Natijojin Auren Dattijo Ga Budurwa
Published: 26th, July 2025 GMT
Sunana Yasar Sale Zareku Miga A Jihar Jigawa:
Gaskiya aurar da yarinya ga mutum mai shekaru ya fi, dan shi zai fi kula da hakkinta ya san rayuwa, ni ban ga wata matsala ba dan mace ta auri mutum mai shekaru. Shawarata shi ne iyaye su san wanda ya kamata su aurawa ‘ya’yansu, domin aure muhimmin al’amari ne da ya kamata a zurfafa bincike kafin a gudanar, domin gudun yin kitso da kwarkwata daga karshe nake addu’ar Allah ya bawa mata miji nagari su ma mazan Allah ya ba su mata nagari.
Sunana Rahama Bashir daga Jihar Katsina:
Ni a gani na auren namijin da ya girmeka ya fi musamman idan shekarun da yawa, sabida kar ku tsufa tare, amma idan namiji shekararku tazarar ba yawa za ku tsufa tare karshe ya fara ganin kin yi masa tsufa bari ya nemo karamar yarinya, amma idan ya baki shekaru da yawa kamar goma ko goma sha ko ashirin to, zai ta ganinki a yarinya komai ki ka yi kuruciya ne sabida ya wuce wajen ke kuma yanzu ki ke zuwa, tunanin ma ya auro yarinya ba zai yi ba tunda bai gama da naki kuruciyar ba.
Sunana Ibrahim Garba Bizi Daga Damaturu, Jihar Yobe:
Wannan batu shi yafi dacewa a yi mata aure da wanda ya fita shekaru, ba rashin amfani sai dai amfano, in ta auri sa’anta ko wanda ya fita da shekara 1 ko 2 za ta tsufa ta bar shi, amma in ta auri wanda ya fita shi ne wanda tafiyar za ta wanye lafiya. Ba wata masala da za ta haifar face ta haifar da maslaha. Su daure su cije su bawa wanda suka ga ya cancanta ba sai mai dukiya ba ko mai azuki ba, yawanci ana ba masu manyan shekaru yara kananu saboda arzikinsu.
Sunana Aisha T. Bello daga Jihar Kaduna:
Wasu iyayen kwadayi ne ke kai wa da haka kuma irin haka na jawo matsala irin-irin mussaman ga yarinya karama cutarwa ce babba, wata daga gun haihuwa ake samun matsala. Gaskiya nafi ganin kwadayi ne kawai, saboda da tsoho ya zo neman aure in yana da kudi kawai sai a bashi saboda na ga irin wannan da yawa gaskiya. Eh to matsala in yana da yara manya to za ka ga abubuwa irin gaskiya sai dai ki ta hakuri. Shawara ta a nan ita ce kowace mata a duniya Allah ya tsara mata rayuwar ta na daniya to, dan Allah iyaye mu bi zabin Allah shi ne mafita Allah ya sa mu dace.
Sunana Muktari Sabo Jahun Jihar Jigawa:
Eh gaskiya yi wa yarinya aure da wanda ya fita shekaru ba wani abu bane matukar dai tana sonsa don hakan ya sha faruwa, kuma ba wata matsala inda matsalar take dai kawai shi ne in ba ta so. Amfanin yi wa yarinya aure da wuri yana da yawa musamman a wannan zamani namu zai taimaka wajen samar wa yarinya da iyayenta kwanciyar hankali. Maganar mijin da ya fi ta shekaru kuwa indai mutumin kirki ne zai kula da hakkinta ai ba matsala bane domin an yi da yawa. Matsala kawai za ta faru ne idan dama dole aka yi mata ko kuma wata bukata aka yi amfani da ita don biyan bukatar. Shawara a nan ita ce iyaye su aurawa ‘ya’yansu mutanen kirki koda kuwa ba masu kudi bane kuma su tabbatar ba su yi musu dole ba.
Sunana Abba Abubakar Yakubu, daga Jos:
Ban ga laifin auren mai shekaru ba.
A ganina babu laifi don karamar yarinya matashiya ta auri wanda ya girme ta, saboda dama bisa dabi’ar halittar mace, ba ta iya zama da wanda suke daidai a shekaru ko kusa da haka. Saboda tana iya fin sa wayo, hikima da dabarar sanin rayuwa. To, shi kuma aure, musamman karkashin koyarwar addini, wanda ya karfafa namiji a kan mace, ana bukatar namijin da zai auri mace, ya kula da rayuwarta, tarbiyyarta da addininta. Duk da kasancewar addini bai hana irin wannan aure da ake samun tazarar shekaru tsakanin miji da mata ba, amma kuma ba uzuri ba ne a aurar da karamar yarinyar da ba ta yi wayo sosai ba, ko kuma jikinta bai rika sosai ba, ga mutumin da yake dattijo mai yawan shekaru ko wanda ba shi da isasshiyar lafiya. Yana da kyau iyaye su rika la’akari da yanayin shekarun yarinya, yanayin cikar halittar ta da kuma wayewarta, kafin su aurar da ita ga wanda zai iya cutar da rayuwarta. Harwayau, kuma ina so in ja hankalin ‘yan mata da su yi la’akari da halayyar wanda suke so, addininsa da sana’arsa ko aikinsa, don ganin ya dace da irin mijin da suke so su aura, ba tare da lura da shekarun sa ba. Matukar mutum yana da halayen kwarai da za ta iya zama da shi a matsayin mijin aure, ina ganin ba sai shekarunta da nasa sun zama daya ba, ko ya zama tazararsu ba ta da yawa ba.
