Shugaban Xi Ya Gana Da Firaministan Rasha
Published: 4th, November 2025 GMT
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan Rasha Mikhail Mishustin yau Talata a birnin Beijing, inda suka yi kira da inganta dangantakar kasashen biyu a bangarori daban-daban da kyautata hadin gwiwarsu kan dabarun samun ci gaba.
Ya ce tun daga farkon bana, Sin da Rasha ke gudanar da harkokinsu cikin nutsuwa duk da yanayi na hargitsi da suke fuskanta a waje, inda suka mayar da hankali kan ingantattun muradun ci gaba.
Da yake bayyana cewa an tsara taswirar bunkasa dangantakar kasashen biyu ne yayin taron da suka yi da shugaba Vladimir Putin a bana, shugaba Xi ya ce kasashen biyu za su ci gaba da tafiya tare da aiwatar da batutuwan da shugabanninsu suka cimma da kuma fadada hadin gwiwarsu bisa muhimman muradun kasashen biyu da jama’arsu, ta yadda za su bayar da karin gudunmawa ga zaman lafiya da ci gaban duniya. (Faeza Mustapha)
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
An Bude Sabon Babin Huldar Sin Da Koriya Ta Kudu
ShareTweetSendShare MASU ALAKA