Jiragen yakin HKI sun kai hare-hare a gabaci da kuma kudancin kasar Lebanon wanda yak eta yarjeniyar zaman lafiyan da HKI ta cimma da kungiyar Hizbullah mai lamba 1701 ta shekara ta 2006.

Tashar talabijin ta Presstv anan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran gwamnatin kasar Lebanon na cewa, jiragen yakin HKI sun kai hare-hare kan bayan kauyen taraya a gundumar ba’alabak, cikin lardin Ba’alabak Hermel, da kuma kan garin Shaara kusa da garin Jenta a dai dai kasar tsaunuka da ke yankin.

A kudancin kasar Lebanon kuma jiragen yakin HKI sun jefa makamai masu linzami har guda 4 a kan yakunan Jibaa da Snaya

Kafafen yada labaran HKI sun tabbatar da wannan labarin sun kuma nakalto sojojin kasar suna cewa sun kai hare-haren ne kan damdamalin cilla makamai masu linzami na kungiyar Hizbullah.

Sanarwan sojojin yahudawan ya ce: Sojojin HKI sun kai hari kan wuraren kungiyar Hizbullah, wadanda suke karkashin kasa a lardin Biqaa a kasar Lebanon.

Gwamnatin HKI a dole ta amince da tsagaita budewa juna wuta da kungiyar Hizbullah a ranar 27 ga watan Nuwamban shekarar da ta gabata, bayan asarorin na rayukan sojoji da tankunan yaki da kuma gine-gine masu muhimmanci wadanda kungiyar Hizbullah ta lalata a cikin yakin watanni 14 da suka fafata. Ta amince da kuduri kwamitin tsaro mai lamba 1701 na kwamitin tsaro ba tare da ta cimma ko guda daga cikin manufofin fara yakin ba.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: kungiyar Hizbullah sun kai hare hare kasar Lebanon yakin HKI sun

এছাড়াও পড়ুন:

Manoma a Jigawa Sun Jinjinwa Kungiyar Sasakawa Africa Bisa Bada Tallafi a Harkar Noma

Daga Usman Muhammad Zaria

 

Kananan manoma a jihar Jigawa sun yabawa kungiyar Sasakawa Africa dangane da tallafin da take samarwa a fannin inganta noma.

Yayin tattaunawa da wasu daga cikin wadanda suka ci moriyar shirin musamman manoman shinkafa a garin Chandam dake karamar hukumar Birnin Kudu, sun bayyana cewa tallafin Sasakawa ya habaka noman shinkafar su tare da samun karin kudade.

Manoman sun bayyana cewar shirin ya taimaka masu wajen bunkasa harkokin noma tare da tallafawa al’ummomin su.

Daya daga cikin wadanda suka amfana da shirin a yankin Chandam dake karamar hukumar Birnin Kudu, Buhari Nafi’u, yace Sassakawa Africa ta samar masu da tallafin  noma daban daban.

A cewar sa tallafin sun hada da horo wanda ya taimakawa kananan manoma wajen ganin sun kara samun kudade tare da inganta rayuwar maza da mata a yankin.

Yace a wannan shekarar sun noma amfanin gona mai yawa sakamakon horon da suka samu karkashin shirin, inda suka hadu sukayi noman a kungiyance a yankin Birnin Kudu.

Buhari ya kara da cewar, a shekarun baya suna daukan kwanaki casa’in kafin su girbe shinkafa amma zuwan Sassakawa ya sa sun yi noma tare da girbe amfanin gonan su a cikin kwanaki saba’in saboda irin da kungiyar ta basu.

Yace yanzu haka sun fara amfani da shinkafar da suka noma a gidajen su.

Yace an basu takin zamani kyauta tare da sauran kayayyakin feshi.

Ya godewa tallafin na Sassakawa, yana mai cewar zai cigaba da amfani da irin da aka basu tare da koyar da mazauna yankin abubuwan da aka horar da su akai.

Shi ma Malam Rufai Nasiru daga yankin na Chandam  yace sun kara samun ilimi akan sabbin dubarun noma wanda suka samu daga kungiyar ta Sassakawa.

Yace a bana ya noma buhun shinkafa 8 ba kamar a baya ba da yake noma buhu biyar, yana mai cewa shirin yana da inganci kuma zai cigaba da amfani da irin da kungiyar ta basu.

A garin Chuwasu  dake karamar hukumar Taura, Aminu Babanyara ya bayyana cewar sun ci moriyar shirin ta hanyar samun iri masu inganci da takin zamani da kuma horo akan sabbin dubarun noma.

Yace wasu daga cikin abubuwan da suka koya sun hada da amfani da shara wajen yin taki a gida inda suka ce hakan yasa sun samu karin shinkafa da geron da suke nomawa idan aka kwatanta da shekarun baya.

Babanyara, yace sabbin dubarun da suka koya da kuma irin da Sassakawa suka basu, ya basu damar ninka abin da suka saba nomawa a damina sau uku.

Yace da farko suna da shakku akan amfani  da sabbin irin da sabbin dubarun noman, amma kuma bayan sun gwada a shekaru biyu na farko sun ga alfanun hakan wajen bunkasa amfanin gonan da suke nomawa.

Manoman sun kuma yi kira ga kunyiyar ta Sassakawa ta samar masu da injinan casa domin saukaka masu al’amura.

Malama Amina Abdulrahman wacce tayi jawabi a madadin kungiyar mata manoma a Karamar  Hukumar Taura, tace shirin tallafin Sassakawa ya kawo sauyi a rayuwar su musamman a fannin samun kasuwanci da amfanin gonar da ake sarrafawa don yin abinci mai gina jiki na yara.

A cewar ta an horar da su akan yadda za su samar da abinci mai gina jiki a yankuna tare da yadda za su yi aiki a kungiyance don inganta noma.

A don haka, tayi kira ga kungiyar Sassakawa ta samar masu da injinan sarrafa amfanin gona na zamani.

Yankunan da aka ziyarta sun hada da Chandan dake Birnin Kudu da kuma Sabon Gari shi ma a karamar hukumar Birnin Kudu.

Sauran sun hada da Baranda dake Dutse da kuma Chuwasu dake karamar hukumar Taura.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Isra’ila Ta Kashe Mutane 4 Tare Da Jikkata Wasu Guda 3 A Kudancin Labanon
  • Shugaban Kasar Najeriya Ya Mayar Da Martani Ga Takwaransa Na Amurka Akan Rikicin Addini
  • Majalisar Dinkin Duniya ta damu da hare-haren Amurka a Caribbean da Pacific
  • Dan Majalisar Jema’a/Sanga, Daniel Amos, Ya Koma Jam’iyyar APC
  • Ya Kamata Sin Da Amurka Su Zama Kawayen Juna Ba Abokan Gaba Ba
  • Manoma a Jigawa Sun Jinjinwa Kungiyar Sasakawa Africa Bisa Bada Tallafi a Harkar Noma
  • Masar da Eritrea Sun Tattauna Bukatar Tallafawa Kasar Sudan
  • NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa
  • Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Kutsen Na Isra’ila A Kudancin Kasar
  • Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Duk Wani Kutse Na Isra’ila A Kudancin Kasar