Iran Da Eu Sun Fara Tattaunawa A Istambul
Published: 25th, July 2025 GMT
Jami’an diblomasiyya na kasashen Iran da kuma na tarayyar Turai 3 wato Faransa da Jamus da kuma burtaniya sun fara tattaunawa gaba da gaba bayan yakin kwanaki 12 wanda Amurka da HKI suka kai mata.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta kara da cewa wannan tattaunawar yana da matukar muhimmanci don zasu tattauna kan shirin makamashin nukliyar kasar Iran da kuma dauke mata takunkuman tattalin arzikin da su dora mata saboda shirinta na makamshin nukliya.
Labarin ya kara da cewa tarunn yana gudana ne a cikin ofishin jakadancin kasar Iran dake birnin Istambul kuma Majid Takht-ravanci da kuma Kazem Ghariba abadi , mataimakin ministan harkokin wajen kasar ta Iran ne zasu jagoranci tawagar Iran a tattaunawar.
Kuma tattaunawar zasu maida hankali ne kan al-amura guda biyu. Shirin nukliyar kasar Iran da kuma dauke mata takunkuman tattalin arziki wadanda turawan suka dora mata.
Kafin taron dai ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa, matsayin Iran bai sawya ba, dole ne tashe makamashin Nukliya a cikin gida ya zama cikin shirin makamashin nukliya na kasar Iran. Ya kuma ce duk wani kokari na amfani da SnapBack zai fuskanci maida martani mai tsanani ga wadannan kasashe.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu Ba Zai Taɓa Tauye ’Yancin Kafafen Yaɗa Labarai Ba, In ji Ministan Yaɗa Labarai
Ya ƙara da cewa, “Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ba zai taɓa, a kowace hanya ko salo, tauye ko hana ci gaban aikace-aikacen kafafen yaɗa labarai a wannan ƙasa ba. Amma dole ne mu duka ‘yan jarida da masu aikin yaɗa labarai mu haɗa kai, mu bi wannan hanya mai sarƙaƙiya, mu tabbatar da cewa al’umma tana ci gaba da zama cikin haɗin kai, yayin da muke riƙe shugabanni da gwamnati da alhakin aikin su.”
Idris ya jaddada muhimmancin kafafen yaɗa labarai wajen kula da tsarin dimokiraɗiyya, inda ya shawarci ’yan jarida da su kula da rawar da suke takawa domin kada su zama abin da zai jawo ruɗani ko rikici a cikin al’umma.
“A yayin da kuke yin wannan aiki, kuna da babban nauyi na riƙe gwamnati da shugabanni da alhakin aikin su. Amma ko da kuna yin hakan, dole ne ku sani cewa saboda matsayin ku na musamman da rawar da kuke takawa, za ku iya taimaka wa ƙasa matuƙa, amma idan ba a yi taka-tsantsan ba, ayyukan ku na iya cutar da al’umma,” inji shi.
Ya bayyana buƙatar sanin ya kamata da hankali wajen tantance sahihin bayani daga wanda zai iya ɓata zaman lafiya ko raba kan al’umma.
Ministan ya ce duk da ƙalubalen da ke fuskantar fannin yaɗa labarai, akwai haske a gaba domin kafafen sun ci gaba da nuna jajircewa da ɗorewa.
Ya kuma bayyana cewa ba shi ba ne Shugaban kamfanin jaridar Blueprint ba tun bayan da aka naɗa shi Minista.
“Ba ni ne shugaban jaridar Blueprint ba yanzu. Ni ma baƙo ne aka gayyata zuwa wannan taro. Na san cewa a baya ni ne ke gaba wajen shirya wannan taron na Blueprint, musamman tun lokacin da aka kafa ta shekaru 14 da suka wuce. Dole ne in gode wa waɗanda aka gayyata su haɗu da ni a watan Mayun 2005 domin tunanin fara jaridar Blueprint: Malam Ibrahim Sheme; Manajan Darakta, Malam Salisu Umar; Shugabar Kwamitin Tace Labarai, Hajiya Zainab Okino, da dukkan ma’aikatan jaridar Blueprint.
“Na gode da cigaba da tafiyar da abin da muka faro cikin nasara. Na shekara guda ban ziyarci ofishin ba, amma ina ganin lokaci ya yi da zan yi hakan. Ina so in ga ko har yanzu kuna ci gaba da tafiyar da abin da muka faro. Ina alfahari kuma ina farin ciki da cewa abin da muka fara ya ci gaba da bunƙasa,” inji shi.
Idris ya taya waɗanda suka samu kyaututtuka murna, inda ya bayyana cewa ba a yi masu kyautar bisa wani son zuciya ko tasiri daga wani waje ba, sai hukuncin jaridar ne kaɗai.
Cikin manyan baƙin da suka halarci taron akwai Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume; Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin; Ministan Ma’adanai, Dakta Dele Alake; Ministan Raya Noman Dabbobi, Idi Mukhtar Maiha; Etsu Nupe, Mai Martaba Alhaji Yahaya Abubakar, da babban baƙon jawabi na taron, Farfesa Attahiru Jega.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp