Kotun ƙoli ta tabbatar da Anyanwu a matsayin sakataren PDP
Published: 21st, March 2025 GMT
Kotun Ƙoli ta yanke hukunci tare da tabbatar da Samuel Anyanwu a matsayin halastaccen Sakataren Jam’iyyar PDP na Ƙasa.
Anyanwu, wanda na hannun daman Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike ne, ya shafe lokaci yana takun-saƙa da Sunday Ude-Okoye kan wannan matsayi.
Tinubu ya ba ni riƙon Ribas don wanzar da zaman lafiya — Ibas Kwankwaso ya yi Allah-wadai da ayyana dokar ta-ɓaci a RibasUde-Okoye ya samu goyon bayan wasu ɓangarori na jam’iyyar PDP bayan Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Enugu ta tabbatar da naɗinsa, biyo bayan hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ta tsige Anyanwu.
Sai dai, a ranar Juma’a, wani kwamitin alƙalan Kotun Ƙoli guda biyar, ya yanke hukunci cewa rikice-rikicen shugabanci a cikin jam’iyya al’amari ne na cikin gida, kuma ba hurumin kotu ba ne sai dai idan akwai wasu dalilai na musamman.
Mai shari’a Jamilu Tukur, wanda ya jagoranci hukuncin, ya bayyana cewa irin wannan shari’a za ta iya shiga hurumin kotu ne kawai idan ta ƙunshi karya doka, aikata laifi, ko saɓa wa yarjejeniya.
Rigima game da muƙamin sakataren jam’iyyar PDP na ƙasa, ta samo asali ne bayan Anyanwu ya ajiye muƙamin don yin takarar gwamna a Jihar Imo, amma bai samu nasara ba.
Yunƙurinsa na sake dawowa kan muƙamin ya jefa jam’iyyar cikin ruɗani.
Bayan Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da tsige shi a watan Disamban 2024, Anyanwu ya shigar da ƙara a Kotun Ƙoli, wacce a yanzu ta yanke hukunci, tare dawo da shi a matsayin halastaccen sakataren jam’iyyar PDP na ƙasa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Anyanwu Sakatare Siyasa jam iyyar PDP tabbatar da
এছাড়াও পড়ুন:
Sudan Ta Zargi Janar Haftar Na Libiya Da Goyon Bayan ‘Yan Tawayen Kasarta Na Rapid Support Forces
Ma’aikatar Harkokin Wajen Sudan na zargin Janar Haftar na Libiya da goyon bayan hare-haren ‘yan tawayen kasarta
Sojojin Sudan da ma’aikatar harkokin wajen Sudan sun zargi Janar Khalifa Haftar mai ritaya da goyon bayan hare-haren da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces suka kaddamar a kan iyakokin Sudan da Masar da Libya.
A cewar sanarwar da Rundunar Sojin Sudan ta fitar, Dakarun Kai Daukin Gaggawa na Rapid Support Forces da ke samun goyon bayan Bataliyar Salafiyya ta Haftar, sun kai hare-hare kan iyakokin Sudan da Masar da Libya, da nufin kwace wadannan yankuna masu matukar muhimmanci.
Sanarwar ta kara da cewa: Wannan shiga tsakani da dakarun Haftar suka yi kai tsaye ya zama “cin zarafi a fili” ga ‘yancin Sudan da al’ummarta, tare da nuna cewa harin wani bangare ne na makircin kasa da kasa da na yanki bisa cikakkiyar masaniya da fahimtar kasashen duniya.
Sojojin kasar ta Sudan sun jaddada aniyarsu ta tunkarar wannan ta’addanci, ba tare da la’akari da irin makircin da ake kullawa ba, gami da tabbatar da aniyarsu ta kare ‘yancin kan kasa tare da goyon bayan al’ummar Sudan.