Sin Ta Yi Kira Da A Ci Gaba Da Himmatuwa Wajen Warware Batun Ukraine Ta Hanyar Lumana
Published: 26th, July 2025 GMT
Ya ce, a cikin mako guda, Amurka ta yi zarge-zarge da dama marasa tushe kan kasar Sin, a lokutan zaman kwamitin tsaron MDD, wanda hakan ya shaida cewa, burinta ba wai na ganin an wanzar da zaman lafiya da tsaro, ko yayata bukatar warware rigingimu, ko kawo karshen yaki ba ne, maimakon haka, Amurka na amfani da dandalin kwamitin tsaron ne wajen kaiwa wasu sassa hari, ko yunkurin dakile ci gabansu, tare da amfani da dabarun siyasa don cimma burikanta na kashin kai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Faransa Ta Saki Dan GWagwarmayar Kasar Lebanon Goerge Abdullah Ya Bayan Zaman Kurkuku Na Shekaru 41
A jiya Juma’a ne dai wanda ya isa birnin Beirut ya yi kira ga al’ummar kasar da su yi riko da hadin kan kasa da dukkanin bangarorinsu, sannan kuma su ci gaba da zage damtse wajen kalubalantar makiyar kasar Lebanon,musamman ‘yan sahayoniya.
Goerge Ibrahim Abdullah wanda kuma ya gabatar da taron manema labaru a garinsu na “Qubyat’ ya kara da cewa; Kamar yadda mu ka kasance garkuwa mai bayar da kariya ga kasa, za mu ci gaba da zama haka’ sannan kuma ya kara da cewa: Saboda jinanen Shahidai kasar Lebanon za ta iya kalubalantar dukkanin hatsurran da take fuskanta.”
Har ila yau, ya bayyana cewa;sojojin kasar Lebanon suna da mazajen da za su iya kare kasa,illa iyaka abinda ya rage su, shi ne makamai.”
Akan mahaifarsa Gubyat, Goege Abdullah ya ce, a tsawon lokacin garin ya kasance wani alami na hadin kan al’ummar kasar.”
A filin saukar jiragen sama na “Rafiqul-Hariri” dake birnin Beirut, Goerge Ibrahim Abdullah ya sami kyakkyawar tarba daga ‘yan majalisa da jam’iyyun siyasa da kuma mutanen gari da dama.
A takaitaccen bayanin da ya yi a filin saukar jiragen saman na Beirut, ya sake tabbatar da matsayarsa na ci gaba da riko da gwgawarmaya da goyon bayan al’ummar Falasdinu.
Har ila yau ya ce; Matukar akwai gwagwarmaya, to da za a koma cikin kasa, sannan kuma ya ce; Gwagwarmaya tana nan da karfinta, ba ta yi rauni ba.”