ICC : Rikicin Sudan kan Iya kasancewa Laifukan yaki da cin Zarafin dan Adam
Published: 4th, November 2025 GMT
Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya (ICC) ta nuna damuwa kan rahotannin baya-bayan nan na “kasha kashe, fyade, da sauran laifuka” da Rundunar Taimakon Gaggawa (RSF) ta aikata a yankin El-Fasher, na Sudan, tana gargadin cewa wadannan ayyukan na iya zama “laifukan yaki da cin zarafin bil’adama.”
“Irin wadannan ayyuka, idan aka tabbatar da su, na iya zama laifukan yaki da cin zarafin bil’adama a karkashin yarjejeniyar Roma,” in ji sanarwar da Ofishin Mai Gabatar da Kara na ICC, ya fitar.                
      
				
A cewar sanarwar, wadannan ayyukan sun lalata dukkan yankin Darfur tun daga watan Afrilun 2023,” ranar da aka fara yaki tsakanin sojojin Sudan da Rundunar Taimakon Gaggawa.
A cikin sanarwar, Ofishin Mai Gabatar da Kara ya tuna cewa, a karkashin kuduri na Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 1593 (2005), Kotun hukuntan manyan laifuka ta Duniya (ICC) tana da hurumin gurfanar da masu hannu a laifukan da aka aikata a rikicin da ke ci gaba da faruwa a Darfur.
Ta kuma bayyana cewa Ofishin yana binciken laifukan da aka aikata a Darfur tun bayan barkewar rikici a watan Afrilun 2023.
A ranar 26 ga watan Oktoba ne, Rundunar (RSF) ta kwace iko da garin El-Fasher tare da aikata kisan gilla ga fararen hula, a cewar kungiyoyin cikin gida da na kasa da kasa.
Rikicin da barke a ranar 15 ga Afrilu, 2023, tsakanin sojojin Sudan da RSF ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kimanin 20,000 tare da raba mutane sama da miliyan 15 da muhallansu, a cewar Majalisar Dinkin Duniya da majiyoyin cikin gida.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya saboda Dalilan Tsaro November 4, 2025 Hizbullah Ta yi Gargadin Mayar Da Martani Idan isra’ila Tayi Kokarin Kai Samame Ta Kasa November 4, 2025 Iran Tayi Maraba Da Kalaman Da Hukumar IAEA Kan Shirinta Na Nukuliya November 4, 2025 Prime Ministan Sudan Yayi Gargadi Game Da Aikewa Da Dakarun Tabbatar Da Zaman Lafiya Kasar November 4, 2025 Ribadu Ya Gana Da Manyan Hafsoshin Tsaron Najeriya kan barazanar Trump November 4, 2025 Mutum Daya Ya Yi Shahada Sanadiyyar Harin Sojojin HKI A Kudancin Lebanon November 3, 2025 Kungiyar Likitocin Kasar Sudan: Rundunar RSF Tana Garkuwa Da Dubban Fararen Hula A Al-Fasha November 3, 2025 An Sami Tsaikon Sauka Da Tashin Jiragen Sama A Tanzania Saboda Rikicin Zabe November 3, 2025 Falasdinawa Biyu Sun Yi Shahada A Nablus Da Khalil November 3, 2025 Jagora: Sabanin Jamhuriyar Musulunci Da Amurka Daga Tushen Manufa Ne Ba Sama-sama Ba November 3, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran : Jagora ya gindaya wasu sharudda kafin yin duk wata hulda da Amurka
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatollah Seyyed Ali Khamenei, ya bayyana cewa rikicin da ke tsakanin Tehran da Washington ya samo asali ne daga muradun jama’a, yana mai gargadin cewa duk wani hadin gwiwa da Amurka za a iya cimma shi ne kawai idan ta kawo karshen goyon bayan da take bai wa Isra’ila, ta kuma janye dukkan sansanonin sojinta daga yankin, sannan ta daina tsoma baki a harkokin Iran.
Ayatollah Seyyed Ali Khamenei ya bayyana hakan yayin ganawa da wani rukunin dalibai na kasar a jajibirin Ranar Dalibai ta Kasa wacce kuma ta yi daidai da ranar kasa ta yaki da girman kai na duniya.
Jagoran ya bayyana ranar a matsayin “ta tarihi” kuma wani muhimmin bangare na asalin Juyin Juya Halin Musulunci.
“Cece-cen da ke tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Amurka abu ne na zahiri, kuma ya samo asali ne daga rikicin muradun dake tsakanin bangarori biyu,” in ji Ayatollah Khamenei.
Jagoran ya bayyana farmakin da aka kai ofishin jakadancin Amurka a shekarar 1979 a matsayin “ranar alfahari da nasara” ga al’ummar Iran.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kasashen Musulmi : Falasdinawa ne kadai ke da hakkin jagorantar yankinsu November 4, 2025 Tanzaniya: An rantsar da shugaba Samia a wa’adi na biyu na shugabanci November 4, 2025 Iraniyawa na bikin tunawa da karbe ofishin jakadancin Amurka a Tehran a 1979 November 4, 2025 ICC : Rikicin Sudan kan Iya kasancewa Laifukan yaki da cin Zarafin dan Adam November 4, 2025 Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya saboda Dalilan Tsaro November 4, 2025 Hizbullah Ta yi Gargadin Mayar Da Martani Idan isra’ila Tayi Kokarin Kai Samame Ta Kasa November 4, 2025 Iran Tayi Maraba Da Kalaman Da Hukumar IAEA Kan Shirinta Na Nukuliya November 4, 2025 Prime Ministan Sudan Yayi Gargadi Game Da Aikewa Da Dakarun Tabbatar Da Zaman Lafiya Kasar November 4, 2025 Ribadu Ya Gana Da Manyan Hafsoshin Tsaron Najeriya kan barazanar Trump November 4, 2025 Mutum Daya Ya Yi Shahada Sanadiyyar Harin Sojojin HKI A Kudancin Lebanon November 3, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci