Leadership News Hausa:
2025-11-04@18:54:38 GMT

Zulum Ya Raba Motocin Sintiri 63 Ga Hukumomin Tsaro A Borno

Published: 4th, November 2025 GMT

Zulum Ya Raba Motocin Sintiri 63 Ga Hukumomin Tsaro A Borno

 

Yayin da yake gabatar da motocin, Gwamna Zulum ya sake nanata kudirin gwamnatinsa na samar da tallafin kayayyaki ga jami’an tsaro a kowane lokaci. Ya jaddada cewa, tsaro wani bangare ne na muhimman abubuwan da gwamnatinsa ta sa a gaba.

 

Zulum ya kuma yaba wa Shugaba Bola Tinubu da jami’an tsaro kan kokarin da suke yi na dawo da zaman lafiya a Borno.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai China Ta Gargaɗi Amurka Kan Tsoma Baki A Harkokin Nijeriya November 4, 2025 Manyan Labarai Atiku Ya Fice Daga PDP Saboda Na Ƙi Bari Ya Lalata Mana Jam’iyya – Wike November 4, 2025 Manyan Labarai Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi  November 4, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Sojoji Sun Kashe Ƴan Bindiga 19, Sun Ƙwato Makamai A Kano

Sojojin haɗin gwuiwa ta Operation MESA ƙarƙashin Birgediya ta 3 sun kashe ƴan bindiga 19 a ƙaramar hukumar Shanono ta jihar Kano, bayan wata musayar wuta mai tsanani da ta faru a yankunan Unguwan Tudu, Unguwan Tsamiya, da Goron Dutse da misalin ƙarfe 5:00 na yamma ranar Asabar. Wannan sumame ya biyo bayan sahihan bayanan leƙen asiri kan motsin wasu ƴan ta’adda da suka shiga yankin daga maƙwabtan dazuka.

A cewar sanarwar Kyaftin Babatunde Zubairu, Mataimakin Daraktan hulɗa da Jama’a na Birgediya ta 3, Sojojin tare da jami’an tsaro sun fatattaki ƴan ta’addan bayan musayar wuta, inda aka kashe ƴan bindiga 19, yayin da wasu suka gudu da raunin harbi. Ya ce an ƙwato babura da dama da kuma wayoyi guda biyu da aka samu a wajensu.

Mayar Da Martani Kan Barazanar Amurka Ga Nijeriya: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yaba Wa Kwankwaso  Kano Ta Amince Da Naira Biliyan 8.2 Don Ayyukan ilimi, Samar Da Ruwa, Da Makamashi

Sai dai, Sojoji biyu da jami’in sa-kai ɗaya sun rasa rayukansu yayin arta. Kyaftin Zubairu ya bayyana cewa sadaukarwar su hujja ce ta kishin ƙasa da jajircewar rundunar wajen kare ƴan Nijeriya da kawar da barazanar ta’addanci a yankin.

Kwamandan Brigade ta 3, Brigediya Janar Ahmed Tukur, ya yaba wa dakarun bisa jarumtarsu, yana mai tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da gudanar da aikace-aikacen tsabtace yankin domin hana ramuwar gayya da kare al’ummomin da ake yawan kai wa hare-hare. Ya kuma shawarci mazauna yankin da su ci gaba da lura da duk wani motsi na baƙuwar fuska da ba a saba gani ba tare da sanar da jami’an tsaro cikin lokaci.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Mayar Da Martani Kan Barazanar Amurka Ga Nijeriya: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yaba Wa Kwankwaso  November 3, 2025 Manyan Labarai Kano Ta Amince Da Naira Biliyan 8.2 Don Ayyukan ilimi, Samar Da Ruwa, Da Makamashi November 3, 2025 Manyan Labarai Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya November 2, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi 
  • Natasha Ta Zargi Akpabio Da Sanya Jami’an Tsaro Su Ƙwace Mata Fasfo A Filin Jirgin Saman Abuja 
  • Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo
  • Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump 
  • Abba ya umarci a riƙa gudanar da taron tsaro a ƙananan hukumomin Kano
  • Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya Bisa Dalilan Tsaro
  • Sojoji Sun Kashe Ƴan Bindiga 19, Sun Ƙwato Makamai A Kano
  • Tsaro: Taimakonmu Amurka ya kamata ta yi maimakon barazana — Kwankwaso
  • Tsaro: Taimakonmu Amurka ya kamata ta yi maimakon ba barazana ba — Kwankwaso