Aminiya:
2025-11-04@20:48:42 GMT

’Yan kwangila sun hana zaman majalisa kan rashin biyan haƙƙoƙinsu

Published: 4th, November 2025 GMT

Majalisar Wakilai ta dakatar da zamanta na tsawon mako guda, sakamakon zanga-zangar da wasu ’yan kwangila suka gudanar a ƙofar shiga ginin majalisar dokoki ta ƙasa da ke Abuja, saboda rashin biyan kuɗaɗen ayyukan da suka kammala tun shekarar 2024.

Rahotanni sun ce ’yan kwangilar sun yi dandazo ne a ƙofar shiga majalisar a ranar Talata, domin nuna rashin jin daɗinsu kan yadda gwamnati ta gaza biyansu haƙƙoƙinsu duk da cewa sun kammala ayyukan da aka ba su.

China ta yi martani kan barazanar Trump ta kai hari Najeriya Kotu ta sahale wa PDP gudanar da babban taronta a Ibadan

Bayanai sun ce masu zanga-zangar sun rufe hanyoyin shiga da fita na majalisar, abin da ya tilasta shugaban majalisar da sauran ’yan majalisa jinkirta zaman da aka shirya gudanarwa.

Wasu daga cikin ’yan kwangilar sun shaida wa manema labarai cewa sun gaji da alkawuran da gwamnati ke ci gaba da yi ba tare da cika su ba, inda suka yi kira da a gaggauta biyansu haƙƙoƙinsu kafin su sake komawa bakin aiki.

Majalisar ƙarƙashin jagorancin mataimakin kakakinta, Benjamin Okezie Kalu, ta ce an dakatar da zaman ne domin ba wa hukumomin da abin ya shafa damar tattaunawa da ’yan kwangilar, da nufin warware matsalar cikin lumana.

Matakin da majalisar ta ɗauka na zuwa ne bayan wani taƙaitaccen ƙudiri na gaggawa da shugaban marasa rinjaye a majalisar, Kingsley Chinda ya gabatar.

Chinda ya jawo hankalin majalisa kan “matsanancin halin da ’yan kwangila ke ciki” saboda rashin biyan su haƙƙoƙinsu duk da alƙawarin gwamnati.

A cewar Chinda, zanga-zangar ta samo asali ne a dalilin gazawar gwamnati wajen aiwatar da umarnin da Shugaba Bola Tinubu ya bai wa Ministocin Kuɗi da Tsara Tattalin Arziki da su biya ’yan kwangilar cikin gaggawa.

Bayan muhawara kan wannan ƙudiri ne majalisar ta amince da buƙatar bai wa Ministan Kuɗi, Wale Edun; da Ministan Tsara Tattalin Arziki, Atiku Bagudu; da Akanta Janar na Ƙasa wa’adin kwanaki bakwai domin su biya dukkan kuɗaɗen kwangilar da aka biyo gwamnati.

Daga bisani ne ɗan majalisa daga Jihar Zamfara, Kabiru Ahmadu Mai-Palace, ya gabatar da wani ƙarin ƙudiri da ya nemi majalisar ta dakatar da zamanta na mako guda har sai an ga matakin da gwamnatin tarayya ta ɗauka.

Da yake nasa tsokacin, Shugaban Kwamitin Majalisar kan Ka’idoji da Hanyoyin Gudanarwa, Francis Waive, ya mara masa baya, inda ya ce hakan ne ya fi dacewa ganin cewa masu zanga-zangar sun yi barazanar ci gaba da rufe hanyoyin majalisar har na tsawon mako guda.

Dangane da hakan ne majalisar ta yanke shawarar  dakatar da dukkan ayyukanta har zuwa Talata mai zuwa, yayin da ake jiran sakamakon tattaunawa tsakanin shugabannin majalisar da ɓangaren zartarwa.

Majalisar ta kuma umurci shugabanninta da su tabbatar da kiyaye wannan matsaya, tare da bayar da rahoto nan da mako guda domin ɗaukar matakai masu tsanani idan gwamnati ta gaza yin abin da ya dace.

 

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: kwangila Majalisar Wakilai yan kwangilar zanga zangar majalisar ta Majalisar ta a majalisar

এছাড়াও পড়ুন:

Prime Ministan Sudan Yayi Gargadi Game Da Aikewa Da Dakarun Tabbatar Da Zaman Lafiya Kasar

Prime ministan kasar sudan Kamil idris yayi gargadin cewa aikewa da dakarun tabbatar da zaman lafiya na kasashen waje a kasar Sudan  zai kara ruruta wutar rikicin ne da kuma keta yancin kasar, kuma kalaman nasa suna cewa ne bayan rahoton da aka fitar game da cin zarafin dan Adam da aka yi a El-fasher dake arewacin Darfur.

Sudan ta dade tana cikin rikci wanda ya haddasa yunkurin juyin mulki sau 20 a kasar da kuma yakin basasa guda biyu, lamarin ya kara taazzara ne bayan rikicin da ya barke a baya bayan nan, wanda ke barazanar ga zaman lafiya yankin , sai dai har yanzu kasashen duniya basu cimma matsaya ba kan yadda zaa samar da zaman lafiya mai dorewa a kasar ba.

Abin da ya faru a baya bayan nan sojojin kungiyar Rsf sun kai mummunan hari a El-fasher , inda majalisar dinkin duniya da kungiyoyin kare hakkin dan adam suka zarge su da yin kisan gilla, yanke hukumci kisa a filin daga da cin zarafin yan gudun hijira duk da yake cewa kungiyar ta Rsf ta karyata zargin.

Daga karshe Idris ya bukaci majalisar dinkin duniya  ta bayyana kungiyar Rsf a matsayin kungiyar yan taadda, kuma yayi watsi da ra’ayin aikewa da dakarun tabbatar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya a kasar don kasancewarsu zai kara ruruta wutar rikici ne kawai.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Ribadu Ya Gana Da Manyan Hafsoshin Tsaron Najeriya kan barazanar Trump November 4, 2025 Mutum Daya Ya Yi Shahada Sanadiyyar Harin Sojojin HKI A Kudancin Lebanon November 3, 2025 Kungiyar Likitocin Kasar Sudan: Rundunar RSF Tana Garkuwa Da Dubban Fararen Hula A Al-Fasha November 3, 2025 An Sami Tsaikon Sauka Da Tashin Jiragen Sama A Tanzania Saboda Rikicin Zabe November 3, 2025 Falasdinawa Biyu Sun Yi Shahada A Nablus Da Khalil November 3, 2025 Jagora: Sabanin Jamhuriyar Musulunci Da Amurka Daga Tushen Manufa Ne Ba Sama-sama Ba November 3, 2025 Turkiyye na karbar taron Kasashen Musulmi Kan Halin Da Ake Ciki A Gaza November 3, 2025 Isra’ila ta aikata laifuka 194 tun bayan tsagaita wuta a Gaza November 3, 2025 Girgizar kasa ta yi ajalin gomman mutane a Afghanistan November 3, 2025 Najeriya : tun kafin kalamman Trump muka dauki matakai November 3, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Majalisar Kaduna Ta Amince da Dokar Kafa Hukumar Fasahar Sadarwa da Tattalin Arzikin na Zamani
  • Li Qiang Ya Zanta Da Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya
  • Kakakin Majalisar Dokokin Lebanon Ya Jaddada Gagarumin Tsaron Kasa Da Gwagwarmaya Ta Baiwa Lebanon
  • Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha
  • NAJERIYA A YAU: Rashin Aikin Yi Da Hanyoyin Magance Su A Najeriya
  • Prime Ministan Sudan Yayi Gargadi Game Da Aikewa Da Dakarun Tabbatar Da Zaman Lafiya Kasar
  • Majalisar Karamar Hukumar Bubura Ta Kai Tallafin Kayayyakin Abinci Cibiyar Gyaran Hali
  • Gwamnatin Isra’ila Tana Ci Gaba Da Hana Masu Jinya Zuwa Kasashen Waje Neman Magani Daga Gaza
  • Rikicin PDP: Tsagin Wike ya dakatar da Damagum