Tinubu ya ba ni riƙon Ribas don wanzar da zaman lafiya — Ibas
Published: 21st, March 2025 GMT
Shugaban Riƙo na Jihar Ribas, Ibok Ibas, ya ce Shugaba Bola Tinubu, ya naɗa shi ne domin dawo da zaman lafiya a jihar, wadda ke fama da rikicin siyasa.
Da yake jawabi a wani shirin talabijin a daren Alhamis a Fatakwal, Ibas ya bayyana naɗin nasa a matsayin matakin da ya dace don kawo ƙarshen rikicin siyasa da ya ɗauki kusan shekaru biyu.
Ya ce rikicin ya hana ci gaban gwamnati, tare da haifar da matsalar tsaro da koma bayan tattalin arziƙi a jihar.
“A matsayina na ɗan yankin Neja Delta, na fahimci damuwar mutanenmu. Rashin tabbas a Jihar Ribas ya shafi iyalai, ’yan kasuwa da rayuwar yau da kullum.
“Naɗin da aka yi min ba na siyasa ba ne, sai dai don dawo da doka da oda, tare da tabbatar da cewa mutanenmu suna rayuwa cikin kwanciyar hankali.”
Ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa babban aikinsa shi ne dawo da zaman lafiya, tabbatar da bin doka da oda, tare da samar da yanayin da zai ba da damar ci gaban gwamnati da bunƙasa tattalin arziƙi.
“Ba aikin mutum ɗaya ba ne. Dole ne al’ummar Ribas su haɗa kai, dattawa, sarakunan gargajiya, ’yan siyasa, ’yan kasuwa, matasa da ƙungiyoyin fararen hula.
“Na zo a matsayin wanda zai hidimta wa jihar, wanda ke da nauyin dawo da zaman lafiya da tsari, domin Jihar Ribas ta dawo da matsayinta na cibiyar arziƙin man fetur a Najeriya.”
Ibas, ya gargaɗi ’yan jihar da su guji tashin hankali da aikata laifuka, inda ya bayyana cewa gwamnati ba za ta yarda da duk wani yunƙuri na kawo ruɗani ba.
Sai dai ya tabbatar da cewa zai mutunta haƙƙoƙin ’yan ƙasa tare da bin doka.
Ya buƙaci jama’a da su haɗa kai don girmama juna da samar da zaman lafiya a jihar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Naɗi Siyasa Zaman lafiya da zaman lafiya
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan bindiga sun hallaka mutum 4, sun sace mata 4 a Sakkwato
’Yan bindiga sun kai sabon hari wasu yankuna na Jihar Sakkwato, inda suka kashe mutane huɗu tare da yin awon gaba da mata huɗu.
Wani mazaunin Gatawa, ya shaida wa Aminiya ce harin ya faru ne a daren ranar Asabar, lokacin da ’yan bindiga sama da goma suka shiga garin a kan babura.
Mutum 5 sun rasu sanadin gobara da faɗa wa rijiya a Kano Sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar BeninA cewarsa, “Sun ratsa gefen gari suka dinga shiga gida-gida. Sun harbe mutane huɗu; uku sun mutu nan take, na huɗu kuma ya rasu a asibiti.”
Ya ƙara da cewa bayan harin, sojoji sun isa garin wanda hakan ya sa maharan suka tsere, amma duk da haka sun tafi da mata huɗu.
Sai dai ya bayyana cewa akwai wani malamin makaranta, Mustafa Malam Malam, da aka taɓa yin garkuwa da shi a baya.
Duk da cewa an biya kudin fansar Naira miliyan ɗaya da rabi, ba su sake shi ba, daga baya suka kashe shi.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Sabon Birni, Alhaji Ayuba Hashimu, ya musanta batun cewa an kai hari masallaci.
Ya ce babu masallacin da aka kai wa hari ko aka kashe limami kamar yadda ake yaɗawa a kafofin watsa labarai.
Shi ma ɗan majalisar yankin, Aminu Boza, ya ce ba su da labarin wani hari da aka kai wa masallaci a yankin.
A wani labarin kuma, ’yan bindiga sun kai hari ƙauyen Shallah da ke mazabar Turba a Ƙaramar Hukumar Isa, inda suka kashe mutum ɗaya.
Daga nan sai suka wuce garin Barkeji, inda suka ƙone rumbunan abinci a daren ranar Asabar.
Ya zuwa yanzu babu wata sanarwar daga rundunar ’yan sandan jihar.