Sabon Kawancen Jihohin Arewacin Najeriya Da Kamfanonin Sin Zai Fa’idantar
Published: 20th, March 2025 GMT
A dunkule, ayyukan da wadannan kamfanoni za su gudanar sun kunshi samar da wadataccen takin zamani da fasahar noma ta zamani, da dabarun sarrafa takin gargajiya da fasahar kiwo mafi dacewa da jihar. Haka nan, kawancen nasu zai hada har da amfani da fasahohin zamani wajen kyautata sha’anin tsaro, da harkokin sufuri da bangaren hidindimun jama’a, da sauran dabaru da tsare-tsare na kwarewar aiki da za a samar a jihar.
Hakika wannan kawance zai fa’idantar sosai saboda yadda yankin na arewa ya kwashi tsawon wasu shekaru yana kaka-ni-ka-yi da matsalolin dake tarnake ci gabansa sakamakon mummunar matsalar tsaro musamman ma a jihar Zamfara wadda ta zama babbar tungar ’yan bindiga.
Kwararru a fannin sha’anin tsaro, sun sha nanata cewa matukar ana so a magance matsalar tsaron da ta hana arewacin Najeriya sakat dole sai an hada da magance zaman kashe wando, da bunkasa tattalin arziki da kuma samar da na-gartaccen ilimi.
Sabon yunkurin jihohin arewa na kulla kawance da kamfanonin Sin babu shakka zai bude kofofin karfafa tattalin arzikin yankin wanda Allah ya albarkace shi da kasar noma mai kyau fiye da sauran sassan Najeriya, sannan ga tarin albarkar yawan jama’a, da albarkatun sarrafa sabbin makamashi, domin kamfanonin Sin suna da kwarewar aiki da dimbin ayyuka na fasahar zamani ta yadda suke iya sarrafa albarkatu kalilan a samar da amfani mai yawa. Sannan suna da karfin zuba jari fiye da yadda ake zato, domin ko a watan Satumban 2024, gwamnatin jihar Neja da ke arewacin Najeriya ta rattaba hannu da wasu kamfanonin Sin guda biyu –COVEC da CREC a kan kwangilar dala miliyan 684 domin gudanar da ayyukan gona na musamman a jihar.
Tabbas, jihohin sun dauki hanya mai kyau da za ta fa’idantar, fatana shi ne a wayi gari yankin arewa ya dawo da martabarsa ta ci gaban tattalin arziki da kyautata rayuwar al’umma.(Abdulrazaq Yahuza)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Yadda Raguwar Maniyyatan Najeriya Ke Tasiri Ga Aikin Hajji A Najeriya
A kwanakin nan ana samun raguwar kujerun maniyyata aikin Hajji daga Najeriya, abin da ya jawo fargaba ga masu shirin zuwa kasa mai tsarki da kuma masu hidimar su.
A da, Najeriya na samun kujeru sama da dubu casa’in daga gwamnatin Saudiyya, amma cikin shekaru kadan da suka gabata adadin ya ragu zuwa kusan dubu sittin da biyar.
Kazalika a yanzu gwamnatin na saudiyya ta bayyana cewa idan har maniyyatan Najeriya basu biya cikakken kudaden hajjin bana ba, to akwai alamun sake rage yawan kujerun zuwa dubu hamsin.
NAJERIYA A YAU: Dalilan Malaman Jami’oi Masu Zaman Kansu Na Shiga Ƙungiyar ASUU DAGA LARABA: Tasirin Da Tura Jami’an ‘Yan Sanda Kare Manyan Mutane Zai Haifar Ga Tsaron Al’ummaKo yaya kara raguwar kujerun maniyyatan Najeriya ke kara tasiri ga Najeriya?
Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokacin zai yi duba a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan