Tanzaniya: An rantsar da shugaba Samia a wa’adi na biyu na shugabanci
Published: 4th, November 2025 GMT
A Tanzaniyaan rantsar da Shugabar kasar Samia Suluhu Hassan a wa’adinta na biyu bayan ta lashe zaben da ya haifar da mummunar zanga-zanga a fadin kasar.
An ayyana Samia, wacce ta hau mulki a shekarar 2021 bayan mutuwar magabacinta, a matsayin wacce ta lashe zaben da aka gudanar a makon da ya gabata da kashi kusan 98.                
      
				
Tayi rantsuwar kama aikin ne a sansanin sojoji da ke Dodoma, babban birnin kasar.
Samia Hassan mai shekaru 65 ta fafata da ‘yan takara daga kananan jam’iyyu, yayin da manyan abokan hamayyarta daga manyan jam’iyyun adawa biyu aka haramta musu tsayawa takara.
Babbar jam’iyyar adawa a kasar ta ce an kashe daruruwan mutane a zanga-zangar.
Gwamnati ta yi watsi da mace-macen, tana mai cewa “an zuzuta alkalumman.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iraniyawa na bikin tunawa da karbe ofishin jakadancin Amurka a Tehran a 1979 November 4, 2025 ICC : Rikicin Sudan kan Iya kasancewa Laifukan yaki da cin Zarafin dan Adam November 4, 2025 Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya saboda Dalilan Tsaro November 4, 2025 Hizbullah Ta yi Gargadin Mayar Da Martani Idan isra’ila Tayi Kokarin Kai Samame Ta Kasa November 4, 2025 Iran Tayi Maraba Da Kalaman Da Hukumar IAEA Kan Shirinta Na Nukuliya November 4, 2025 Prime Ministan Sudan Yayi Gargadi Game Da Aikewa Da Dakarun Tabbatar Da Zaman Lafiya Kasar November 4, 2025 Ribadu Ya Gana Da Manyan Hafsoshin Tsaron Najeriya kan barazanar Trump November 4, 2025 Mutum Daya Ya Yi Shahada Sanadiyyar Harin Sojojin HKI A Kudancin Lebanon November 3, 2025 Kungiyar Likitocin Kasar Sudan: Rundunar RSF Tana Garkuwa Da Dubban Fararen Hula A Al-Fasha November 3, 2025 An Sami Tsaikon Sauka Da Tashin Jiragen Sama A Tanzania Saboda Rikicin Zabe November 3, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Girgizar kasa ta yi ajalin gomman mutane a Afghanistan
Rahotanni daga Afganistan na nuni da cewa mutane akalla 20 ne suka rasa rayukansu a wata girgizar data auka wa kasar a cikin daren jiya Lahadi.
Girgizar kasar ta auku ne a arewacin kasar ta Afghanistan a yankin Kholm, da lardin Samangan, kusa da birnin Mazar-e-Sharif, inda ta yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 20, a cewar Ma’aikatar Lafiya ta kasar.
Duk da haka, adadin wadanda suka mutu na iya karuwa sosai.
Wannan sabuwar girgizar kasa ta zo ne watanni biyu bayan girgizar kasa mafi muni a tarihin kasar.
Hukumar Kula da Bala’i ta Kasa ta Afghanistan ta ba da rahoton cewa yawancin wadanda suka ji rauni a Samangan sun koma gida bayan sun sami magani.
A Mazar-e-Sharif, babban birni a lardin Balkh da ke arewacin Afghanistan, Masallacin Shuɗi mai tarihi ya lalace.
Ma’aikatar Tsaro ta ba da rahoton sake buɗe hanyar da zaftarewar ƙasa ta katse ta kuma ceto mutanen da suka makale a wurin cikin daren jiya.
Wannan girgizar ƙasa ta zo ne bayan girgizar ƙasa mai girman maki 6 da ta afkawa lardunan gabashin Kunar, Laghman, da Nangarhar a ƙarshen watan Agusta inda ta kashe mutane sama da 2,200, ta raunata kusan wasu 4,000, ta kuma lalata gidaje 7,000, a cewar hukumomin Taliban.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Najeriya : tun kafin kalamman Trump muka dauki matakai November 3, 2025 Sudan : Mutane 1,500 sun rasa matsugunansu sakamakon tashin hankali November 3, 2025 UNICEF Tayi Gargadi Game Da Mawuyacin Hali Da Yara Ke Ciki A Gaza November 3, 2025 Hamas Ta yi Watsi Da Zargin Da Amurka Tayi Mata Kan Batun Motocin Agaji A Gaza November 3, 2025 El-Zakzaki: Yakin Sudan Yana Kare Maslahar Kasashen Yamma ne Kawai November 3, 2025 Iran Ta Karbi Sako Kan Batun Komawa Teburin Tattaunawa Ba Kai Tsaye Ba November 3, 2025 Ministar Jin Dadin Jama’a ta Sudan: Mayakan RSF Sun Kashe Mata 300 Da Yi Wa 25 Fyade A El Fasher November 3, 2025 Pezeshkian: Bunkasa Masana’antar Makamashin Nukiliyar Iran Don Inganta Rayuwar Al’ummar Iran Ne November 2, 2025 Araqchi: Da Hadin Bakin Amurka, Gwamnatin Isra’ila ta kaddamar Da Hari Kan Kasar Iran November 2, 2025 Larijani: Iran Ba Ta Tsoron Gudanar Da Tattaunawa, Amma Ta Zama Mai Amfani November 2, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci