Sanata Dickson ya ƙara da cewa duk da wasu jami’an gwamnati ba su bi umarnin shugaban ƙasa ba, amma shi ya lashe zaɓen, kuma ya gode wa Buhari.

Hakazalika, ya ce bayan ya kammala wa’adinsa a 2020, a lokacin da APC ke shirin karɓar mulki a Bayelsa, kotun ƙoli ta yanke hukunci cewa ɗan takararsu bai cancanta ba, amma Buhari bai matsa lamba kan kotun ta sauya hukuncin ba.

“A lokacin mutane sun shirya rantsar da ɗan takarar APC a Bayelsa, amma cikin ƙasa da awa guda, kotun ƙoli ta soke nasararsa. Duk da haka Buhari ya karɓi hukuncin,” in ji shi.

Ya ce Buhari shugaba ne na gari, wanda duk da bambancin siyasa da ra’ayi, bai taɓa nuna bambanci tsakanin gwamnoni ba, ko suna APC ne ko na jam’iyyar adawa, yana girmama su tare da ba su tallafi iri ɗaya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Bayelsa Buhari Zaɓe

এছাড়াও পড়ুন:

HOTUNA: Shugaban Gambiya ya kai wa iyalan Buhari ziyarar ta’aziyya a Daura

Shugaban Ƙasar Gambiya, Adama Barrow, tare da matarsa Fatoumata Barrow, sun ziyarci Jihar Katsina, inda suka yi ta’aziyyar rasuwar tsohon shugaban ƙasa, marigayi Muhammadu Buhari.

Sun kai ziyarar ne a ranar Juma’a domin jajanta wa iyalan marigayin game da rashin da suka yi.

Za a ɗauke wuta na tsawon kwanaki 25 a Legas — TCN Wani mutum ya buɗe Ofishin Jakadancin Indiya na bogi a ƙasar

Sun sauka a filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina, inda Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Barista Abdullahi Faskari, ya tarbe su a madadin Gwamna Dikko Umar Radda.

Bayan sojoji sun yi wa Shugaba Barrow faretin ban girma, sun wuce Daura kai-tsaye, inda suka yi wa iyalan marigayin da kuma Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk ta’aziyya.

 

Ga hotunan a ƙasa:

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dalilan Da Suka Sa Cinikin Bayi Bai Yi Nasara A Arewacin Nijeriya Ba
  • ‘Yancin Gashin Kai: Ma’aikatan Kananan Hukumomi Sun Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki
  • HOTUNA: Shugaban Gambiya ya kai wa iyalan Buhari ziyarar ta’aziyya a Daura
  • An yanke wa mutum 3 hukuncin kisa kan kisan kai a Gombe
  • Buƙatar Rijistar Sabbin Jam’iyyu Ta Kai 144 — INEC
  • Yawan Ma’aikata Ne Ya Hana Borno Fara Biyan Sabon Mafi Ƙarancin Albashi – Zulum
  • Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutum 11 Da ‘Yan Bindiga Suka Sace A Sakkwato
  • Sojoji Sun Hallaka ‘Yan Bindiga Sama Da 100 A Neja
  • Brazil Ta Shiga Yaki Da HKI, Inda Ta Kudurin Anniyar Goyon bayan Afirka Ta Kudu A Kotun ICJ