Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Na Mata
Published: 27th, July 2025 GMT
Tawagar ƙwallon ƙafa ta mata a Nijeriya (Super Falcons) ta samu nasarar lashe kofin ƙasashen nahiyar Afirika na mata bayan doke masu masaukin baƙi Maroko a wasan ƙarshe da ci 3 da 2.
An buga wasan ne a daren ranar Asabar, wanda ya ƙayatar da masu kallo.
Musuluntar Wata Ce Ya Ja Hankalina Shiga Fim – Sailuba Dadin Kowa Masanin Kimiyyar Na’ura Mai Kwakwalwa Robert Tarjan Ya Jinjinawa Dabarun Sin Na Ingiza Ilimin KimiyyaƘasar Moroko ce ta fara jefa ƙwallaye biyu a minti na 14 da minti 24.
Amma Nijeriya ta farke duka ƙwallaye biyu kuma ta jefa ta uku a minti na 89 na wasan, da wannan sakamakon Nijeriya ta samu nasarar lashe gasar karo na 10 a tarihi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: ƙwallo Maroko Nahiyar Afirka
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Da Eu Sun Fara Tattaunawa A Istambul
Jami’an diblomasiyya na kasashen Iran da kuma na tarayyar Turai 3 wato Faransa da Jamus da kuma burtaniya sun fara tattaunawa gaba da gaba bayan yakin kwanaki 12 wanda Amurka da HKI suka kai mata.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta kara da cewa wannan tattaunawar yana da matukar muhimmanci don zasu tattauna kan shirin makamashin nukliyar kasar Iran da kuma dauke mata takunkuman tattalin arzikin da su dora mata saboda shirinta na makamshin nukliya. Har’ila yau ana ganin tattaunawar ta Istambul shi zai fayyace makomar dangantaka tsakanin Iran da tarayyar Turai gaba daya nan gaba.
Labarin ya kara da cewa tarunn yana gudana ne a cikin ofishin jakadancin kasar Iran dake birnin Istambul kuma Majid Takht-ravanci da kuma Kazem Ghariba abadi , mataimakin ministan harkokin wajen kasar ta Iran ne zasu jagoranci tawagar Iran a tattaunawar.
Kuma tattaunawar zasu maida hankali ne kan al-amura guda biyu. Shirin nukliyar kasar Iran da kuma dauke mata takunkuman tattalin arziki wadanda turawan suka dora mata.
Kafin taron dai ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa, matsayin Iran bai sawya ba, dole ne tashe makamashin Nukliya a cikin gida ya zama cikin shirin makamashin nukliya na kasar Iran. Ya kuma ce duk wani kokari na amfani da SnapBack zai fuskanci maida martani mai tsanani ga wadannan kasashe.