Kakakin Majalisar Dokokin Lebanon Ya Jaddada Gagarumin Tsaron Kasa Da Gwagwarmaya Ta Baiwa Lebanon
Published: 4th, November 2025 GMT
Shugaban Majalisar Dokokin Lebanon ya bayyana cewa; Gwagwarmaya ta tilastawa gwamnatin mamayar Isra’ila rashin girke sojojinta a kan iyakar da ke tsakanin Isra’ila da Lebanon
Kakakin Majalisar Dokokin Lebanon Nabih Berri ya tabbatar da cewa: “Gwagwarmaya ta yi cikakken biyayya ga sharuɗɗan yarjejeniyar tsagaita wuta, kuma sojojin Lebanon sun tura sojoji da jami’ai sama da 9,000 a yankin da ke kudancin Kogin Litani.
Jawabin Kakakin Majalisar Dokokin Berri ya zo ne a ranar Talata yayin wani taro a hedikwatar Shugaban Ƙasa ta Biyu da ke Ain al-Tineh tare da tawagar kungiyar gidajen Rediyo da Talabijin ta Musulunci. Ya ce, “Amma tambayar da dole ne a yi ita ce: yaushe, a ina, kuma ta yaya Isra’ila ta bi ko da sashe ɗaya na yarjejeniyar tsagaita wuta?” Ya bayyana mamaki da “matsayin wasu a cikin Lebanon game da yadda suke nuna adawa ga ‘yan gwagwarmaya,” yana mai cewa “waɗannan mutane suna ƙin ambaton kalmar ‘gwagwarmaya’ a cikin kowace tattaunawa ta siyasa ko ta kafofin watsa labarai.” Yana mai tambayar cewa: “Shin akwai wata ƙasa a duniya da ta musanta babi mafi tsarki na tarihinta?”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Mataimakin Tsohon Shugaban Kasar Amurka Dick Cheney Ya Mutu A Yau Talata November 4, 2025 Ana Tattara Gawawwakin Mutanen Da Mayakan Rapid Support Forces Suka Kashe A Arewacin Kordofan Na Sudan November 4, 2025 Iran : Jagora ya gindaya wasu sharudda kafin yin duk wata hulda da Amurka November 4, 2025 Kasashen Musulmi : Falasdinawa ne kadai ke da hakkin jagorantar yankinsu November 4, 2025 Tanzaniya: An rantsar da shugaba Samia a wa’adi na biyu na shugabanci November 4, 2025 Iraniyawa na bikin tunawa da karbe ofishin jakadancin Amurka a Tehran a 1979 November 4, 2025 ICC : Rikicin Sudan kan Iya kasancewa Laifukan yaki da cin Zarafin dan Adam November 4, 2025 Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya saboda Dalilan Tsaro November 4, 2025 Hizbullah Ta yi Gargadin Mayar Da Martani Idan isra’ila Tayi Kokarin Kai Samame Ta Kasa November 4, 2025 Iran Tayi Maraba Da Kalaman Da Hukumar IAEA Kan Shirinta Na Nukuliya November 4, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Majalisar Dokokin
এছাড়াও পড়ুন:
Isra’ila ta aikata laifuka 194 tun bayan tsagaita wuta a Gaza
Ofishin Yada Labarai na Gwamnatin Gaza Ismail al-Thawabteh y ace Rundunar sojin Isra’ila ta aikata laifuka 194 tun bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza wadda ta fara aiki a ranar 10 ga Oktoba.
al-Thawabteh, darektan ofishin, ya shaida wa kamfanin dinalancin labarai na Anadolu cewa laifukan sun hada da hare-haren da Isra’ila ta kai hana shigar da kayayyakin lafiya, magunguna, tantuna.
Jami’in na Hamas ya ce sojojin Isra’ila sun sha ketare “layin da aka shata musu”, suna aika motoci zuwa wuraren zama, suna kai hare-hare ta sama da rusa gidaje, wanda ya haifar da mutuwar fararen hula da raunuka.
A cewar ofishin yada labarai, daga ranar 10 ga Oktoba zuwa karshen watan, manyan motoci 3,203 ne kawai suka shiga Gaza daga cikin motoci 13,200 da ake sa ran za su shiga karkashin yarjejeniyar, wato kashi 24 cikin 100.
Ofishin yada labarai ya kiyasta cewa har yanzu Falasdinawa kusan 9,500 ne suka bace, ko dai a karkashin baraguzan gine gine ko kuma ba a gano su ba.
Thawabteh ya ce wannan yarjejeniya ta kuma yi kira da a shigar da tantuna sama da 300,000 don ba da mafaka ga iyalai da suka rasa matsuguni.
Bayanan gwamnatin Gaza sun nuna cewa Isra’ila ta lalata kusan kashi 90 cikin 100 na kayayyakin more rayuwa na fararen hula na yankin, wanda ya haifar da asarar da aka kiyasta ta kai dala biliyan 70.
Thawabteh Ya yi kira ga shugaban Amurka Donald Trump da masu shiga tsakani na kasa da kasa da su shiga tsakani cikin gaggawa don tilasta wa Isra’ila ta aiwatar da yarjejeniyar gaba daya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Girgizar kasa ta yi ajalin gomman mutane a Afghanistan November 3, 2025 Najeriya : tun kafin kalamman Trump muka dauki matakai November 3, 2025 Sudan : Mutane 1,500 sun rasa matsugunansu sakamakon tashin hankali November 3, 2025 UNICEF Tayi Gargadi Game Da Mawuyacin Hali Da Yara Ke Ciki A Gaza November 3, 2025 Hamas Ta yi Watsi Da Zargin Da Amurka Tayi Mata Kan Batun Motocin Agaji A Gaza November 3, 2025 El-Zakzaki: Yakin Sudan Yana Kare Maslahar Kasashen Yamma ne Kawai November 3, 2025 Iran Ta Karbi Sako Kan Batun Komawa Teburin Tattaunawa Ba Kai Tsaye Ba November 3, 2025 Ministar Jin Dadin Jama’a ta Sudan: Mayakan RSF Sun Kashe Mata 300 Da Yi Wa 25 Fyade A El Fasher November 3, 2025 Pezeshkian: Bunkasa Masana’antar Makamashin Nukiliyar Iran Don Inganta Rayuwar Al’ummar Iran Ne November 2, 2025 Araqchi: Da Hadin Bakin Amurka, Gwamnatin Isra’ila ta kaddamar Da Hari Kan Kasar Iran November 2, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci