Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi
Published: 4th, November 2025 GMT
Ya kuma tunatar da cewa Nijeriya da Amurka na da kyakkyawar alaƙa tun da daɗewa, don haka bai kamata wannan sabuwar dambarwa ta lalata dangantakar ƙasashen biyu ba.
Obi ya ce dole ne a yi amfani da diflomasiyya da tattaunawa wajen shawo kan matsalar.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Mayar Da Martani Kan Barazanar Amurka Ga Nijeriya: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yaba Wa Kwankwaso
Kwankwaso, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na NNPP a zaben 2023, ya fitar da wata sanarwa mai karfi yana gargadin cewa kalaman Trump na iya kara ruruta wutar rikicin addini da kuma kara ta’azzara rashin tsaro a kasar.
A shafinsa na X, tsohon gwamnan ya yi Allah-wadai da matakin Trump na ayyana Nijeriya a matsayin “kasar da ke da matukar damuwa,” wanda kuma ya yi zargin ikirarin “kisan kare dangi ga Kiristoci.”
Kwankwaso, ya yi kira ga Amurka da ta taimaka wa Nijeriya da tallafin fasaha da leƙen asiri maimakon barazana, sannan ya shawarci Gwamnatin Tarayya da ta zurfafa hulɗar diflomasiyya ta hanyar naɗa wakilai na musamman domin tattaunawa.
“Ga ‘yan uwana ‘yan ƙasa, wannan muhimmin lokaci ne da ya kamata mu jaddada haɗin kai maimakon rarrabuwar kawuna. Allah ya albarkaci Nijeriya,” in ji Kwankwaso.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA