Shanghai Ya Gabatar Da Shirin Gina Yankin Motoci Masu Tuka Kansu
Published: 27th, July 2025 GMT
An fitar da wani sabon tsarin aiki na Shanghai na gina wani yanki da zai zamo kan gaba a fagen tafiyar da motoci masu tuka kansu jiya Asabar, yayin da ake ci gaba da gudanar da taron fasahar kirkirarriyar basira na duniya a birnin dake kudancin kasar Sin.
An tsara shirin ne da nufin ganin motoci masu tuka kansu a mataki na 4 sun yi jigilar fasinjoji fiye da miliyan shida nan da shekarar 2027, tare da bude hanyoyi sama da kilomita 5,000 domin motocin masu tuka kansu, tare da tabbatar da cewa an sanya wa fiye da kashi 90 cikin dari na sabbin motocin birnin na’urorin tuka kai na mataki na 2 da kuma mataki na 3.
An rarraba matakan tuka kai daga mataki na 0 zuwa mataki na 5. Yanayin girman kowane mataki ne yake nuna yanayin fasaharsa. Motoci masu tuka kansu na mataki na 4 na iya tuka kansu a mafi yawan yanayoyi ba tare da an tanadi wani direban ko-ta-kwana ba.
Darektan sashen ba da bayanai na hukumar kula da tattalin arziki da masana’antar kera motoci ta birnin Shanghai Han Dadong, ya bayyana cewa, Shanghai zai hanzarta gina wani yanki da zai zamo kan gaba a duniya wajen tukin motoci masu sarrafa kansu, ta hanyar hadin gwiwar bangarori daban-daban da suka hada da dandalolin tattara bayanai, da sansanonin horaswa, da na manyan tsare-tsaren fasahohin zamani da manufofi. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
IMF na Shirin aikewa da wata tawaga zuwa Senegal domin tattauna batun basussukan kaaar
Asusun ba da lamuni na duniya IMF ya fada a wannan alhamis cewa yana shirin aikewa da tawaga zuwa kasar Senegal a cikin watan Augusta domin tattauna yadda aza magance matsalar basussukan da ke kan kasar da kuma fara tattaunawa kan tsarin sabon shirin lamuni.
Kasar Senegal na fama da bashin biliyoyin daloli da gwamnatin da ta shude ta karba, lamarin da ya sanya asusun lamuni na duniya IMF ya dakatar da shirin ba da lamuni ga kasar.
A nasa bangaren kuma, wani mai magana da yawun IMF ya ce, “Asusun na bukatar karin bayanai kafin ya karfafa kimanta halin da ake ciki na basussukan kasar Senegal, sannan yana bukatar yarjejeniya kan muhimman matakan gyara.”
Ya kara da cewa, “Da zarar mun cimma matsaya kan manyan matakan gyara, hukumar ta IMF za ta sake yin nazari kan batun, yana mai bayyana cewa “zai yiwu a cimma matsaya kan wadannan matakan nan da makonni masu zuwa.”
Kakakin ya kara da cewa “Hukumar lamuni ta duniya IMF ta yi kiyasi bisa ga sabbin bayanai daga hukumomin kasar Senegal cewa basusukan da aka boye wanda gwamnatin da ta gabata ta karb, sun kai dala biliyan 11.3 a karshen shekarar 2023. Wannan ya hada da wani kaso na bashin kamfanonin gwamnati da aka kiyasta kusan kashi 7.4% na GDP.”
Kakakin IMF ya ce zai ba da bayanai ga hukumar kan yadda lamarin ya faru , yana mai cewa “IMF na gudanar da bincike na cikin gida da tantancewa a matsayin wani bangare na rashin bayar da rahotonni da suka dace.”