Ƙungiyoyin ƙwadago sun buƙaci Tinubu ya mayar da Fubara kan kujerarsa
Published: 19th, March 2025 GMT
Ƙungiyoyin Ƙwadagon Najeriya, NLC da TUC, sun yi Allah-wadai da matakin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ɗauka na sanya dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas.
Ƙungiyoyin sun soki dakatar da Gwamna Siminilayi Fubara, mataimakiyarsa, da ’yan majalisar dokokin jihar.
Goman Ƙarshe: Dama ta ƙarshe ga mai neman rahamar Allah Matatar Dangote ta dakatar da sayar da fetur a NairaA wata sanarwa da suka fitar ranar Laraba, ƙungiyoyin bitu sun bayyana cewa wannan mataki ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Najeriya, musamman sashe na 2 da 305 na dokar 1999 da aka yi wa kwaskwarima.
Sun ce wannan mataki ne da ka iya tauye ikon zartarwa, tare da zama barazana ga dimokuraɗiyya a Najeriya.
A ranar Talata ne, Shugaba Tinubu ya sanar da sanya dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas, inda ya bayyana cewa rikicin siyasar jihar yana barazana ga zaman lafiya da tsaron al’umma.
Wannan mataki ya janyo ce-ce-ku-ce a faɗin Najeriya, inda mutane da dama ke ganin hakan bai dace da kundin tsarin mulki ba.
Ƙungiyoyin NLC da TUC sun buƙaci Shugaba Tinubu da ya gaggauta janye wannan mataki, don kada ya jefa Najeriya yanayin saɓa wa doka a nan gaba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Dokar Ta Ɓaci Fubara Ƙungiyoyin Ƙwadago
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Kano Ta Kara Jaddada Dokar Haramcin Yin Haya da Babur a Jihar
Daga Abdullahi Jalaluddeen
Gwamnatin Jihar Kano ta sha alwashin daukar mataki kan masu yin haya da babura a fadin jihar.
Mai bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Sufuri, Alhaji Danladi Idris Karfi, ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a Kano.
Ya ce gwamnatin ta lura da yadda aka cigaba da yin haya da babura a cikin birnin Kano, lamarin da ya bayyana a matsayin barazana ga zaman lafiya a jihar.
Danladi Karfi ya jaddada cewa dokar da ta haramta zirga-zirgar babura a matsayin sufuri na haya har yanzu tana nan daram, kuma za a aiwatar da ita sosai, inda ya gargadi masu karya doka da cewa za su fuskanci hukunci mai tsanani.
Ya kara da cewa Kano na daga cikin jihohi mafi zaman lafiya a kasar nan, kuma gwamnati ba za ta lamunci duk wani abu da zai iya tayar da hankalin jama’a ba.
Ya kuma yi kira ga jama’a su kasance masu lura da kai rahoton duk wani abin da suke shakku ga hukumomin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.