Leadership News Hausa:
2025-11-04@21:11:44 GMT

Li Qiang Ya Zanta Da Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya

Published: 4th, November 2025 GMT

Li Qiang Ya Zanta Da Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya

A yau Talata ne firaministan Sin Li Qiang, ya gana da kakakin majalisar wakilan tarayyar Najeriya Tajudeen Abbas, wanda ya isa birnin Shanghai don halartar baje kolin CIIE karo na takwas.

Yayin zantawarsu, Li Qiang ya bayyana aniyar kasar Sin ta karfafa salon wanzar da ci gaba bisa manyan tsare-tsare tare da Najeriya, da zage damtse wajen aiwatar da wasu muhimman matakai goma na bunkasa kawance tsakanin Sin da kasashen nahiyar Afirka, da hada hannu wajen gina shawarar “Zira Daya Da Hanya Daya” mai inganci, da bunkasa matakin hadin gwiwa a sassan gargajiya, da fadada hadin gwiwa a sabbin masana’antu, da kara kyautata gina tattalin arziki da zamantakewar al’ummun sassan biyu.

Li Qiang ya kara da cewa, akwai bukatar kasashen biyu su karfafa tsare-tsare, da hadin gwiwa a fannin gudanar da cudanyar mabambantan sassa, karkashin irinsu hadakar kasashen BRICS, da MDD, da yayata hadin kai, da inganta karfin kasashe masu tasowa.

A nasa tsokacin, Tajudeen Abbas ya ce Najeriya na rike da manufar nan ta Sin daya tak a duniya, kuma a shirye take ta karfafa musayar kwarewar jagoranci tare da Sin, da fadada hadin gwiwa a sassa da dama, kamar tattalin arziki da cinikayya, da samar da ababen more rayuwa, da makamashi, da al’adu, tare da ci gaba da daga cikakkiyar dangantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Najeriya da Sin zuwa babban matsayi. (Saminu Alhassan)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Tsohon Jami’in Diflomasiyyar Nijar: Baje Kolin CIIE Muhimmin Dandali Ne Na Bunkasa Hadin Gwiwa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa November 4, 2025 Daga Birnin Sin Shugaban Xi Ya Gana Da Firaministan Rasha November 4, 2025 Daga Birnin Sin Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin November 3, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: hadin gwiwa a

এছাড়াও পড়ুন:

Majalisar Kaduna Ta Amince da Dokar Kafa Hukumar Fasahar Sadarwa da Tattalin Arzikin na Zamani

Daga Shamsuddeen Mannir Atiku 

Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta amince da dokar kafa Hukumar Fasahar Sadarwa da Tattalin Arzikin na Zamani ta Jihar Kaduna, wacce za ta taimaka wajen ƙarfafa tsarin fasaha na jihar da inganta gasa a fannin tattalin arziki.

Dokar mai taken “Kaduna State Information Technology and Digital Economy Agency and for Related Matters, 2025” ta samu amincewa bayan karatu na uku a zaman majalisar na ranar Talata.

Shugaban majalisar, Hon. Yusuf Dahiru Liman, wanda ya jagoranci zaman, ya bayyana muhimmancin dokar, yana mai cewa kafa hukumar zai faɗaɗa damar tattalin arziki tare da bai wa jihar Kaduna damar cin moriyar cigaban fasahar zamani a duniya.

Ya ce hukumar za ta ƙarfafa kirkire-kirkire, bunƙasa ƙwarewar dijital, da daidaita jihar da sauye-sauyen fasaha da tattalin arzikin dijital a duniya.

Tun da farko, shugaban kwamitin haɗin gwiwa kan Yada Labarai, Kungiyoyi Masu Zaman Kansu da Abokan Cigaba, Mr. Henry Marah Zakariah, ya gabatar da rahoton kwamitin.

Ya bayyana cewa an yi nazari mai zurfi kan dokar, kuma an tabbatar da cewa mataki ne mai muhimmanci wajen ƙara damar samun ayyukan yi da sauƙaƙa wa al’umma samun ilimin fasahar zamani.

Mr. Henry Zakariah ya kuma jaddada cewa kafa hukumar za ta bunƙasa tattalin arzikin jihar da samar da kudaden shiga, inda ya bayyana cewa za a kafa cibiyoyin fasahar zamanin a yankunan karkara domin bai wa kowa damar cin gajiyar ayyukan Hukumar.

Daga karshe majalisar ta amince da dokar baki ɗaya, bayan Dan Majalisa mai wakiltar mazabar Birnin Zaria, Barr. Mahmood Lawal Sama’ila ya gabatar da kudirin amincewa inda ya samu goyon baya daga Dan Majalisa mai wakiltar mazabar Makarfi, Isiyaku Ibrahim ya goyi bayan shi.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ‘Yan Sama Jannatin Kumbon Shenzhou-20 Za Su Dawo Doron Kasa A Gobe Laraba
  • Majalisar Kaduna Ta Amince da Dokar Kafa Hukumar Fasahar Sadarwa da Tattalin Arzikin na Zamani
  • ’Yan kwangila sun hana zaman majalisa kan rashin biyan haƙƙoƙinsu
  • Kakakin Majalisar Dokokin Lebanon Ya Jaddada Gagarumin Tsaron Kasa Da Gwagwarmaya Ta Baiwa Lebanon
  • Shugaban Xi Ya Gana Da Firaministan Rasha
  • Shugabannin Wasu Kasashe Za Su Halarci Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas A Birnin Shanghai
  • Li Qiang Zai Halarci Bikin Bude Taron CIIE Na 8 Da Sauran Ayyuka
  • El-Zakzaki: Yakin Sudan Yana Kare Maslahar Kasashen Yamma ne Kawai
  • Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik