KADUNA TA ZAMA JIHAR FARKO A NIJERIYA DA TA AIWATAR DA SHIRIN SAMAR DA ABINCIN MAI GINA JIKI GA YARA – UNICEF
Published: 4th, November 2025 GMT
KADUNA TA ZAMA JIHAR FARKO A NIJERIYA DA TA AIWATAR DA SHIRIN SAMAR DA ABINCIN MAI GINA JIKI GA YARA – UNICE
Daga Abdullahi Shettima.
Hukumar Asusun kula da yara kananan yara ta majalisar dinkin duniya (UNICEF) ta jinjinawa gwamnatin jihar Kaduna bisa zama jihar farko a Nijeriya da ta amince kuma fara aiwatar da shirin samar da abinci mai gina jiki da lafiya ga yara kanana (RUTF) wanda hakan ya zama wani muhimmin mataki wajen yakar karancin abinci mai gina jiki tsakanin yara.
Da take jawabi yayin wani taron hadin gwiwa da gwamnatin jihar Kaduna, wakiliyar UNICEF a Nijeriya, Wafaa Saeed Abdelatef, ta bayyana yadda jihar Kaduna ta nuna gagarumar jajircewa a bangaren kiwon lafiya tare da samar da walwalar yara da cika alkawuran kuɗin haɗin gwiwa akai-akai.
Tace “Jihar Kaduna ta zama abin koyi ga sauran jihohi. Yadda gwamnati ta rungumi shirin samar da abinci mai gina jiki da lafiya ( RUTF) da sauri kuma ta fara aiwatar da shi na nuna cikakkiyar niyya wajen kare rayuwar yara da tabbatar da cewa babu wani yaro da zai ci gaba da fama da rashin abinci mai gina jiki,”
Taron wanda aka gudanar da shi a fadar gwamnatin jihar Kaduna, ya zama abin tarihi a dangantakar hadin gwiwar da ke tsakanin UNICEF da gwamnatin jihar Kaduna wajen inganta lafiya da walwalar yara.
Gwamna Uba Sani ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da gina kan wannan nasara, inda ya bayyana shirin RUTF a matsayin wani muhimmin ɓangare na dabarar gwamnatin sa wajen yakar rashin abinci mai gina jiki da inganta ci gaban jama’a baki ɗaya.
“Kaddamar da rabon abincin RUTF a fadin jihar Kaduna wani babban mataki ne na kawo ƙarshen cutar karancin abinci mai gina jiki,”
“Mun kuduri aniyar cewa babu wani yaro da za a bar shi a baya wajen yaƙar yunwa, rashin lafiya, da kuma samar da makoma mai kyau.” inji gwamna Uba Sani
Gwamnan ya kuma godewa UNICEF bisa wannan haɗin gwiwar da ke samar da sauye-sauye masu amfani a fannoni kamar su lafiya, abinci mai gina jiki, ilimi, da tsaftar ruwa da muhalli.
Ya kara da cewa shiga jihar Kaduna cikin muhimman shirye-shirye irin su RUTF da ASWA III wanda Kaduna ita kaɗai ce ta shiga cikinsa a Nijeriya na nuna hangen nesan gwamnatinsa na gina tsarin da ke tallafa wa marasa ƙarfi a fadin jihar baki daya.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: gwamnatin jihar Kaduna samar da abinci
এছাড়াও পড়ুন:
Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya
Ya ce Sin tana maraba da kamfanonin dake fuskantar kalubale su tuntubi ma’aikatar ko hukumomi masu ruwa da tsaki, yana cewa, ma’aikatar za ta nazarci ainihin abubuwan dake faruwa da kuma bayar da damar fitar da kayayyaki ga wadanda suka cancanta. (Mai fassara: FMM)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA