Aminiya:
2025-09-18@02:18:02 GMT

An wawushe motar abinci ta Hukumar WFP a Borno

Published: 20th, March 2025 GMT

Wasu da ba a san ko su wanene ba sun yi awan gaba da kayayyakin wata mota ɗauke da kayan abinci na Hukumar abinci ta duniya (WFP) a garin Gubio, yayin da take kan hanyarta ta zuwa Damasak a Jihar Borno.

Majiyar leƙen asiri ta shaidawa Zagazola Makama cewa, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:30 na rana lokacin da Aminu Malam Umar direban wata babbar mota ƙirar Iɓeco ya tsaya a gefen titi.

’Yan adawa sun shirya ƙalubalantar Tinubu a zaɓen 2027 – Atiku Gobara ta ƙone gidaje tare da asarar dukiya a Gombe

Yayin da motar ta tsaya a gefen titi ba tare da kula daga jami’an tsaro ba, wasu da ba a san ko su waye ba suka sace buhunan shinkafa da gishiri da sukari da wake da kuma man girki da dama, duk da cewa ba a tantance adadin da kuma darajar kayayyakin da aka sace ba har ya zuwa yanzu.

Jami’an tsaro sun ziyarci wurin da lamarin ya faru, amma ba a kama kowa ba.

Daga bisani sojoji sun ɗauke motar zuwa  Gubio lafiya lau a yayin da ake ci gaba da bincike don gano waɗanda suka aikata laifin tare da ƙwato kayayyakin da aka sace.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Kundin Bajinta na Guinness ya taya Hilda Baci murna

Fitacciyar mai girkin nan, Hilda Effiong Bassey, wadda aka fi sani da Hilda Baci, ta sake kafa tarihi a duniya ta hanyar girka tukunyar dafa-dukar shinkafa mafi girma bayan shafe awa takwas tana girkin.

Hakan dai na ƙunshe ne cikin wani saƙon taya murna da Kundin Bajinta na Guinness ya wallafa a shafukan sada zumunta.

Peter Obi ya kai wa Obasanjo ziyara ’Yan sanda sun sasanta rikicin asibitin AKTH da KEDCO

Hilda Baci dai ta dafa shinkafa dafa-duka mafi yawa a tarihi tare da sauran kayan haɗi da sunadaran ɗanɗano wadda nauyinta ya kai kilo 8,780 a yankin Victoria Island da ke Legas.

A shekarar 2023 Hilda mai shekaru 28 ta shiga Kundin Bajinta na Guiness World Record bayan shafe awa 93 da mintuna 11 tana girke-girken abinci iri-iri.

A wannan karon, Hilda ta girka ƙananan buhuna 200 na shinkafa wanda nauyinsu ya kai kilo 4,000 da katan 500 na tumatir da kilo 600 na albasa da sauran kayan haɗi.

An gudanar da zaman girkin a fili a cikin birnin kasuwanci na Legas, lamarin da ya ja hankalin ɗaruruwan masu kallo.

Dafa-dukar shinkafa wadda a wasu harsunan ake kira Jollof rice abinci ne da ake sha’awa sosai a yankin Yammacin Afirka, inda ƙasashe kamar Nijeriya, Ghana, Senegal, Kamaru, da Gambiya ke da’awar cewa su ne ke da mafi ƙwarewa a wurin girka ta.

A shekarar 2023, Hukumar Ilimi, Kimiyya, da Al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO) ta amince da Senegal a matsayin wurin da wannan abinci na dafa-dukar shinkafa ta samo asali.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • UNICEF Ya Ba Da Tallafin Kayayyakin Aiki Ga Cibiyoyin Lafiya A Kirikasamma
  • Larijani: Iran Da Saudiyya Za Su Bunkasa Aiki Tare A Fagagen Kasuwanci Da Tsaro
  • NECO ta saki sakamakon jarabawar 2025
  • Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna
  • Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno
  • Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabala
  • ’Yan bindiga sun sace mutum 40 a masallaci a Zamfara
  • Kundin Bajinta na Guinness ya taya Hilda Baci murna
  • ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Masallata Tare Da Garkuwa Da Mutane A Zamfara
  • Mummunan Hatsarin Mota Ya Kashe Fasinjoji 17 A Zamfara