HausaTv:
2025-07-27@04:19:20 GMT

Musulmi A Amurka Sun Fara Daukar Matakan Tsaro A Masallatai Saboda Makiya

Published: 26th, July 2025 GMT

Shuwagabannin kungiyoyin musulmi a kasar Amurka sun fara daukar matakan tsaro a masallatai da wuraren taro da kuma makarantun musulci saboda yawan samun wasu magoya bayan yahudawa suna yawaita shiga irin wadannan wurare suna lalatasu.

Shafin yanar gizo na labarai ‘ArabaNews” ya bayyana cewa a jihohin Texas da Califonia, masu goyon bayan yahudawan sun lalata masallatai da dama sun kuma sace abubuwa da dama a cikinsu.

Edward Ahmed Mitchell, mataimakin sakataren kungiyar ‘ Council on American-Islamic Relations’ wata kungiyar kare hakkin musulmi a Amurka ya shaidawa Arabnew kan cewa tun bayan fara yaki a Gaza shekaru kimani biyu da suka gabata, musulmi a Amurka suka fara fuskantar sabon kiyayya daga wadanda basa son musulmi a kasar.

Edword yace abu mafi muni da ya faru a cikin kimani shekaru biyu da suka gabata, shi ne ind wani, mutum ya bindige wani yaro dan shekara 6 a duniya, bafalasdine musulmi ya kuma jiwa mahaifiyar yaron rauni.

Yace wadannan shekaru biyu sun yiwa musulmi a Amurka wahala. Musamman idan sun hadu da maso goyon bayan yahudawa a kasar.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Musuluntar Wata Ce Ya Ja Hankalina Shiga Fim – Sailuba Dadin Kowa

Masu karatu za su so jin dan takaitaccen tarihinki?

An haife ni a garin Gombe, amma sai daga bisani na bar garin Gomben da zama na dawo Kano, tun ina ‘yar shekara biyar da haihuwa, sakamakon mahaifina yana aiki a Kanon. Kazalika, na girma a gaban iyayena, na yi firamare da sakandare duk a garin Kano, sannan kuma ban taba yin aure ba; budurwa ce ni.

 

Wace irin rawa kike takawa a cikin masana’antar shirya finafinai ta Kannywood?

Ina fitowa ne a matsayin Jaruma kawai, amma kuma ina da niyyar zama mai bayar da umarni a nan gaba kadan insha Allah.

 

Me ya ja hankalinki, har kika tsunduma harkar fim?

Wato batu na gaskiya, fim yana burge ni kwarai da gaske, amma dalilin shigata sana’ar ita ce; wani fim aka yi sai wata arniyya ta musulunta, daga nan ne na ce; in dai har fim yana isar da sako, har ya zama silar gyaruwar al’umma, gaskiya zan zama daya daga cikin wadanda za su isar da wannan sako, tunda da ma raina yana so matuka gaya.

 

Ya gwagwarmayar shiga masana’antar ta kasance?

Gaskiya ni ban sha wahala ba, dalili kuwa shi ne; dan fim ne ya sa ni a harkar ta fim, sannan kuma kamar yaya yake a wajena, dan Unguwarmu ne, iyayena da nasa sun zama kamar ‘yan’uwa.

 

Lokacin da kika fara sanar wa iyayenki cewa, kina son shiga harkar fim, wane kalubale da kika fuskanta daga wurinsu? 

Eh! Gaskiya na fuskanci kalubale, amma daga baya sun fahimce ni, sakamakon iyayen nawa masu fahimta ne.

 

Za ki yi kamar shekara nawa da fara fim?

Ina ga zan samu kamar shekara takwas da farawa.

 

Ya farkon fara dora miki Kyamara ya kasance?

Ban ji tsoron komai ba, kuma Alhamdulillahi na samu yabo sosai daga wajen masu bayar da umarni da sauran abokan aiki.

 

Wane fim kika fara yi a farkon zuwanki?

Na fara ne da fim din Dadin Kowa.

 

Wace rawa kika taka a cikin shirin na Dadin Kowa?

Na fito ne matsayin Sailuba, inda na taka rawa a matsayin matar aure. Surukata ce ta auro wa mijina ni a kauye, saboda ba ta son matar dan nata da aura, sakamakon cewa; Beyerabiya ce, wato maman Rasaki kenan, ni kuma a nan na yi ta tsula tsiyata.

 

Bayan da aka fara haska fuskarki cikin shirin Dadin Kowa, ya kika ji a lokacin, sannan kuma yaya kika kasance da mutanen Unguwarku da sauran ‘yan’uwa?

Alhamdulillah! Wadanda suka san ni a gaske, sun biyo ni har gida suna kallona kamar a da ba su san ni ba, wadanda kuma ba su san ni ba, idan muka hadu abin ba dama, ga tarin alhairai daga masoya daga gurare daban-daban.

 

Bayan shirin Dadin Kowa da kika fito a ciki, ko akwai wasu fina-finan da kika fito ciki?

Eh, na yi wasu fina-finan da dama.

 

Kamar wadanne kenan?

Kamar irin su: Ni da Mijin Yayata, Matar Waye, Zaman Tare, Matar Kaddara da dai sauransu, dukkanninsu masu masu dogon zango ne kuma ni ce jarumar ciki.

 

Cikin wadannan fina-finai da kika zayyano, wane fim ne ya fi burge ki, kuma me yasa, sannan wace rawa kika taka a cikin shirin?

Ni da mijin Yayata, na fito ne a matsayin budurwa wacce take matukar son mijin yayarta.

 

Ya kika ji a lokacin da za ki taka rawa a wannan shirin?

Na ji dadi sosai, saboda zan yi abin da nake so; sannan kuma an kara min kwarin gwiwa, har muka yi muka gama babu wata matsala.

 

Ya batun masu kallo bayan shirin ya fita, ko kin samu wani kalubale daga gare su?

A a, kawai dai idan aka gan ni a zahiri, a kan yi mamaki tare da bayyana cewa; na fi kyau a fili, wasu ma har su ce ba su yi zaton cewa; ‘yar birni ba ce ni, sun yi zaton yadda nake ‘yar kauye a Dadin Kowa, a gaske ma haka nake.

 

A fina-finan da kika yi, wane fim ne ya fi haska ki; har mutane suke iya gane ki?

Dadin Kowa, sai kuma wannan fim din na Matar Waye, shi ma ba abin da zan ce gaskiya.

 

Ko akwai wani kalubale da kika taba fuskanta, tun daga farkon zuwanki cikin masana’antar zuwa yanzu?

Gaskiya an samu, amma a da ne; yanzu cikin ikon Allah an samu daidaito.

 

Wadane irin nasarori kika samu game da fim?

Akwai nasarori da dama kamar ta fuskar samun kudi, mota, kayan sakawa, turaruka da sauran makamantansu.

 

Ko kina da ubangida a masana’antar Kannywood?

Kwarai da gaske ina da su, akwai Adam Musa Adam da kuma Usman Adam Hali Dubu.

 

Kafin ki fara fim, wadane jarumai ne suka fi burge ki har kike jin dama ki zama tamkar su?

Ina kowace jaruma, domin kuwa dukkaninsu suna burge ni.

 

Yaushe kike sa ran yin aure?

Duk lokacin da Allah ya kawo shi, a shirye nake.

 

Ko akwai wanda ya taba cewa yana son ki zai aure ki a masana’antar?

Kwarai da gaske, akwai.

 

Ko za mu iya jin sunansa?

A’a gaskiya.

 

Mene ne ra’ayinki game da auren dan fim?

Zan iya aurensa mana, ai babu wata matsala a ciki.

 

Wane irin namiji kike so ki aura?

Ya kasance Musulmi, mai ilimi, wanda kuma yake da cikakkiyar sana’a.

 

Wace shawara za ki bai wa abokan aikinki na masana’antar Kannywood?

Da farko dai, ya kamata mu hada kanmu, sannan mu kiyaye abin da zai bata sunan sana’ar tamu, mu kuma yi kokari wajen kare mutuncinmu, wannan shi ne a takaice.

 

Wacce shawara za ki bawa masu kokarin shigowa wannan masana’anta?

Su tabbata sun shigo da niyya mai kyau, sannan kuma su yarda cewa; sana’a suka zo yi, ba wani abu daban ba.

 

Ko kina da wadanda za ki gaisar?

Ina fatan alhairi ga kowa da kowa, musamman masoyana.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Musuluntar Wata Ce Ya Ja Hankalina Shiga Fim – Sailuba Dadin Kowa
  • Burtaniya Zata Fara Jefawa Falasdinawa Abinci Daga Sama
  • Faransa Ta Saki Dan GWagwarmayar Kasar Lebanon Goerge Abdullah Ya Bayan Zaman Kurkuku Na Shekaru 41
  • Yawan Mutanen Da Suka Rayukansu A Rikicin Lardin Suwaida Na Kasar Siriya Ya Kai 1,400
  • Iran Da Eu Sun Fara Tattaunawa A Istambul
  • An Watse A Taron EU Da China Saboda Ricikin Kasuwanci Da Siyasa  Tsakaninsu
  • Iran da Bangladesh sun bukaci taron gaggawa na OIC kan kisan kiyashi a Gaza
  • An Fara Binciken Bidiyon Ciyar Da Sojoji Garaugarau
  • Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya Ya Fara Tattaunawa kan Masifar Zirin Gaza Na Falasdinu