Hajjin Bana: Maniyata 3, 155 Suka Yi Rijista a Kano
Published: 21st, March 2025 GMT
Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta ce ta samu nasarar kammala rijistar maniyyata aikin hajjin bana 3,155.
Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Lamin Danbappa, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Kano a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar gudanarwar Hukumar Shige da Fice a ofishinsa.
Danbappa ya bayyana cewa hukumar ta kammala dukkan shirye-shirye da suka hada da kwasa-kwasan horas da aikin hajji, da takardu da kuma tattara kayanai.
“Yanzu haka hukumar ta fara bayar da biza ga maniyyatan da suka yi rijista.
Ya yabawa gwamnatin jiha bisa yadda take ci gaba da tallafawa kokarin hukumar na ganin an gudanar da aikin Hajji cikin sauki.
A nata bangaren, sabuwar shugabar hukumar shige-da-fice mai kula da filin jirgin sama na Malam Aminu Kano (MAKIA), Aisha Nda ta ce sun kasance a hukumar ne domin bayar da lambar yabo ga Darakta Janar.
Abdullahi jalaluddeen/Kano
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন: