Ousmane Dembele zai buga wasan PSG da Bayern Munich
Published: 4th, November 2025 GMT
Dan wasan gaban Paris Saint-Germain (PSG) ɗan asalin ƙasar Faransa, Ousmane Dembele, zai kasance cikin tawagar da za ta fafata da Bayern Munich a wasan Champions League da za a buga yau Talata.
Dembele, wanda ya zura ƙwallo a wasan da PSG ta doke Bayern Munich da ci 2–0 a gasar Club World Cup zagaye na kwata-final a watan Yuli, bayan mako guda ya fice daga wasa sakamakon jin ciwo a cinyarsa ta dama a fafatawar da suka yi da Lorient.
Kocin PSG, Luis Enrique, ya tabbatar da cewa dan wasan ya murmure daga raunin kuma zai iya buga wasan yau.
“Dembele yana cikin ƙoshin lafiya, ya koma atisaye cike da karsashi, kuma zai kasance cikin jerin ‘yan wasan da za su buga wasan da Bayern,” in ji Enrique.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Bayern Munich
এছাড়াও পড়ুন:
Karuwanci da zubar da cikin ’yan mata ’yan gudun hijira ya karu a Maiduguri
Sarakunan gargajiya, lauyoyi da jami’an gwamnati sun koka bisa yawaitar kananan ’yan mata da ke daukar ciki da kuma zubar da ciki ba bisa ƙa’ida ba, a sansanonin ’yan gudun hijira da ke Maiduguri, Jihar Borno.
Lamarin ya fito fili ne a wani taron tattaunawa na kwanaki biyu da ƙungiyar Grassroots Researchers Association (GRA) ta shirya tare da tallafin We Are Not Weapons of War (WWoW) a karshen makon da ya gabata a Maiduguri.
Taron ya haɗa mutane fiye da 500, ciki har da waɗanda suka tsira daga fyade da cin zarafi a lokacin rikici, sarakunan gargajiya, lauyoyi, jami’an gwamnati da abokan ci gaban ƙasa, domin tattauna hanyoyin magance wannan matsala.
“’Yan mata kanana na sayar da jikinsu, suna kuma zubar da ciki a bandaki,” in ji wata mai taimaka wa GRA, Zaynab Abdallah.
NAJERIYA A YAU: Rashin aikin yi da hanyoyin magance su a Najeriya Gidan rediyo ya ɗauki nauyin sanya yara 40 a makaranta a KanoShugaban sansanin ’yan gudun hijira na EYN Jerusalem da ke unguwar Wulari a Maiduguri, Mista John Gwoma, ya bayyana yadda kananan ’yan mata da ƙananan yara ke fadawa tarkon lalata da kuma zubar da ciki a asirce.
Ya ce, “Wasu maza daga cikin gari kan zo cikin manyan motoci su ɗauki waɗannan ’yan mata ƙanana, su yi lalata da su har su sami ciki. Saboda haka yanzu zubar da ciki ba bisa ƙa’ida ba ya zama ruwan dare a sansanin.”
Ya ƙara da cewa, “Bandakunan mata sun koma kamar mayanka. Ana samun jini ko’ina saboda waɗannan ’yan matan na shiga su zubar da ciki sannan su bar tayin a ciki. Wasu iyaye na sane da abin da ’ya’yansu ke yi”
Wata mai taimaka wa GRA, Zaynab Abdallah, ta tabbatar da wannan zargi, tana mai cewa karuwanci da kuma zubar da ciki tsakanin ƙananan yara na ƙara yaduwa a Maiduguri.
Ta ce, “Wasu daga cikin waɗannan ’yan mata ƙanana suna lalata ne domin samun kuɗin abinci ga iyalansu. Amma abin takaici, wasu iyaye suna sane da hakan, amma suna yi shiru saboda suna amfana da abin da ’ya’yansu ke samu.”
Zaynab ta ci gaba da cewa, “Talauci ya kai ga karuwanci ya zama tamkar wani ɓangare na rayuwarsu. Ba za ka iya hana su ba. Idan sun sami ciki, sai su zubar da shi a ɓoye domin guje wa tozarci.”
Rikici da talauci sun kai mata ga lalacewa”A yayin zaman, waɗanda suka tsira daga fyade da sauran masu ruwa da tsaki sun ruwaito irin raɗaɗin da suka sha na fyade, da kuma yadda matsin tattalin arziki ke tura mata cikin harkar karuwanci.
Sai dai sun kuma bayyana yadda gangamin wayar da kai na GRA ya taimaka wajen rage tozarci da suka sha, tare da ƙara musu ƙarfin guiwa wajen neman adalci a kotuna.
Daraktan gudanarwa na ƙungiyar GRA, Mista Friday Bitrus, ya ce sakamakon tattaunawar da suka samu daga mahalarta zai zama ginshiƙi wajen fitar da takardar “Kira ga Daukar Mataki” domin tursasa gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki su ɗauki matakai na gaskiya.
Ya ce, “Abin da muka tattara daga bakin waɗanda abin ya shafa da sauran mahalarta ya nuna cewa akwai gaggawar buƙatar tsari na musamman don kare ’yan mata da mata daga fyade, ciki da kuma zubar da ciki a sansanonin.”
Kira ga gwamnatiMasu ruwa da tsaki a taron sun yi kira ga gwamnati ta ƙara tsaurara matakai wajen tsaron sansanonin, ta samar da abinci da kayan masarufi, da kuma hanyoyin koyar da sana’o’in dogaro da kai ga ’yan gudun hijira — musamman mata da matasa.
Sun kuma bukaci a hukunta duk wanda aka kama da laifin lalata da yara a sansanonin, tare da samar da ingantattun cibiyoyin kula da lafiya domin dakile zubar da ciki ba bisa ƙa’ida ba.
A cewar wani mahalarcin taron, “Wannan matsala ba wai ta Borno ce kawai ba, tana iya bazuwa zuwa sauran jihohi idan ba a ɗauki mataki cikin gaggawa ba.”
Taron ya ƙare da amincewa da kafa kwamitin bin diddigi domin tabbatar da cewa an aiwatar da shawarwarin da aka cimma.