Sin Ta Gudanar Da Gasar Kirkire-kirkire Ta Daliban Kasa Da Kasa A Yankin Afirka Karo Na Farko
Published: 26th, July 2025 GMT
Jiya Juma’a an kammala zagayen karshe na gasar kirkire-kirkire, ta daliban kasa da kasa ta kasar Sin ta yankin Afirka a birnin Nairobin kasar Kenya, wadda jami’ar koyon ilmin aikin gona ta Nanjing ta kasar Sin ta karbi bakuncin shiryawa. Wannan shi ne karon farko da aka gudanar da gasar a nahiyar Afirka.
Rahotanni na cewa, an gudanar da gasar ne a tsawon kwanaki biyu, kuma dalibai 559 daga jami’o’in Afirka 115 sun yi rajitar halartar gasar, kana an baje kayayyakin shiga gasar har 185, wadanda suke shafar fasahohin aikin noma da abinci, da amfani da basirar AI, da kiyaye muhalli, da samun ci gaba mai dorewa da sauransu.
A karshe, alkalan gasar sun tattauna, tare da tsai da kudurin bayar da lambobin yabo ga tawagogi 30 na jami’o’i 21 daga kasashe 9. A cikinsu, tawagar jami’ar Egerton ta kasar Kenya, ta samu lambar yabo ta zinari bisa aikin da ta gabatar na dasa tsiron tumatir a jikin wata bishiya ta daban.
Mataimakiyar shugaban jami’ar koyar da ilmin aikin gona ta Nanjing Zhu Yan, ta bayyana cewa, an gudanar da gasar kirkire-kirkire ta daliban kasa da kasa ta kasar Sin ta yankin Afirka karo na farko ne, don sa kaimi ga matasan Sin da Afirka, da su yaukaka mu’amalar al’adu da juna, da kokarin yin kirkire-kirkire tare, da kuma nazarin samar da ci gaba mai dorewa tare. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Dalilin Da Ya Sa Hukumar NIWA Ta Fara Gyaran Hanyoyin Ruwa A Jihar Legsa
Manajar ofishin na NIWA, da ke a jihar ta Legas Injiniya Sarat Braimah ta bayyana cewa, tura ma’ikatan hukumar domin yin aikin, zai taimaka wajen gudanar da aikin a cikin inganci.
Kazalika, ya sanar da cewa, hakan zai kuma bayar da damar yin safarar kaya a cikin sauki da kuma safarar matafiya da ke bin hanyar ruwa ta yankin na Ikorodu.
“Mun yi nazari a cikin kwanciyar hankali kan yadda za a tabbatar da an cire fulawar da ke a cikin kasan ruwan ba tare da wata miskila ba tare da kuma bai wa jiragen ruwan damar yin zirga-zirgarsu a hanyoyin ruwan, ba tare da wata matsala ba, “ Inji Injiya Braimah.
“ Aikin ya wuce batun fannin samar da saukin yin sufurin jiragen ruwan har da tabbatar da an kiyaye janyo matsala ga ayyukan kamun Kifi a hanyoyin na ruwan, “ A cewar Inji Manajar.
Ta kara da cewa, babban shugabanmu na hukumar ta NIWA, Bola Oyebamiji, ne tuni ya riga ya bayar da kwangilar yin aikin, ba wai a jihar Legas kawai ba, har da a sauran hanyoyin ruwa da ke a sassan kasar.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA