wanda zai samu. An kuma shirya gudanar da gagarumin hawan daba a Fadar Sarkin Daura, albarkacin zagayowar bikin Ranar Hausa ta Duniya karo na 10. A wannan ranar ake cika shekara 10 da fara wannan gagarumin biki,...
Mataimakin Ministan harkokin wajen Iran da takwarorinsa na Faransa, Jamus, da Birtaniyya za su gudanar da wani sabon zagaye na tattaunawa a birnin Geneva na kasar Switzerland, a daidai lokacin da kasashen uku ke barazanar aiwatar da abin da ake kira tsarin dawo da takunkumin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a kan Iran. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya fada a ranar Litinin cewa, za a koma yin shawarwari tsakanin wakilan Iran da E3 a ranar Talata. Ya ce za a gudanar da taron ne a matakin mataimakan ministocin harkokin waje da daraktocin siyasa. Hakan na zuwa ne bayan wata tattaunawa ta wayar tarho tsakanin ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da babban wakilin kungiyar EU mai...
Harin sama na Isra’ila kan cibiyar lafiya ta Nasser Medical Complex a Khan Younis ya kashe ‘yan jarida biyar ranar Litinin. Daga cikinsu akwai mai ɗaukar hoto Moaz Abu Taha da Mariam Abu Daqqa da mai ɗaukar bidiyon gidan talabijin na Palestine TV Hussam al-Masri, da kuma ɗan jaridar Al Jazeera Mohammad Salama da ma’aikacin kwantaragi na Reuters Hatem Khaled, in ji majiyoyin lafiya da kuma kafar watsa labaran da ke Qatar. Kashe-kashe na baya bayan nan sun nuna irin gagarumar ta’adin da yaƙin ya yi a kan ‘yan jaridan Gaza, lamarin da ya mayar da yankin wuri mafi hatsari ga ‘yan jarida a duniya. Daga farko a cikin ƙarshen mako, ƙungiyar ‘yan jarida ta Falasɗinu ta tabbatar da cewa...
A duk ranar 26 ga watan Agustan kowace shekara ake bukukuwan zagayowar Ranar Hausa ta Duniya. An fara wannan biki ne tun a shekarar 2015, inda wani tsohon ma’aikacin sashen Hausa na BBC kuma ma’aikacin TRT Hausa a yanzu, Abdulbaƙi Jari Aliyu ya ƙirƙiro tare da wasu masu amfani da shafukan sada zumunta. An ɓullo da ranar ce domin haɗa kan masu magana da harshen Hausa a faɗin duniya da nufin magance matsalolin da ke ci musu tuwo a ƙwarya. Da farko dai, an fara bikin wannan rana ce kamar wasa a shafukan sada zumunta, inda aka yi ta amfani da kalmar #RanarHausa. Zuwa shekara ta 2018 kuma aka fara yin bikin a zahiri tare da gudanar da tarurruka...
Na yi imani babu rayuwa ba tare da harshe ba, domin duk wata al’umma tana da buƙatar harshe domin gudanar da rubuce-rubuce, kimiyya da fasaha. Amma an yi sakaci da nazarin harshen Hausa, duk da cewa yana cikin manyan harsunan duniya masu ƙarfi da adabi. Don haka zan fara bayyana matsalolin, sannan in kawo shawarwari. Matsala ta farko: Sai Bango Ya Tsage… Idan gwamnati da manyan al’umma ba su ɗauki Hausa da muhimmanci ba, ba zai samu ci gaba ba. An taɓa samun shugaban ƙasa da ya ce nazarin wasu darusa ɓata lokaci ne, amma shi kansa a lokacin yaƙin neman zaɓe da Hausa yake magana. Gwamnati ta nuna rashin kulawa da harshen Hausa, tana ganin ba shi da amfani....