Sunana Comr. Nr. Ibrahim Lawan Stk Sule Tankarkar Jihar Jigawa:
Maganar aure tsakanin yarinya da mutumin da ya manyanta wannan ba wani sabon abu bane ba kuma abu ne da bai sabawa addini ko al’ada ba abin da ya kamata ayi la’akari da shi ko kuma a lura da shi shi ne soyayya da kuma kauna, domin kuwa ni a nawa ganin indai tana son shi shi ma yana sonta wannan ba wani abun damuwa bane kuma hakan zai yi matukar basu dama da kuma lokaci na morewa rayuwar su, haka ma idan aka bar ta ta auri saurayi indai tana son shi shi ma hakan daidai ne. Haka kuma barinta ko bata damar mallakar hankalin shi ma wani abun lura ne, domin kula da lafiyarta da yaran da za ta haifa kawai dai abun da ya kamata mu sani a nan shi ne; kaucewa auren dole da kuma yi mata auren wuri wanda abubuwa ne da ka iya tauye mata hakkinsu ta bangaren cigabansu, iliminsu, lafiyarsu, tunaninsu zamantakewarsu da ma dai abubuwa da dama ta bangarori daban-daban. Sannan ya kamata ake lura da kauna da soyayya tsakanin mace da namiji walau babban mutum ko kuma dai yaro daidai sa’anta wannan shin zai tabbata da zaman lafiya da kuma cigaban zamantakewa a cikin al’umma. Amfanin auren yarinya da kuma namijin da ya fita da wuri na iya sawa yarinyar ta koyi wasu dubarun zama da manyan mutane da kuma yadda za ta kula da su, haka kuma za ta samu kulawa ta musamman da kuma biyawa kanta bukatun rayuwar yau da kullum sai dai rashin amfanin ya fi amfanin da yawa musamman idan ba ta sonsa duk abin da ta samu daga gare shi za ta yi kokarin farantawa wanda take so ne a boye kuma hakan na iya sawa ta fada aikata ba daidai ba da asalin saurayinta da take so, auren namiji da ya girmi yarinya na tauyewa yarinya hakkinta wanda suka hada da hakkin samun nutuwar zaman aure, rashin biyan bukatar sunnar zaman aure a gare shi, wanda ka iya taba lafiyarta, iliminta da tunaninta hadi da cigabanta a rayuwarta na yau da kullum.
Sunana Hassana Yahaya Iyayi (Maman Noor graphics), daga Jihar Kano:
Wani lokaci auren wanda ya mallaki hankalinsa ya fi auren kusan tsarerka shekara daya biyu duk kusan sa’ani ne duk aure na gani inaso kana so ya fi armashi, sannan kowa ya san ciwon kansa. Auren mai shekaru wani lokacin sai ka ga yarinya da kuruciyarta kafin ta gama cin lokacinta mijin ya tsufa sai ka ga ana ‘yan tsale-tsale. Iyaye dai su bari yarinya ta mallaki hankalinta Allah ya kawo wanda za su daidaita. Ba shi da wani amfani in dai yarinya ba tashi tayi da fitina ba bari lokacinta yayi tukun in Allah ya kawo abokin hadin sai ayi. Ana samun matsaloli barkatai daga baya ki ga yarinya ta fandare wata ma dai ki ga tana ‘yan tsale- tsale. Su yi hakuri su bari Allah kawo lokacinsu auren cikin salama kowa na so ya fi ba ruwansu da wata matsala.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sarkin Katsinan Gusau ya rasu
Allah ya yi wa Sarkin Katsinan Gusau da ke jihar Zamfara, Dr Ibrahim Bello rasuwa.
Ya rasu da safiyar Juma’a a Abuja yana da shekaru 71, bayan ya sha fama da jinya.
Yadda aka mayar da yaran da aka sace a Kano masu wanke-wanke a Kudu An kama budurwa mai shekara 19 da ake zargi da kashe yara 2 a BauchiMarigayin, wanda shi ne Sarkin Gusau na 16, ya ɗare kan karaga ne a shekara ta 2015, bayan rasuwar mahaifinsa.
Gogaggen ma’aikacin gwamnati, Dr Ibrahim ya taɓa zama Babban Sakatare a tsohuwar jihar Sakkwato da ma jihar Zamfara.
Ya yi mulkin ne na tsawon shekara 10 da ’yan watanni kafin rasuwar tasa.
Da yake tabbatar da rasuwar, Kakakin Gwamna Dauda Lawal na jihar ta Zamfara, Sulaiman Idris, a jajanta wa mutanen jihar a kan rasuwar.
A cikin wata sanarwa da safiyar Juma’a, Gwamnan ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi a wajensa, inda ya ce Sarkin ya tsaya tsayin daka wajen ci gaban jihar.
Daga nan sai ya yi addu’a Allah ya jikan mamacin ya kuma ba iyalansa da ma al’ummar jihar haƙurin jure rashin sa.