Majalisar Dokokin Nijeriya Ta Zama Ƴar Amshin Shata — Kwankwaso
Published: 21st, March 2025 GMT
Jagoran jam’iyyar adawa ta NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya soki Majalisar dokoki ta 10 a Nijeriya bisa amincewarta da ƙaddamar da dokar ta ɓaci (State of Emergency) a Jihar Ribas da kuma dakatar da gwamnan jihar da mataimakinsa da majalisar dokokin jihar daga aiki ta hanyar shugaban ƙasa Bola Tinubu, yana mai cewa ‘yan majalisar sun zama kamar ƴan amshin Shata.
Kwankwaso, wanda ya riƙe muƙamin gwamnan jihar Kano sau biyu, ya ga baiken wannan mataki na majalisar, in da ya ce yayi kama da irin kuskuren da ‘yan majalisar tarayya suka yi a lokacin majalisa ta uku (Third Republic), wanda ya haifar da soke zaɓensu na ranar 12 ga Yuni, 1993. Ya bayyana cewa ƴan majalisar ya kamata ta juya wa wannan rashin adalci da shugaban ƙasa Tinubu ya aikata a Rivers, amma sun sai suka zaɓi goyon bayan wannan mataki wanda yake ba bisa ƙa’ida ba.
Ba Na Goyon Bayan Dakatar Da Gwamnan Jihar Ribas – Ndume Jigon APC Ya Fara Yunkurin Sulhunta Kwankwaso, Ganduje Da ShekarauKwankwaso ya ci gaba da cewa wannan matakin da shugaban ƙasa Tinubu ya ɗauka na dakatar da dukkan jami’an da suke zaɓaɓɓu a jihar Ribas ya saɓa wa kundin tsarin mulki, yana kuma kawo barazana ga tsarin dimokuraɗiyya. Ya bayyana damuwarsa game da yadda majalisar ta yi amfani da tsarin zabe na muryar wajen goyon baya (voice vote) wanda bai dace da ƙa’idojin zaɓe na ƙasa ba.
Kwankwaso ya ƙara da cewa wannan mataki na iya kawo matsala ga ci gaban dimokuraɗiyyar da aka samu cikin shekaru 26 na dawowarta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Kwankwaso
এছাড়াও পড়ুন:
Tsaro: Taimakonmu Amurka ya kamata ta yi maimakon ba barazana ba — Kwankwaso
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana damuwarsa kan kalaman da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi game da Najeriya.
Kwankwaso, ya yi wannan magana ne bayan Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin yaƙi game da zargin kisan kiyashi da ake yi wa Kiristoci.
Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka Kisan Kiristoci: Lauyoyi sun nemi Gwamnatin Tarayya ta tattauna da AmurkaA cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kwankwaso, ya ce Najeriya ƙasa ce mai cikakken ’yanci, wadda ke fama da matsalar tsaro daga miyagu a sassa daban-daban na ƙasar.
“Matsalar tsaron da muke fuskanta ba ta bambanta tsakanin addini, ƙabila ko ra’ayin siyasa,” in ji shi.
Ya buƙaci gwamnatin Amurka da ta tallafa wa Najeriya da sabbin fasahohi domin yaƙar matsalar tsaro maimakon yin kalaman da za su iya raba kan ’yan ƙasa.
“Amurka ya kamata ta taimaka wa hukumomin Najeriya da ingantattun fasahohi don magance matsalolin tsaro, maimakon yin barazanar da za ta ƙara raba ƙasar,” in ji Kwankwaso.
Haka kuma, ya shawarci Gwamnatin Najeriya da ta naɗa jakadu na musamman domin inganta hulɗar diflomasiyya da Amurka da kare muradun ƙasar a matakin duniya.
Ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su zauna lafiya, inda ya bayyana cewa wannan lokaci ne da ya dace a fifita haɗin kan ƙasa ba abin da ke raba ta ba.
“Wannan lokaci ne da ya kamata mu mayar da hankali kan abin da zai haɗa kanmu ba wanda zai raba mu ba. Allah Ya albarkaci Najeriya,” in ji shi.