Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-11-04@04:20:12 GMT

Gwamna Namadi Ya Yaba Da Tasirin Shirin NG-CARES A Jihar Jigawa

Published: 4th, November 2025 GMT

Gwamna Namadi Ya Yaba Da Tasirin Shirin NG-CARES A Jihar Jigawa

Daga Usman Muhammad Zaria

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na fadada ayyukan ci gaban karkara, tare da aiwatar da shirye-shiryen da za su inganta rayuwar al’umma.

Gwamnan ya bayyana haka ne lokacin da ya karɓi bakuncin jami’in kula da shirin rage radadin illar da annobar cutar Korona ta haifar, wato (NG-CARES), Dakta Abdulkareem Obaje, wanda ya kai masa ziyara ta ban girma a Dutse.

Dakta Obaje ya yaba wa gwamnan da gwamnatin jihar Jigawa bisa goyon bayan da suke bai wa shirin NG-CARES tun daga lokacin da aka ƙaddamar da shi a shekarar 2021.

Ya bayyana cewa an kirkiro shirin ne a shekarar 2020 sakamakon tasirin annobar COVID-19, domin taimaka wa jihohi su farfaɗo da tattalin arziƙin karkara da tallafa wa marasa ƙarfi.

“Shirin NG-CARES ya kai shekaru huɗu yana gudana, kuma mun biya jihohi kuɗaɗe har zuwa dala miliyan 696, inda aka taimaka wa  mutane kusan miliyan 70 a fadin ƙasar nan.” In ji Dakta Obaje.

Ya ƙara da cewa shirin, wanda ya fara da jimillar dala miliyan 750, ya ba da dama ga jihohi irin su Jigawa su taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da ayyuka da suka taɓa rayuwar jama’a kai tsaye.

Dakta Obaje ya kuma bayyana cewa sabon zagaye na shirin, NG-CARES 2.0, zai fara aiki  nan ba da jimawa ba.

A nasa jawabin, Gwamna Namadi ya gode wa tawagar NG-CARES bisa ziyarar da suka kai masa, tare da bayyana shirin a matsayin ɗaya daga cikin manyan shirye-shiryen da suka fi tasiri wajen kai tallafi kai tsaye ga al’umma mafi ƙaranci a Jihar Jigawa.

“NG-CARES shi ne shirin da ya fi taɓa rayuwar jama’armu kai tsaye.” In ji shi.

Ya tunatar da yadda ya yi ƙoƙari wajen ganin an ci gaba da aiwatar da shirin a matakin Majalisar Gwamnonin Najeriya (NGF) da kuma Babban Bankin Duniya (World Bank).

“Ina iya cewa ba tare da wata shakka ba, NG-CARES 2.0 ra’ayinmu ne, domin mu ne muka nemi a ci gaba da shirin.” In ji Gwamna Namadi.

Gwamnan ya kuma yi alkawarin cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da tallafa wa shirin domin ƙarfafa hanyoyin kyautata rayuwa da kuma inganta tsaron zamantakewa a tsakanin jama’a.

Ziyarar ta kasance wani ɓangare ne na zagayen da ofishin NG-CARES ke yi a fadin ƙasa domin tattara rahotanni, jin ra’ayoyin jama’a, da kuma nuna nasarorin da aka samu yayin da ake shirin kaddamar da NG-CARES 2.0.

 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Jigawa NG CARES

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamna Uba Sani Ya Bayyana Tsare-tsaren Ci Gaban Kaduna a Taron Duniya a Dubai.

Daga Abdullahi Shettima

Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya wakilci Nijeriya a taron ƙoli na biranen Asiya da ya gudana a ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), inda ya gabatar da kudirorin sauyin ci gaban Kaduna.

Taron ya samu halartar manyan baki daga ƙasashe sama da 150, ciki har da gwamnoni, shugabannin birane da jagororin kasuwanci daga Asiya, Fasifik, Turai da Afirka. Taken taron shi ne “Haɗin Gwiwa. Ƙarfafawa. Sauyi.”

A jawabinsa mai taken “Gina Haɗin Gwiwa Domin Ci Gaban Kowa,” Gwamna Uba Sani ya bayyana yadda Kaduna ke samun nasara a fannoni da dama kamar gyaran birane, bunƙasa noma da tallafawa jama’a. Ya ce tsarin ci gaban jihar yana dogara ne kan faɗaɗa damar tattalin arziki, kare marasa ƙarfi, da ƙarfafa jama’a su cim ma nasara a rayuwarsu.

Haka kuma, ya halarci baje kolin birnin Dubai mai taken “Sauya Arewa a Nijeriya: Jagoranci, Ƙirƙira da Tasirin Zamantakewa,” inda ya jaddada muhimmancin jagoranci mai nagarta da amfani da fasaha wajen buɗe damarmaki ga al’umma.

A yayin taron, Gwamnan ya gudanar da ganawa ta musamman da Marwan Bin Galita, Darakta-Janar na birnin Dubai, inda suka tattauna batutuwan kirkirar makamashin sharar gida, kula da sharar zamani, da tsare-tsaren gine-ginen birane na zamani.

Duk ɓangarorin biyu sun amince da zurfafa haɗin kai a fannin fasaha da musayar ƙwarewa domin tallafawa sauyin tattalin arzikin Kaduna zuwa mai ɗorewa.

Gwamna Sani ya bayyana cewa halartar Kaduna a taron (APCS 2025) na nuna shirin jihar na shiga sahun gaba wajen yin haɗin kai, ƙirƙira da zama abin koyi a fannin ci gaba mai ɗorewa — a Najeriya da duniya baki ɗaya.

Karshe.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Uwargidan Gwamnan  Zamfara Ta Yaba Wa  Karamar Hukumar Gusau Bisa Shirin Tallafawa Jama’a
  • Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Yabawa Gwamna Namadi Bisa Ayyukan Hanyoyi A Fadin Jihar
  • Trump ya jaddada shirin Amurka na kai hari a Najeriya
  • 2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su
  • Gidauniyar IRM Da KADCHMA, Ta Ƙaddamar Da Inshorar Lafiya Kyauta Ga Mutane 200 A Kaduna
  • Muna shirin kai farmaki a Nijeriya — Ma’aikatar Yaƙin Amurka
  • Gwamna Uba Sani Ya Bayyana Tsare-tsaren Ci Gaban Kaduna a Taron Duniya a Dubai.
  • Gwamna Namadi Ya Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
  • Gwamnatin Jigawa Ta Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda